GMN News Hausa

GMN News Hausa Gaskiya Media Network (GMN) is an independent, digital-first media organization based in Northern Nigeria.
(4)

We produce trusted, public-interest journalism primarily in Hausa, with selected content in English, to inform citizens, amplify community voices.

Majalisar Ƙoli ta Shari'a ta Najeriya ta yi kira da a saurari ƙarar tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa'i, domin a...
01/09/2026

Majalisar Ƙoli ta Shari'a ta Najeriya ta yi kira da a saurari ƙarar tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa'i, domin a samar masa da adalci a daina riƙe shi ba tare da sanin makomarsa ba.

Cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun sakatarenta na ƙasa Nafi'u Baba Ahmed, SCSN ta ce a tsarin dokokin Najeriya babu wanda ake ayyanawa a matsayin mai laifi har sai an same shi da aikata laifin.

SCSN ta ce a kundin tsarin mulki, ko wanne ɗan ƙasar na da 'yancin da ya k**ata a mutunta shi, ba tare da duba inda ya fito ba ko addininsa ko kuma jam'iyyar siyasar da yake da alaƙa da ita, bin ƙa'idar aiki da adalci da kuma tsare mutum bisa doron doka ba zaɓi ba ne a ƙasar, suna cikin ginshiƙan na adalci a dokokin Najeriya.

"Don haka, Majalisar ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su yi aiki da kundin tsarin mulki da dokokin Najeriya ta hanyar tabbatar da cewa an bi duk matakan doka a kowane mataki.

Haka kuma, Majalisar ta buƙaci hukumomi da su guji duk wani mataki da za a iya fassara shi a matsayin muzgunawa saboda dalilan siyasa, maimakon haka su nuna cikakken ƙudiri ga adalci, gaskiya da bin doka".

Sanarwar ta ƙara da cewa haɗin kan Najeriya da kwanciyar hankalinta na dogon lokaci suna da alaƙa kai tsaye da adalcin da hukumomin gwamnati da kuma amincewar da al'umma s**a yi da su.Dole ne a samar da adalc.

GMN News Hausa

Hukumar Kwastam  ta ce ta k**a bindigogi kirar pump-action 204 da aka ɓoye a cikin wani kwantena da ya isa tashar jirgin...
01/09/2026

Hukumar Kwastam ta ce ta k**a bindigogi kirar pump-action 204 da aka ɓoye a cikin wani kwantena da ya isa tashar jirgin ruwa ta TinCan Island da ke Legas daga ƙasar Turkiyya.

An ɓoye mak**an ne a tsakanin kayayyakin gida k**ar kujeru, firinjoci, na'urorin hasken rana da kuma garin sabulu.

Jami'an kwastam sun ce sun gano su ne bayan bayanan sirri da s**a samu s**a sa aka yi cikakken bincike kan kwantenan.

Hukumar ta bayyana cewa bindigogin nau'in MAS 49 Alter Magnum pump-action rifles ne, kuma an gano wasu kayayyakin bindiga tare da su.

Wannan ne karo na biyu cikin makwanni ƙalilan da aka k**a irin waɗannan mak**ai a tashar, bayan da aka gano wasu bindigogi 399 a wani kwantena a watan Agusta.

Jami'ai sun ce ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda s**a shigo da mak**an da kuma waɗanda aka nufa a kai musu.

GMN News Hausa

A wasu biranen ƙasar Hausa, musamman jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, da zarar ranar Maulidin Annabi Muham...
01/09/2026

A wasu biranen ƙasar Hausa, musamman jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, da zarar ranar Maulidin Annabi Muhammad ta zo, ta wuce, hankali yana komawa ne kan bikin Takutaha.

Ana dai gudanar da bikin Takutaha ne a ranar bakwai daga ranar Maulidi, wato ranar da Hausawa a al'ada suke yin bikin sunan wanda aka haifa.

A ranar bakwai da haihuwa ne dai aka saba da bikin raɗa suna da yanka da taron bikin na suna idan an samu ƙaruwa.

Bikin na Takutaha dai yana ɗaukar hankali sosai ne, inda mutane da dama suke bukukuwan shagali da dama, akwai dafe-dafe da yanka, sannan ake hawa domin murnar ranar.

Sai dai akwai bukukuwan al'ada da dama da ake aiwatarwa a ranar, sannan kuma akwai abubuwa da suke da alaƙa da ibada.

Wata kotu a Las Vegas, jihar Nevada ta Amurka, ta samu tsohon shugaban ƙungiyar 'yan daba Duane "Keffe D" Davis da laifi...
01/09/2026

Wata kotu a Las Vegas, jihar Nevada ta Amurka, ta samu tsohon shugaban ƙungiyar 'yan daba Duane "Keffe D" Davis da laifin kashe shahararren mawaƙin rap Tupac Shakur, wanda aka harbe a shekarar 1996.

Alƙalan kotun sun yanke hukuncin ne bayan shari’ar da ta ɗauki makonni ana sauraron shaidu da hujjoji.

An same Davis mai shekara 63 da laifin kisan kai na matakin farko tare da amfani da makami.

