30/08/2026
DSS za ta dakatar da ƙarar da ta shigar kan Sowore har sai bayan zaɓen 2027
Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta umarci lauyanta, Akinolu Kehinde, SAN, da ya ɗauki matakin dakatar da ƙarar da take yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, kan zargin cin zarafin mutane ta kafafen sada zumunta, har zuwa bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jaridar Punch ta rawaito cewa wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta ce an yanke shawarar hakan ne bayan wani taro tsakanin Darakta-Janar na DSS, Tosin Ajayi, babban lauyan hukumar da wasu manyan jami’an sashen shari’a na hukumar, wanda aka gudanar ranar 20 ga Agusta, 2026.
A cewar majiyar, taron ya tattauna yiwuwar dakatar da shari’ar domin bai wa Sowore damar shiga harkokin zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar ranar 16 ga Janairu, 2027, ba tare da wata matsala ba.
Majiyar ta ce Ajayi ya bayyana wa lauyoyin cewa, ganin yadda shari’ar ta kwashe kusan shekara guda tana gaban kotu, dakatar da ita na wasu watanni huɗu ba zai haifar da wata babbar illa ba.
Ana sa ran DSS za ta sanar da Babbar Kotun Tarayya a hukumance game da matakin dakatar da shari’ar daga ranar 14 ga Satumba, 2026, lokacin da kotuna za su koma zaman yau da kullum bayan hutun shekara-shekara na shari’a.
Idan kotu ta amince da dakatarwar, shari’ar za ta kasance a ajiye yayin da ake gudanar da yakin neman zaɓen shugaban ƙasa da kuma lokacin zaɓen 2027.
Sowore ya wallafa wasu saƙonni a shafinsa na X da Facebook ranar 25 ga Agusta, 2025, inda ya kira Shugaba Bola Tinubu da kalmar “criminal” (mai laifi).
Bayan wallafe-wallafen, DSS ta ba shi wa’adin kwanaki bakwai da ya goge saƙonnin, amma rahotanni sun ce ya ƙi yin hakan.
Daga bisani, hukumar ta garzaya Babbar Kotun Tarayya domin neman fassarar kotu kan ko kiran Shugaba Tinubu ko wani mutum da kalmar “mai laifi” a kafafen sada zumunta ya zama laifi na cin zarafi ta yanar gizo.
DSS ta ce manufar shari’ar ita ce neman kotu ta fayyace ko ya dace a kira mutum mai laifi ba tare da wata kotu ta yanke hukunci kan cewa mutumin ya aikata laifin ba.