
18/08/2025
DA DUMI-DUMI: An Zargi Shugaban Jami'ar FCAPT ta Kano da Gwanjon manyan Taraktoci, da Daukar ’Ya’yansa Aiki ba Bisa Ka’ida ba
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban Kwalejin Noma ta Tarayya da ke Kano (Federal College of Agricultural Produce Technology – FCAPT), Dr. Yusha’u Muhammad Gwaram, na fuskantar zarge-zarge masu nauyi na yiwa kansa gwanjon taraktoci da motar makarantar, tare da daukar ’ya’yansa aiki a kwalejin ba bisa ka’ida ba.
Bincike ya nuna cewa duk da ya rage masa kasa da watanni biyu ya sauka daga kujerarsa, shugaban ya mayar da hankali wajen baiwa wasu malamai da ma’aikata kwairi, alhali kuma daya daga cikin ’ya’yansa da ya dauka aiki yana ci gaba da kauracewa wajen aikinsa.
Wata majiya mai tushe ta shaidawa kamfanin dillancin labarai cewa akwai wani asusun banki da ake karbar kudade daga hannun dalibai ta hanyar da ba ta dace ba.
Sai dai a nasa bangaren, Dr. Gwaram ya musanta duka zarge-zargen, inda ya ce ma’aikatan da ke neman bata masa suna ne ke yada irin wadannan rahotanni.
Shi ma Rejistar makarantar, Malam Waziri Umar, ya yi karin haske, inda ya ce duk wani gwanjon da aka gudanar, ko na taraktoci ko na motocin hawa, an yi shi bisa ka’ida.
Game da zargin ’ya’yan shugaban makarantar kuwa, ya ce Ahmad – daya daga cikinsu – yana zuwa aiki, har ma sun hadu da shi kwanan nan a makarantar. Ita kuma ’yar tasa mace tana ci gaba da karatun digiri tare da izinin hukumar makarantar na tsawon shekaru biyu, sannan idan bukatar hakan ta taso, za a iya kara mata lokaci.
A nasa bangaren, Shu’aibu Umar Idris, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai magana da yawun shugaban makarantar, ya ce za su dauki matakin shari’a idan aka sake wallafa wani labari da zai bata musu suna.