Masu gabatar da ƙara sun ce shi ne ya shirya harin da aka kai wa Tupac bayan wata arangama da ta haɗa mawakin da dan uwansa Orlando Anderson a daren da aka kashe shi.

Tupac Shakur, ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan hip-hop a duniya, ya samu raunuka ne yayin harbin da aka yi masa daga cikin wata mota a Las Vegas a ranar 7 ga Satumban 1996.

Ya rasu kwanaki shida bayan harin yana da shekara 25 kacal, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da hasashe tsawon shekaru da dama ba tare da an k**a wani ba.

An sake farfaɗo da binciken kisan ne bayan Davis ya bayyana wasu bayanai a cikin tarihin rayuwarsa da aka wallafa a shekarar 2019.

Bayan hukuncin kotun, an bayyana cewa zai iya fuskantar ɗaurin rai da rai, yayin da ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce ta kori ma'aikatanta sama da 40 cikin shekaru biyu da rabi da s**a ga...
01/09/2026

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce ta kori ma'aikatanta sama da 40 cikin shekaru biyu da rabi da s**a gabata saboda zargin hannusu a cin hanci da sauran laifukan kuɗi.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce fiye da mutum biyar daga cikin waɗanda aka kora na fuskantar shari'a a kotu, yayin da ake shirya gurfanar da wasu.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta ƙaddamar da sabbin matakan tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin ma'aikatanta, yana mai cewa EFCC ba za ta iya yaƙar cin hanci yadda ya k**ata ba idan nata jami'an suna aikata irin wannan laifi.

Haka kuma ya ce hukumar ta ƙwace sama da naira tiriliyan 1.23 da wasu manyan kuɗaɗen ƙasashen waje tsakanin Oktoban 2023 da Yunin 2026. - GMN News Hausa

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya jinjinawa jami'an tsaro bayan ceto mutum 21 da aka sace a jihar Kogi, ciki har da mambobin...
01/09/2026

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya jinjinawa jami'an tsaro bayan ceto mutum 21 da aka sace a jihar Kogi, ciki har da mambobin bautar ƙasa 15.

Shugaban ya ce haɗin gwiwar sojoji, 'yansanda, jami'an DSS da kuma masu sa-kai ne s**a gudanar da aikin ceton, inda aka kuɓutar da waɗanda aka sacen daga maɓoyar masu garkuwa da mutane a dajin Ofu.

Tinubu ya ce jami'an tsaro na ci gaba da farautar masu garkuwar, yana mai jaddada cewa duk wanda ke da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci bisa doka.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya. -

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce ƙasarsa za ta koma aiwatar da yarjejeniyar Islamabad nan take idan Amurka ta kom...
01/09/2026

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce ƙasarsa za ta koma aiwatar da yarjejeniyar Islamabad nan take idan Amurka ta koma cika alƙawuran da ta ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar.

Yayin da yake jawabi a taron Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai, Pezeshkian ya ce Iran a shirye take ta mayar da martani iri ɗaya idan Washington ta mutunta yarjejeniyar.

A wani ɓangaren kuma, rundunar sojin Iran ta sake gargaɗin ƙasashen yankin cewa za ta kai farmaki ga duk wata ƙasa da aka yi amfani da yankinta wajen kai mata hari.

Rahotanni sun kuma ce an kai hari kan wani tankar ɗanyen mai a mashigar Hormuz, yayin da Sakataren Sojin Amurka Daniel Driscoll ya yi murabus bayan samun saɓani da Sakataren Tsaro Pete Hegseth. -

Hukumar hana fataucin mutane ta Najeriya (NAPTIP) ta ce ta ceto yara sama da 180 da aka yi safararsu daga jihohin Kaduna...
01/09/2026

Hukumar hana fataucin mutane ta Najeriya (NAPTIP) ta ce ta ceto yara sama da 180 da aka yi safararsu daga jihohin Kaduna, Anambra, Benue, Nasarawa da wasu wurare a ƙasar.

Hukumar ta bayyana cewa wasu ƙungiyoyin masu fataucin yara na yaudarar iyaye ta hanyar bayyana kansu a matsayin ma'aikatan ƙungiyoyin farar hula masu tallafa wa yara da ilimi, sannan su tafi da yaran da sunan ba su ilimi da tallafi.

A baya-bayan nan, an ceto wasu yara uku da aka kwaso daga Kajuru a jihar Kaduna a wani gini da ke Onitsha ta jihar Anambra, yayin da aka kuma gano wani yaro a hannun wata ma'aikaciyar lafiya.

NAPTIP ta ce wasu daga cikin yaran da aka ceto an kai su gidajen marayu inda aka rika sayar da su ga mutane da sunan ɗaukar yara reno.

Hukumar ta ce tana ci gaba da farautar masu hannu a wannan laifi domin gurfanar da su a gaban kuliya. -

Manyan Labaran mu na Yau 31-08-2026 - GMN News Hausa
31/08/2026

Manyan Labaran mu na Yau 31-08-2026 - GMN News Hausa

31/08/2026

Manyan Labaran mu na Yau 31-08-2026 - GMN News Hausa

Address

Media House Plaza Sani
Kano
700101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GMN News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share