10/07/2026
An Ceto Dukkan Ɗalibai Da Malaman Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Oyo — Onanuga
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya sanar da cewa jami'an tsaro sun yi nasarar ceto dukkan ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Orire ta Jihar Oyo.