Umar Yahaya Labbo

Umar Yahaya Labbo I'm proud to be Muslim �
I'm proud to be Hausa �
I love Muhammad
Then Fear Allah wherever you are

ALHAMDULILLAHI GOBE ZAMU TASHI DA AZUMIN WATAN RAMADAN
17/02/2026

ALHAMDULILLAHI GOBE ZAMU TASHI DA AZUMIN WATAN RAMADAN

LABBAIKA YA RASULULLAH LABBAIKA YA NURULLAH LABBAIKA YA HABIBULLAHABIN ALFAHARINMU MUHAMMAD RASULULLAH 💯💯💯💯💯💯💯💯💯💯💯💯💯💯SAW
26/12/2025

LABBAIKA YA RASULULLAH
LABBAIKA YA NURULLAH
LABBAIKA YA HABIBULLAH
ABIN ALFAHARINMU
MUHAMMAD RASULULLAH 💯
💯💯💯💯💯💯💯💯💯💯💯💯💯
SAW

🤲🤲 🤲 💯💯💯💯💯💯ALLAH KAIMANA DON ANNABI
25/12/2025

🤲🤲 🤲
💯💯💯💯💯💯
ALLAH KAIMANA DON ANNABI

Masoyin mu ANNABI MUHAMMAD 💯
25/12/2025

Masoyin mu ANNABI MUHAMMAD 💯

KA SANI: ALLAH YANA TARE DA KAIKa danne damuwa… ka kwantar da zuciya… ka saurara:Allah baya barin bawansa shi kaɗai.Ko l...
10/12/2025

KA SANI: ALLAH YANA TARE DA KAI

Ka danne damuwa… ka kwantar da zuciya… ka saurara:
Allah baya barin bawansa shi kaɗai.
Ko lokutan da kake tunanin ka faɗi,
ko lokacin da kake jin kowa ya juya baya—
Allah na nan.

Allah yana tare da kai

A lokacin da mutane ba su fahimce ka ba.

A lokacin da zuciyarka ta kulla damuwa.

A lokacin da kake neman mafita amma ba ka ganewa.

A lokacin da kake cikin gwaji, kukan da baka furtawa kowa.

Shi yafi kusa da kai fiye da jijiyoyin wuyanka.
Yana jin kukanka, yana ganin damuwarka,
yana sanin abin da kake boyewa.

Ka tsaya da tawakkali

Domin duk wanda ya dogara ga Allah,
Allah ya isar masa.

Ka cigaba da addu’a,
ka cigaba da ƙoƙari,
ka cigaba da gaskiya—
domin ba ka tafiya kai kaɗai.

Ka sani: Allah yana tare da kai—ko da kai kanka baka jin hakan.

Umar Yahaya Labbo ✍️

DA ƊUMI-ƊUMI: Burkina Faso ta saki Jirgin Sojin Nijeriya da ta tsare da Sojoji 11Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya 1...
10/12/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Burkina Faso ta saki Jirgin Sojin Nijeriya da ta tsare da Sojoji 11

Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya 11 da ta tsare bayan saukar gaggawa da jirgin sojin saman Nijeriya ya yi.

Lamarin ya fara ne bayan Burkina Faso ta ce wani jirgin sojin C-130 ya shiga sararin samaniyarsu ba tare da izini ba, sannan ya sauka a garin Bobo-Dioulasso. Hukumomin kasar sun ɗauki matakin gaggawa bisa damuwar kare ikon ƙasarsu, lamarin da ya sa aka tsare ma’aikatan jirgin na dan lokaci.

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa jirgin yana kan hanyarsa ne zuwa Portugal, amma matsalar na’ura ce ta tilasta masa yin saukar gaggawa.

Sakin sojojin ya kawo sauƙi a wannan lokaci na ƙarin tsoron tashin hankali a yankin, musamman ganin yadda Burkina Faso da sauran kasashen Ƙungiyar Kawancen Kasashen Sahel (AES) ke nuna taka-tsantsan kan motsin dakarun waje.

