28/09/2022
'Yan ta'adda 90,000 ne s**a mika wuya a cikin shekara daya- Zulum
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce sama da 'yan Boko Haram 90,000 ne s**a mika wuya a cikin shekara guda da ta gabata a tsakanin 'yan kungiyar Boko Haram da kungiyar IS a yammacin Afirka.
Gwamnan, a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron da aka shirya a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 a birnin New York, ya ce ‘yan ta’addan da radin kansu sun mika wuya ga rundunar soji domin kwance damara, da kawar da tsattsauran ra’ayi da sake hadewa.
Zulum ya ce wannan bai taba faruwa a ko’ina a duniya ba, kuma yanzu an kawo karshen ta’addanci.
“Ina so in sanar da wannan taron cewa a cikin shekara daya da ta gabata, gwamnatin jihar Borno, da kuma gwamnatin tarayya ya zuwa yanzu ta karbi tubabbun ‘yan Boko Haram da ISWAP sama da 90,000,” inji shi.