07/06/2026
Matashin tauraron ƙwallon ƙafa na ƙungiyar FC Barcelona kuma ɗan wasan ƙasar Spain, Lamine Yamal, ya sake jawo hankalin duniya bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa yanzu yana samun kusan dala miliyan 4.4 a duk wani saƙon talla da ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Idan wannan rahoto ya tabbata, hakan na nufin Yamal ya zarce fitattun taurarin ƙwallon ƙafa irin su Lionel Messi da Cristiano Ronaldo, har ma da shahararriyar mawaƙiya kuma jarumar fina-finai Selena Gomez wajen kuɗin da ake biya domin tallace-tallace a kafafen sada zumunta.
Rahotannin sun nuna cewa karuwar shahararsa a duniya, musamman bayan bajintarsa tare da Barcelona da tawagar Spain, ta sa manyan kamfanoni ke neman yin amfani da sunansa wajen tallata hajojinsu. Hakan ya sanya darajarsa a duniyar talla da kasuwancin kafafen sada zumunta ta yi matuƙar ƙaruwa.
Sai dai har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga Yamal ko wakilansa da ta tabbatar da adadin dala miliyan 4.4 da ake cewa yana karɓa a kowane rubutu na Instagram.