Majalla Post.

Majalla Post. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Majalla Post., Media/News Company, Katsina.

Idan Allah Ya Sa Na Zama Gwamnan Jihar Katsina A 2027 Zan Yi Bakin Kokarina Ganin Na Kawo Karshen Matsalar Tsaro Da Ta Ƙ...
05/01/2026

Idan Allah Ya Sa Na Zama Gwamnan Jihar Katsina A 2027 Zan Yi Bakin Kokarina Ganin Na Kawo Karshen Matsalar Tsaro Da Ta Ƙi Ci Ta Ƙi Cinye Wa, Amma Fa Ba Zan Yi Goyan Bayan Sulhu Da Ƴan Bìñdiga Ba, Cewar Lawal Daura, Tsohon Shugaban Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta DSS

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

RAHOTON AYYUKAN ENGR. SAGIR TANIMU SABUWA (BULLDOZER) GUDA 115 A CIKIN WATA SHIDA (6) KACAL A KARAMAR HUKUMAR SABUWAA ci...
01/12/2025

RAHOTON AYYUKAN ENGR. SAGIR TANIMU SABUWA (BULLDOZER) GUDA 115 A CIKIN WATA SHIDA (6) KACAL A KARAMAR HUKUMAR SABUWA

A cikin dan kankanin lokaci na watanni shida kacal tun bayan zaben Hon. Engr. Sagir Tanimu (Bulldozer) a matsayin shugaban karamar hukumar Sabuwa, al’umma sun shaida sabon salo na jagoranci mai cike da aiki, jajircewa, da hangen nesa wajen kawo cigaba A Sabuwa.

Ya shigo Ofis amatsayin Shugaban karamar hukumar Sabuwa da manufar sake Gina karamar hukumar Sabuwa bisa gaskiya da saita akalar siyasar karamar hukumar tare da bunkasa muhimman ababen more rayuwa domin amfanin kowa da kowa.

Tun daga kwanakin farko na zuwansa an fara ganin sakamako a fili aiki ba surutu ba kuma Al'umma sun sheda da jajircewarsa.

Wannan rahoto ya ƙunshi jerin manyan ayyuka guda 115 da aka kammala su wasu kuma ana kan aiwatarwa a cikin karamar hukumar Sabuwa kuma duk acikin watanni shida kacal da zuwansa (CHAIRMAN) ENGR. SAGIR TANIMU BULLDOZER
Wannan ba ƙaramin abu ba ne, domin ya tabbatar da cewa gwamnatin Sabuwa ta mayar da aiki shi ne ginshikin mulkinta.

Ayyukan sun shafi bangarori daban–daban na rayuwa, ciki har da:

🔹 Gina da gyaran gine-gine
🔹 Fannin kiwon lafiya
🔹 Ilimi da tallafi ga makarantu
🔹 Tsaro da walwalar jama’a
🔹 Samar da ruwan sha
🔹 Da Sauran ababan more rayuwa

Wannan cigaba ya tabbatar da cewa al’umma suna cikin farin ciki da ganin yadda karamar hukumar Sabuwa ta dauki Saitin dawowa cikin tsarin da Al'umma zasuyi Alfahari da ita ba tare da wariya ko fifita rukuni ɗaya akan wani ba.

Ayyuka 115 sun zama tamkar shaida ta cewa Sabuwa ta samu sabon shugabanci na gaskiya da aiki a sanadiyyar Engr. SAGIR TANIMU.

Muna godiya ga Mai Girma Gwamna,Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda (PhD) bisa goyon baya da kulawar da yake baiwa kananan hukumomi domin samar da ci gaba mai dorewa ga jama’a.

Sabuwa tana samun gagarumin ci gaba, kuma al’umma na ganinsa da ido ba labari ba.

Hon. Engr. Sagir Tanimu (Bulldozer) Aiki Bai tsaya ba........

OFFICE OF THE SA

Hon. Aminu Ibrahim Doguru (SLA) na maigirma Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabun Mashi/Dutsi, ya bada tallafin kay...
10/11/2025

Hon. Aminu Ibrahim Doguru (SLA) na maigirma Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabun Mashi/Dutsi, ya bada tallafin kayan karatu ga ɗalibai domin ƙarfafa ilimi da ƙara musu kwarin gwiwa a harkar karatu.

1. Litattafan rubuta guda 300
2. Jikunan makaranta guda 300
3. Fensil na rubuta guda 300

A yayi ziyarar ya samu rakiyar shugaban kungiyar malamai na karamar hukumar mashi malam jamilu Ado Karau Jamilu da kuma wakilin sakataren ilmi na karamar hukumar mashi Alh. Tanimu PPO da kuma shugaban kungiyar iyayen yara mai unguwa Bala Bola. ya samu kyakkyawan tarba daga shugaban makarantar da kuma sauran malamai.

sun kuma godiya so sai a gare shi.

