Hausa Lens TV

Hausa Lens TV Hausa Lens TV Jarida ce da za ta riƙa kawo maku Labarai da Documentaries akan abinda ya shafi Tarihi, al'adu, Siyasa, kasuwanci da sauransu.

05/06/2026
Ɗaukar mutane tare dabbobi cikin mota ɗaya babban laifi ne.Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadi...
02/06/2026

Ɗaukar mutane tare dabbobi cikin mota ɗaya babban laifi ne.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana haka cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ya ce sashe na 93 na dokar hanya, National Road Traffic Regulations ya haramta wannan irin lodi.

Me za ku ce?

INEC Ta Fara Bincike Kan Zargin Fitar da Bayanai daga Kundin Masu Kada Kuri’aHukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC)...
02/06/2026

INEC Ta Fara Bincike Kan Zargin Fitar da Bayanai daga Kundin Masu Kada Kuri’a

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ta fara gudanar da bincike kan zargin samun bayanan masu kada kuri’a daga kundinta ba tare da izini ba, bayan wata takaddama da ta taso a shafukan sada zumunta.

Takaddamar ta biyo bayan wani sako da Lere Olayinka mai magana da yawun Ministan Abuja, Nyesom Wike ya wallafa inda ya bayyana wasu bayanai da s**a shafi canja wurin rijistar zabe ta wani dan siyasa yayi. Lamarin ya janyo cece-kuce, inda mutane da dama s**a nuna damuwa kan yadda aka samu bayanan.

A wata sanarwa, INEC ta ce ta ɗauki lamarin da muhimmanci, kuma ta fara cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Hukumar ta kara da cewa binciken farko ya nuna wanda ake zargi bai samu bayanan kai tsaye daga kundin INEC ba, sai dai ta yi alkawarin daukar matakin da ya dace bayan kammala binciken.

Arsenal ta sha kashi a hannun Manchester City a wasan karshe na cin kofin Carabao Kungiyar kwallon kafa ta Manchester Ci...
22/03/2026

Arsenal ta sha kashi a hannun Manchester City a wasan karshe na cin kofin Carabao

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta lallasa Arsenal da ci 2 da nema a wasan karshe na cin kofin Carabao.

Masu sharhi kan wasan ƙwallon ƙafa, sun yi hasashen cewa Arsenal na da damar ɗaukar kofuna har guda 4 a wannan kakar wasan duba da yadda suke nuna bajinta.

Amma a halin yanzu har sun rasa kofi ɗaya, shin za su iya daukar sauran kofuna ukun da s**a rage, wato Premier League, da Champions League, da kuma FA Cup?

Address

Zoo Road Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Lens TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share