AREWA VOICE MEDIA

AREWA VOICE MEDIA Shirye-Shirye | Labarai | Wasanni | Nishadi
kafa Ce Wanda take kawo muku Shirye-Shirye masu kayatarwa da ilimantarwa.

A lalubemu ta hanyar WhatsApp 08088787766
ko Kuma ta channel dinmu https://whatsapp.com/channel/0029Vb7ktZiJ3jv3wDNpCv1a

13/09/2026

A.U Dorayi Pop and interior decoration.

13/09/2026

Ku kasance tare da Kabiru Yau Adam Bahawa a Cikin Shiri na Musamman.

🚨 DA DUMI-DUMI: RUNDUNAR SOJI TA TABBATAR DA SACE MALAMAI 6 A ZAMFARAZAMFARA: Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da cew...
13/09/2026

🚨 DA DUMI-DUMI: RUNDUNAR SOJI TA TABBATAR DA SACE MALAMAI 6 A ZAMFARA

ZAMFARA: Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da cewa wasu malaman addinin Musulunci guda shida (6) sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Zamfara.

Sai dai Rundunar ta musanta rahotannin da ke cewa an sace malaman ne a gidan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, da ke Talata Mafara.

A cewar Rundunar Sojin, malaman sun shiga hannun masu garkuwa ne yayin da suke tafiyar daga yankin dajin Sububu na ƙaramar hukumar Bakura zuwa Talata Mafara.

Lamarin ya faru ne yayin da malaman ke kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara domin halartar wata addu’a ta musamman da aka shirya domin neman zaman lafiya da kuma addu’ar samun nasara ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙoƙarinsa na sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace malaman ne kimanin kilomita uku daga ƙauyen Damri, a wani wuri da ake kira Gidan Suleiman Bature, cikin dajin Gonar Sarkin.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ma ta tabbatar da faruwar lamarin, inda kakakinta, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da cewa limamai shida ne aka yi garkuwa da su.

A halin yanzu, Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da kuma taimakon bayanan sirri daga al’ummar yankin, suna ƙara kaimi wajen gudanar da aikin ceto malaman.

Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, domin kauce wa haifar da fargaba ko kawo cikas ga ayyukan ceto da jami’an tsaro ke gudanarwa.

📰 AREWA VOICE MEDIA
— Muryar Arewa, Madubin Labarai —

Annada mahaifiyar Rahama sadau sarautar gargajiya a kaduna.
13/09/2026

Annada mahaifiyar Rahama sadau sarautar gargajiya a kaduna.

Ukashat ne zaici Mazabar maraku Saboda Abun Alkhairi da yayi WA Alummar Mazabar.
13/09/2026

Ukashat ne zaici Mazabar maraku Saboda Abun Alkhairi da yayi WA Alummar Mazabar.

Shi ya gyara mana Asibiti Ya Koma Sabo fill.
13/09/2026

Shi ya gyara mana Asibiti Ya Koma Sabo fill.

Hon Ukashat Adam Riruwai mutumin kirki ne shi.
13/09/2026

Hon Ukashat Adam Riruwai mutumin kirki ne shi.

2027: ZAN BIYA N500,000 A MATSAYIN MAFI KARANCIN ALBASHI — SOWOREƊan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sow...
13/09/2026

2027: ZAN BIYA N500,000 A MATSAYIN MAFI KARANCIN ALBASHI — SOWORE

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi alkawarin ƙaddamar da mafi ƙarancin albashi na N500,000 a wata ga ma’aikatan Najeriya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Sowore ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Independent, inda ya ce manufofin jam’iyyar AAC sun fi mayar da hankali kan adalci, daidaito da inganta rayuwar al’ummar Najeriya.

Daga cikin muhimman alkawuran da ya bayyana akwai:

- Samar da wutar lantarki sa’o’i 24.
- Samar da ilimi kyauta a dukkan matakai.
- Gina gidaje miliyan ɗaya na jama’a.
- Gyara dokokin haya domin rage wa ‘yan Najeriya matsin lambar biyan kuɗin haya na shekara ɗaya ko biyu a gaba.
- Bunƙasa masana’antu da noma.
- Samar da ƙarin ayyukan yi da inganta ababen more rayuwa.
- Inganta harkar kiwon lafiya.

Dangane da matsalar tsaro kuwa, Sowore ya yi alkawarin sake fasalin tsarin tsaro da ‘yan sanda, inganta jin daɗin jami’an tsaro tare da amfani da fasahohin zamani wajen yaƙi da miyagun laifuka.

Ya kuma ce gwamnatinsa za ta mai da hankali wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, tare da ƙoƙarin kwato dukiyar gwamnati da aka wawure.

Sowore, wanda ya sake zama ɗan takarar AAC a zaɓen 2027, ya ce damar jam’iyyar ta fi ta kowane lokaci, domin a cewarsa, AAC ba ta dogara da masu hannu da shuni ko ‘yan siyasar da ke jagorantar wasu manyan jam’iyyu ba.

AREWA VOICE MEDIA

13/09/2026

Dan takarar Shugaban Kasar Nigeria na jam'iyar ADC ya bayyana manufofinsa.

An Sace Malaman Musulunci 6 a Hanyar Talata MafaraRundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta fara bincike kan sace wasu malam...
13/09/2026

An Sace Malaman Musulunci 6 a Hanyar Talata Mafara

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta fara bincike kan sace wasu malaman Addinin Musulunci shida da ke kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara.

Rahotanni sun ce an sace malaman ne bayan sun halarci wani taron addu’a na Jam’iyyar APC a jihar.

Rundunar ta ce ta baza jami’ai domin gano inda suke da kuma ceto su.

Address

No 6B Plaza Near Doguwa Police Station Dadinkowa Doguwa Local Government
Kano
710105

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AREWA VOICE MEDIA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share