Ina tabbatar muku za mu kawo ƙarshen ta'addanci - Tinubu
06/11/2025

Ina tabbatar muku za mu kawo ƙarshen ta'addanci - Tinubu

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR SABUWA HON. SAGIR TANIMU SABUWA YA AMINCE DA NADIN MASHAWARTA NA MUSAMMAN DA MATAIMAKA NA MUSAM...
04/11/2025

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR SABUWA HON. SAGIR TANIMU SABUWA YA AMINCE DA NADIN MASHAWARTA NA MUSAMMAN DA MATAIMAKA NA MUSAMMAN.

Shugaban Karamar Hukumar Sabuwa, Hon. Sagir Tanimu Sabuwa, ya amince da nadin wasu mutane a matsayin masu bashi Shawararori na Musamman da kuma Mataimaka na Musamman.

Wannan mataki ya kara nuna kudurin sa na tabbatar da ingantacciyar gudanarwa da, hadin kai, da kuma jajircewa wajen samar da kwararrun da za su taimaka wajen ciyar da Karamar Hukumar gaba ta fuskar ci gaba da cigaban Al'ummar karamar hukumar sabuwa baki daya.

An yi tsammanin wadanda aka nada za su amfana da gogewarsu da basirar su a fannoni daban-daban domin tabbatar da nasarar manufofin gwamnati da aiwatar da shirye-shiryen ci gaba na Karamar Hukumar Sabuwa.

Shugaban Karamar Hukumar ya taya sabbin wadanda aka nada murna, tare da kiran su da su tabbatar da amincewar da aka nuna gare su ta hanyar aiki tukuru, gaskiya, biyayya da sadaukar da kai domin bauta wa al’ummar Karamar Hukumar Sabuwa.

Shugaban karamar hukumar sabuwa Ya kara da bayyana cewa za'a sanar da takamaiman mukamai da fannoni na aikin kowan ne daga cikin su a nan gaba kadan bada jimawa ba.

Nijeriya za ta karbi bashin Dala biliyan daya daga bankin duniyaKarin bayani: https://is.gd/Sg3K8R
02/11/2025

Nijeriya za ta karbi bashin Dala biliyan daya daga bankin duniya

Karin bayani: https://is.gd/Sg3K8R

Shugaban Gwagware Foundation, Alh Yusuf Aliyu Musawa , ya yaba wa Gwamna Malam Dikko Umar Radda, PhD, CON, bisa nadin En...
29/10/2025

Shugaban Gwagware Foundation, Alh Yusuf Aliyu Musawa , ya yaba wa Gwamna Malam Dikko Umar Radda, PhD, CON, bisa nadin Engr. Surajo Yazid Abukur a matsayin Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Katsina.

A yau Alhamis, 29 ga Oktoba, 2025, dubban masoya da abokai sun raka Engr. Surajo yazid zuwa sabuwar ma’aikatarsa bayan ya mika mulki a Hukumar KASAROMA. An kuma gudanar da liyafar taya murna a dakin taro na Gwagware Foundation da ke Katsina.

Alh Yusuf Ali musawa ya ce nadin Engr. Surajo ya nuna yadda Gwamna Radda ke mutunta ƙwazo da gaskiya wajen zabar mutane masu kishin ci gaban jihar. Ya bayyana Engr. Surajo a matsayin mutum mai jajircewa wanda ya dade yana bayar da gudunmawa domin cigaban Matasa da alumma.

A nasa jawabin, Engr. Surajo yazid ya godewa Gwamna Radda bisa amincewar da yayi masa domin bashi mukamin Kwamishinan matasa da wasanni, tare da yin alkawarin aiki tukuru don inganta harkokin matasa da wasanni a jihar.

A ƙarshe, Alhaji Yusuf Ali Musawa ya yi addu’ar nasara ga sabon kwamishinan da kuma ci gaba mai ɗorewa ga Gwamnatin Mal Dikko Umaru Radda.

Salim Ahmad Gaiwa
Public Relations officer
Gwagware foundation
Gidan-Amana

Nadin Da Aka Yi Wa Hadi Sirika Shugaban Gudanarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Ba Daidai Ba Ne – Inji Hon. Ghali Salis...
29/10/2025

Nadin Da Aka Yi Wa Hadi Sirika Shugaban Gudanarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Ba Daidai Ba Ne – Inji Hon. Ghali Salisu Bakori

Mashawarci na musamman kan harkokin dalibai da matasa ga Sanata Yakubu Lado Dan Marke, Hon. Ghali Salisu Bakori, ya bayyana cewa nadin da gwamnatin jihar Katsina ta yi wa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, a matsayin Shugaban Gudanarwa (Pro-Chancellor) na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) ba daidai ba ne.

