Dala Alkibla

Dala Alkibla Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dala Alkibla, News & Media Website, Dala, Kano.

05/03/2026
05/03/2026

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da samar da kuɗaɗe har ₦334 biliyan domin sake fasali da kuma gina titin Kano–Kongolom, wani muhimmin aiki da ake sa ran zai kawo sauyin fasalin sufuri da tattalin arziki.

Cikin wata takarda da ya fitar, Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce amincewar da Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta bayar na nuna ƙudirin gwamnatin tarayya wajen tallafa wa manyan ayyukan more rayuwa a Kano da ma Arewa baki ɗaya.

Ya bayyana cewa aikin zai ratsa tsawon kilomita 132, inda za a gina shi a matsayin hanya mai layi uku da kankare, tare da hasken tituna na hasken rana da kuma na’urorin sa ido na CCTV domin ƙara inganta tsaro da sauƙaƙa zirga-zirga.

Sanarwar ta ƙara da cewa titin Kano–Kongolom na haɗa Kano da jihohin Jigawa da Katsina, lamarin da ya sanya shi zama ɗaya daga cikin manyan hanyoyin tattalin arziki a Arewa maso Yamma, musamman ga harkokin noma, kasuwanci da sufuri.

Arewa Trends ta rawaito cewa samar da wannan manyan kudadei na ₦334 biliyan na daga cikin manyan matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka domin bunƙasa hanyoyi da ƙarfafa tattalin arzikin yankuna, tare da ƙara haɗin kai tsakanin jihohi.

Fadakarwa daga Hazikin matashinnan mai Gidauniyar taimakawa Marayu da Marasa karfi, Alh Sani Rogo Aikawa.
27/02/2026

Fadakarwa daga Hazikin matashinnan mai Gidauniyar taimakawa Marayu da Marasa karfi, Alh Sani Rogo Aikawa.

Autan mawaka ya nuna godiyarsa ga shugaban karamar hukumar birni bisa bisa dama da ya ba shi ta taya shi aikin al'umma
27/02/2026

Autan mawaka ya nuna godiyarsa ga shugaban karamar hukumar birni bisa bisa dama da ya ba shi ta taya shi aikin al'umma

Address

Dala
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dala Alkibla posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share