14/08/2025
FARASHIN KAYAN ABINCI YA KARA SAUKA A KASUWAR MAKARFI.
14 ga Agusta, 2025
A wannan makon, Kasuwar Makarfi ta Kaduna ta shaida raguwar farashin wasu muhimman kayan abinci idan aka kwatanta da makon da ya gabata.
Bisa ga rahoton kasuwa:
Masara (mai aure) ta sauka daga ₦38,000 zuwa ₦32,000
Wake fari manya daga ₦85,000 zuwa ₦70,000
Shinkafa Jamila daga ₦40,000 zuwa ₦38,000
Kalwa babban buhu daga ₦150,000 zuwa ₦145,000
Barkono Ɗan zagade daga ₦40,000 zuwa ₦30,000
Masu sana’a sun ce raguwar na iya zama sakamakon karin kayayyaki da s**a shigo kasuwa da kuma yanayin damina da ke taimakawa wajen noman kayan abinci.
Amma duk da haka wannan Sauki Yazo Da barazana ga manoma Saboda tsadar taki Da Sauran kayan Aikin gona.
SHIN AWANI MA'AUNI ZA'A AUNA WANNAN SAUKIN?