Hon. Ghali ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce bai dace a rika shigar da siyasa cikin harkokin ilimi ba, domin hakan yana iya jefa al’umma cikin matsala.

“Mun yarda siyasa tana da wurinta a rayuwa, amma ba ta da gurbi a bangaren ilimi. Da zarar an shigar da siyasa cikin harkar ilimi, to tabbas hakan zai haifar da koma-baya da rashin ci gaba,” in ji shi.

Ya ce ya kamata gwamnati ta rika yin duba sosai wajen nadin shugabanni a jami’o’in da ke karkashin ta, domin tabbatar da cewa mutanen da s**a dace ne suke rike da mukamai.

“Tambayarmu ita ce: shin Sanata Hadi Sirika yana da kwarewa a harkokin gudanarwar jami’a? Saninmu shi ne, ƙwarewarsa tana kan fannin sufurin jiragen sama, ba na gudanarwar jami’a ba,” in ji Hon. Ghali.

Ya ƙara da cewa nadin tsohon ministan a matsayin shugaban gudanarwar jami’a babban abin damuwa ne, musamman ga jihar Katsina wadda ta shahara da mutanen da s**a yi fice a fannin ilimi da bincike.

“A bashi irin mukamin da ya dace da ƙwarewarsa – kamar a fannin sufurin jiragen sama. Amma ba a jami’a ba, domin hakan tozarta ilimi ne da kuma abin da jihar Katsina ba ta cancanta da shi ba,” in ji shi a ƙarshe.

Dan Majalisar dokoki a Zamfara da jiga-jigai a PDP sun sauya sheƙa zuwa APCDan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Marad...
29/10/2025

Dan Majalisar dokoki a Zamfara da jiga-jigai a PDP sun sauya sheƙa zuwa APC

Dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Maradun II ta jihar Zamfara, Hon. Maharazu Salisu, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC tare da wasu manyan ‘yan jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar ta APC a jihar Tukur Danfulani ne ya karbesu a yayin taron da ya gudana a ofishin jam’iyyar APC na jihar da ke Gusau.

Hon. Salisu ya ce rashin adalci da nuna banbanci a cikin jam’iyyar PDP ne ya sa ya fice daga cikinta, inda ya bayyana cewa mazabarsa ba ta samu kulawa ko wakilci daga gwamnati bayan zaben 2023,wadannan dalilan s**a sa shi sauya sheka zuwa APC.

Ba A Tauye ’Yancin Addini A Nijeriya, In Ji  Ministan Yaɗa Labarai A Hirar CNNMinistan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alh...
29/10/2025

Ba A Tauye ’Yancin Addini A Nijeriya, In Ji Ministan Yaɗa Labarai A Hirar CNN

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana ƙara maida hankali wajen magance matsalolin tsaro a ƙasar nan domin tabbatar da tsaro da walwalar ’yan ƙasa.

Da yake magana a cikin wata hira da gidan talbijin na CNN ya yi da shi a London a daren Talata, Idris ya ƙaryata iƙirarin da wasu jami’an ƙasashen waje suke yi cewa wai ’yan ta’adda a Nijeriya suna kai hare-hare ne kan Kiristoci kawai.

Ya bayyana cewa irin waɗannan iƙirari ba su da tushe kuma ba su bayyana haƙiƙanin yanayin tsaron ƙasar nan, inda ya jaddada cewa ’yancin yin addini yana cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Ya ce: “Wasu daga cikin iƙirarin da wasu jami’an Amurka s**a yi sun ta’allaƙa ne kan bayanai marasa inganci da kuma zato cewa yawancin waɗanda ake kai wa hare-hare Kiristoci ne. E, ana kai wa Kiristoci hari, amma waɗannan miyagun ba mabiya addini ɗaya kawai suke kai wa farmaki ba. Suna kai wa Kiristoci hari, suna kuma kai wa Musulmi hari, musamman a arewacin ƙasar.”

Idris ya ce masu yaɗa irin waɗannan labaran ƙaryar suna taimaka wa ’yan ta’addar ne, saboda manufar ’yan ta’adda ita ce su haddasa rikici tsakanin Musulmi da Kiristoci a ƙasar.

Ya ƙara da cewa Nijeriya ƙasa ce da ta yi yarda da bambancin addinai, don haka yaɗa labaran ƙarya na nuna rashin jituwa zai iya haifar da rarrabuwar kai.

