Arewa Daily Reporters

Arewa Daily Reporters 📰 Bringing you timely and authentic news from Arewa and across Nigeria. Empowering the region with verified daily reports.

🗳️ 2027: Tinubu Ya Gina Matasa Sama Da Milyan Goma A Arewa – Musa Iliyasu Kwankwaso"Tinubu ya yi ayyukan alkairi da yawa...
28/06/2025

🗳️ 2027: Tinubu Ya Gina Matasa Sama Da Milyan Goma A Arewa – Musa Iliyasu Kwankwaso

"Tinubu ya yi ayyukan alkairi da yawa amma an rasa masu fitowa su fadawa al'umma musamman a Arewa." – cewar Kwankwaso.

Wannan furuci na Musa Iliyasu Kwankwaso ya tayar da tambayoyi da dama:
📌 Shin da gaske matasa fiye da milyan goma sun ci gajiyar gwamnatin Tinubu?
📌 Ayyukan da Tinubu ya yi a Arewa — shin an riga an ga tasirinsu?

🧠 *Kuna ganin wannan ya isa ya tabbatar da nasarar sa a 2027?*

👇 Ku bayyana ra’ayinku a comment. Mu karanta daga gareku!

Idan kanada LINKEDIN account da yakai Shekara 1 zuwa sama da budewa! Akwai hanyar da zaka Rika samun 10k Kowane sati!!!K...
27/04/2025

Idan kanada LINKEDIN account da yakai Shekara 1 zuwa sama da budewa! Akwai hanyar da zaka Rika samun 10k Kowane sati!!!
Kayi mani DM +2348134443592

Bayan Sama Da Shekara Goma Babu Wutar Lantarki A Yankin Kubau Dake Jihar Kaduna, Shugaban Karamar Hukumar Ya Bada Tallaf...
13/04/2025

Bayan Sama Da Shekara Goma Babu Wutar Lantarki A Yankin Kubau Dake Jihar Kaduna, Shugaban Karamar Hukumar Ya Bada Tallafin 'Power Bank' Ga Ma'aikata

Hakan na nuna cewa babu ranar gyara wutar kenan?

"Ni shawarar da zan bawa Kabeer 2pac mai Trending shine, tunda dai Trending din yake son yi da gaske, a videon sa ya dai...
13/04/2025

"Ni shawarar da zan bawa Kabeer 2pac mai Trending shine, tunda dai Trending din yake son yi da gaske, a videon sa ya daina magana.

Sannan ya daina cewa komai saboda Furman abu yafi tafiya viral, amma Idan ya biyewa masu zuwa wajan sa, suna magana a video sai sun durƙusar dashi.

Kawai yadda ka fara content dinka ya karbu, to ka cigaba har sai kayi Trending fiye da yanzu,

~ Cewar jarumin TikTok Abdul Bk

13/04/2025
Uba Sani Ya Mayar Da Jihar Kaduna Birni Da Dawo Mata Da Martabar TaDaga Abubakar SarakiYadda gwamnan jihar Kaduna, Sanat...
07/04/2025

Uba Sani Ya Mayar Da Jihar Kaduna Birni Da Dawo Mata Da Martabar Ta

Daga Abubakar Saraki

Yadda gwamnan jihar Kaduna, Sanata Mallam Uba Sani mai faɗa da cikawa, Ya ci gaba da aikin gyara da sabunta tituna masu amfani da muhimmanci ga al'umma irin su Ahmadu Bello Way da Independence Way da sauran titunan cikin Unguwanni da s**a lalace kuma aka yi watsi da su tun a gwamnatin baya.

Yamzu haka bisa umarnin gwamna Uba Sani mai kishi da son ci gaba, Tuni KADRA sun yi nisa wajen gyara su da shimfida kwalta mai ƙwari da inganci a faɗin ƙwaryar birnin jihar Kaduna.

Kuma idan za ku iya tunawa Sanata Uba Sani, Ya ƙaddamar tare da buɗe wasu sabbin hanyoyi 12 da gwamnatin sa ta shimfiɗa wa kwalta a jihar Kaduna, Da s**a haɗar da:

1- Ja Abdulkadir Road.
2- Bissau Road.
3- Unguwar Mu'azu Township Road.
4- Water Intake Road.
5- Off Yakubu Gowon Residential Layout Road. 6- Kawo Layout Road, Off Ƴan Awaki Road.
7- State House Road Network.
8- Stadium to Station Roundabouts.
9- Residential Layout, Off Gobarau Road.
10- Residential Layout, Off Kinshasa Road.
11- Sultan-Surame Road.
12- Ohinoyi Road.

Kuma hanyoyin an yi su masu inganci da samar da tsaro da wutar lantarki da sauran ingantattun al'amura, Sannan har yanzu akwai muhimman hanyoyi da ya sanya a gaba irin titin da ya taso daga Airport zuwa Tudun Biri da ake yi akwai aikin hanyar Fanteka wanda a Fantake akwai ƴan kasuwa da masu sana'oin hannu da dama wannan ya sa za mu mayar da hankali akai ƙwarai da gaske da sauran su da dama a ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.

Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed.....
05/04/2025

Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed
..Malami ne mara tsoro da ya sadaukar da rayuwarsa wajen karantar da mušùĺùnçìn, wanda jihar Bauchi za ta yi kewarsa
..ya ku mallakawa Almajiransa filin game village

Daga Rariya

A yammacin yau Abasar ne Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Sheik Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ga iyalansa da mabiyansa, wanda ya rasu a daren Juma'ar da ta gabata.

Gwamna Bala wanda ya jagoranci tawagar mukarraban gwamnati, ya kai ziyarar ta'aziyyar ne a madadin kansa, iyalansa, gwamnati da kuma daukacin al'ummar jihar Bauchi.

Gwamnan ya bayyana marigayi Shehin Malamin a matsayin malamin mara tsoro wanda ya sadaukar da kansa wajen karantar da addìnìn musulunci, shari'a da kuma doka. Inda ya ce jihar Bauchi ta yi rashin gwani, masani kuma fasihi.

Gwamnan ya yi fatan Allah ya jikan Sheik Idris Dutsen Tanshi ya sa shi a aljannatul firdausi, Ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin.

A yayin ziyarar jajen, Gwamna Bala ya kuma sadaukarwa mabiyan Malamin filin idi na game village. Ya kuma bayyana cewa ya yafe duk wani rashin fahimata da ya shiga tsakaninsa da marigayin.

Da yake jawabi a madadin iyalan mamacin da kuma al'ummar musulman yankin, Malam Ya'u da Alhaji Shehu Barau Ningi sun mika godiyar su ga Gwamnan bisa ziyarar da ya kawo da kuma irin kalaman da ya yi.

Shehu Barau ya kuma bayyana muhimmancin sake mallaka musu filin na game village, wanda marigayin ya jima yana fatan mallaka.

Daga Lawal Muazu Bauchi
Mai taimakawa Gwamna Bala
Kan harkokin kafafun sadarwar zamani
05/04/25

A hukumance, daga yau hukumar INEC ta amince ‘yan takarar shugabancin Najeriya su yi gangamin yakin neman zabe.Wa za ku ...
28/09/2022

A hukumance, daga yau hukumar INEC ta amince ‘yan takarar shugabancin Najeriya su yi gangamin yakin neman zabe.

Wa za ku zaba a cikin ’yan takarar shugaban kasa?

Ɗan Takarar Shugaban Kasa A Ƙarƙashin Jam'iyyar Labour Party Mista Peter Obi Ya Ziyarci Tsohan Shugaban Kasa Olusegun Ob...
28/09/2022

Ɗan Takarar Shugaban Kasa A Ƙarƙashin Jam'iyyar Labour Party Mista Peter Obi Ya Ziyarci Tsohan Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo Ziyara A Gidansa Dake Otta, Jihar Ogun

Hutuna: Jibwis medical outreach foundation da hadin gwuiwar IMAN ta hijar katsina sun gabatar da training akan yadda ake...
28/09/2022

Hutuna: Jibwis medical outreach foundation da hadin gwuiwar IMAN ta hijar katsina sun gabatar da training akan yadda ake cetar maras lafia ko hadari kafun akai ga likita

Mataimaki na musamman akan harkokin lafiya Dr Adam Ahmad (S.A on medical issues) na shugaban JIBWIS na kasa shine ya jagoranci shirin.

JIBWIS NIGERIA 🇳🇬

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Masu Garkuwa Da Mutane sun zagaye garin Kusa dake a ƙaramar hukumar Jibia dake jihar Katsina, kamar yad...
28/09/2022

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Masu Garkuwa Da Mutane sun zagaye garin Kusa dake a ƙaramar hukumar Jibia dake jihar Katsina, kamar yadda mazaunin garin ya shaidawa wakilin Katsina Online ta wayar salula.

Cikakken rahoton na nan tafe...

Dan Gidan Buhari Ya Sake Dawowa Jam'iyyar APC Biyo bayan ficewar da Hon Fatuhu Muhd daga jam'iyya APC ya tada hankali wa...
28/09/2022

Dan Gidan Buhari Ya Sake Dawowa Jam'iyyar APC

Biyo bayan ficewar da Hon Fatuhu Muhd daga jam'iyya APC ya tada hankali wa mutanen yankin Daura, Sandamu da Mai'Adua wanda jama'a s**a yi ta jimami yanzu ya sake dawowa cikin Jam'iyyar.

An nemi ya dawo ne duba da la'akarin da aka yi da lallai idan bai dawo ba Jam'iyyarza ta iya shan kaye, tunda a lokacin jam'iyyu da dama sun yi zawarcin shi duk da cewar bai amsa goron gayyatar ba.

Daga Musa Lawal Daura

Address

Katsina
811922

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Daily Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Daily Reporters:

Share