A halin yanzu, al’amari ya warware cikin lumana — amma ya nuna irin raunin da ke cikin dangantakar soja da diflomasiyya a yankin Sahel.

Umar Yahaya

10/12/2025

Duk masoyin ANNABI MUHAMMAD
Me Arziki ne

 Mafii  Itace Soyayyar     #
07/12/2025


Mafii
Itace Soyayyar
#

Kiyo da Tallan NonoShine gaba wajen cigabanKasar Hausa in
05/12/2025

Kiyo da Tallan Nono
Shine gaba wajen cigaban
Kasar Hausa in

Dan Allah Tambaya Nake Son Nayi...?Meyasa a cikin yan kannywood gabaki daya ADAM.A.ZANGO ne kadai yake da irin yan masif...
04/12/2025

Dan Allah Tambaya Nake Son Nayi...?

Meyasa a cikin yan kannywood gabaki daya ADAM.A.ZANGO ne kadai yake da irin yan masifar masu kaunar sa "Die Hard Fans", yafi kowa fan base da irin su shi suke kauna ɗin.

Kusan an kai wani mataki da ni shine kadai dan film da ake kafewa a media, amma kaga duk yan comment section suna kaunarsa. Kusan a kannywood idan kana son gama da yan comment section lafiya to ka so shi.

"Wallahi ni kaina kaf yan film bani da wanda a raina nake jin ina matuƙar kaunar sa kamar sa"

BARKA DA YAMMACI

LABARIN ADDININ MUSULINCI A JAHAR KANO KAFIN ZUWAN ƊAN FODIOMusulunci ne addinin mutanan jahar Kano tun a ƙarni na 14 a ...
03/12/2025

LABARIN ADDININ MUSULINCI A JAHAR KANO KAFIN ZUWAN ƊAN FODIO

Musulunci ne addinin mutanan jahar Kano tun a ƙarni na 14 a zamanin Sarki kano Ali Yaji a shekarar (1349–1385)
A da can… kafin zuwan sarakunan fulani jahar Kano, kafin yaƙin Yandoto da Gobir a ƙasar Hausa, Kano ta riga ta yi tsayin daka a matsayin babbar cibiyar Musulunci.

Saidai akwai abubuwan fama dasu irin na Al-adu, haraji, bori a wasu wurare.
Amma duk da haka:
Sarki Musulmi ne.
Majalisar sarauta Musulmai ne.
Shari’ar Musulunci tana da tasiri, musamman a harkokin aure, kasuwanci da zamantakewa.

Tun a zamanin Sarki Ali Yaji, tun kafin zuwan dan fodio an rusa wuraren bori, an kafa masallatai, kuma malamai s**a fara shigowa daga ƙasar Bornu, da Gao, Timbuktu, da wasu daga cikin Hausawa da Fulani da s**a tuba su koma malamai.

Idan dare yayi ana kunna fitulu masallatai malamai suna karanta Alƙur’ani har zuwa lokacin da za’ayi sallar shiga gida (ISHA’I).
Ana tattara yara a koya musu karatun addini idan angama za’a sallami kowa su tafi gidajen iyayensu.

Kano garin kasuwanci ce mai cike da Attajirai, malamai da makarantun allo.
Tun a lokacin Al’umma masu bin abin da suke ganin ya fi dacewa da su ne.

Saboda haka lokacin yaƙin bai kasance tsakanin Musulmi da kafiri ba, ya kasance tsakanin tsarin gargajiya da sabon tsarin gargajiyya ne.😂

Zan fada muku manofifin fodiyawa da dalilan da yasa s**a yaki masarautun Hausawa.

Duk me buqatar karin bayana zai iya zuwa ya bincika Bayanan masu tarihin Hausa (oral tradition)

Masana tarihi kamar:
• M. G. Smith
• H. R. Palmer
• Murray Last
• Yusuf Baba

✍️ Umàr Yahaya Labbo
Dalibin kimiyar zamantakewa

Address

Dala Kano
Kano
UMARYAHAYALABBO1011

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Umar Yahaya Labbo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share