Ya ce: “Kiran lamarin da cewa hare-haren kan Kiristoci ne kawai zai iya haifar da rarrabuwar kai a Nijeriya. Miyagun suna son a ɗauka kamar ana faɗa ne tsakanin Musulmi da Kiristoci. Mun shaida akwai hare-hare kan Kiristoci, kuma mun shaida akwai hare-hare kan Musulmi. Amma ba daidai ba ne a ce Nijeriya ƙasa ce da ba ta mutunta ’yancin addini, ko a ce ko'ina babu tsaro a Nijeriya. Nijeriya ƙasa ce mai aminci.”

Ministan ya amince cewa akwai matsalolin tsaro, amma kuma gwamnati tana ɗaukar matakai masu ƙarfi da tsari don magance su.

Ya bayyana cewa gwamnati ta ƙarfafa rundunonin tsaro tare da zuba jari a fannoni kamar noma da ayyukan jinƙai domin ƙarfafa zaman lafiya.

Ya ce: “Ko canje-canjen da aka yi na shugabannin hafsoshin tsaro kwanan nan duk don a ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar ne, domin gwamnati ta iya magance kowace irin matsala a kan lokaci.”

SANARWA GA JAMA’A GAME DA AIKIN HAINIYA KYAUTA DA MAIGIRMA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR SABUWA YA DAUKI NAUYI GA MUTUM 50.Ma...
29/10/2025

SANARWA GA JAMA’A GAME DA AIKIN HAINIYA KYAUTA DA MAIGIRMA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR SABUWA YA DAUKI NAUYI GA MUTUM 50.

Mai girma Shugaban Karamar Hukumar Sabuwa, Hon Sagir Tanimu Sabuwa, ya ƙara ɗaukar nauyin mutane 50 masu fama da ciwon hainiya domin a yi musu aiki kyauta.

Za a fara gudanar da aikin ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025.

Duk wanda ke da wannan lalura zai iya tuntuɓar kansilansa (councilor) ko kuma zuwa ofishin karamar hukuma domin samun cikakken bayani.

Wannan shiri na daga cikin jajircewar Shugaban wajen inganta lafiyar al’ummar karamar hukumar Sabuwa.

Ziyarar Duba Ayyukan Magudanen Ruwa Waɗanda Shugaban Karamar Hukumar Malumfashi Hon. Mukhtar Abdullahi  City, Yake Gudan...
29/10/2025

Ziyarar Duba Ayyukan Magudanen Ruwa Waɗanda Shugaban Karamar Hukumar Malumfashi Hon. Mukhtar Abdullahi City, Yake Gudanarwa

Kwamitin duba ayyuka da tabbatar da ingancinsu a karamar hukumar Malumfashi, karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin kuma Supervisory Councilor na Ma’aikatar Ayyuka, Hon. Abdullahi Yahaya Karfi, ya kai ziyarar duba ayyuka a wasu sassa na karamar hukumar a ranar Talata, 28 ga Oktoba, 2025.

wuraren da aka ziyarta sun haɗa da Gangarawa Gandu, Unguwar Mata, da kuma Agagiwa, inda ake aiwatar da ayyukan magudanan ruwa domin sauƙaƙa wa al’umma.

A yayin ziyarar, Hon. Abdullahi Yahaya Karfi ya yaba da yadda ‘yan kwangila s**a nuna jajircewa da himma wajen aiwatar da ayyukan da aka basu. Ya kuma yi kira ga sauran ‘yan kwangila da su gaggauta komawa wuraren ayyukan da aka basu domin tabbatar da ci gaban aikin da aka basu.

Ya ƙara da cewa, kwamitin zai ci gaba da bin diddigin ayyukan domin tabbatar da an yi su cikin nagarta da inganci, kamar yadda Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Malumfashi, Hon. Alhaji Mukhtar Abdullahi City, ya umarta.

“Zamu tsaya tsayin daka wajen ganin an yi aiki mai inganci. Duk wani ɗan kwangila da ya yi aiki mara kyau zai fuskanci hukuncin gwamnati,” in ji Hon. Abdullahi Yahaya Karfi.

Kwamitin ya bayyana cewa ziyarar duba ayyuka za ta kasance ta kai-tsaye daga farkon fara aiki har zuwa ƙarshe, ba tare da sanarwa ga ‘yan kwangila kafin zuwan kwamitin ba, domin tabbatar da gaskiya da inganci a duk matakin aiwatar da ayyuka.

Buhari Lawal Mlf.
SSA to the Executive Chairman Malumfashi Local Government.
29/10/2025.

Address

Katsina

Telephone

+2347041418010

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Majalla Post. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Majalla Post.:

Share