10/09/2026
MUNA CIGABA DA TANTANCE DIREBOBINMU DOMIN INGANTA HARKAR SUFURI
A yau, muna ci gaba da gudanar da aikin tantance direbobinmu, domin tabbatar da cewa muna da direbobi nagari, masu mutunci, da kuma fahimtar muhimmancin kula da fasinjoji da kuma martabar DAKATA TSAMIYA INVESTMENT LTD.
A yayin wannan aiki mai muhimmanci, Mai Girma Chairman/CEO na DAKATA TSAMIYA INVESTMENT LTD, IDRIS DALHATU SH*TU, ya kai ziyara tasharmu ta Bata, inda ya gana da wasu daga cikin direbobinmu tare da tattaunawa da su kan muhimman abubuwan da s**a shafi aikinsu da kuma makomar harkar sufuri.
Chairman ya bayyana cewa manufar wannan tantancewa ba wai don wahalar da direba ba ce, a'a, an yi ta ne domin a kara inganta tsarin aiki, a san direbobin kamfani yadda ya kamata, a tabbatar da bin doka da ka'idojin kamfani, tare da kara samar da ingantaccen tsaro da kwanciyar hankali ga fasinjojinmu.
Haka kuma, ya jaddada muhimmancin kyakkyawar mu'amala tsakanin direba da fasinja, domin direba shi ne fuskar kamfani a cikin al'umma. Don haka, duk direban da ke aiki tare da DAKATA TSAMIYA INVESTMENT ya zama wajibi ya kasance mai ladabi, gaskiya, hakuri, tsafta da kuma mutunta kowa.
Mai Girma Chairman ya kuma yabawa direbobin da s**a nuna jajircewa da biyayya ga tsarin kamfani, tare da kira ga kowa da ya hada kai domin gina kamfani mai girma wanda zai amfani direbobi, fasinjoji, masu zuba jari da kuma al'umma baki daya.
DAKATA TSAMIYA INVESTMENT LTD ta kuduri aniyar ci gaba da kawo sabbin tsare-tsare da za su inganta rayuwar direbobi tare da samar wa fasinjoji sufuri mai inganci, tsaro da kwanciyar hankali.
A gare mu, direba ba kawai ma'aikaci ba ne, abokin tafiya ne kuma babban ginshikin nasarar kamfaninmu.
Muna godiya ga dukkan direbobinmu bisa hadin kai da goyon bayan da suke bayarwa. Muna kira ga kowa da ya ci gaba da ba da gudummawarsa domin tare mu gina DAKATA TSAMIYA INVESTMENT LTD mai karfi da ci gaba.
DAKATA TSAMIYA INVESTMENT LTD
Self Reliance and Sustainability
Tare muke, tare za mu ci gaba!