Dikko/Jobe Continuity Project 2027

Dikko/Jobe Continuity Project 2027 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dikko/Jobe Continuity Project 2027, Broadcasting & media production company, Sabon Titin Kwado Beside Imam Plaza Katsina, Katsina.

Kungiyar Concern Teachers Forum For Educational Development A Karamar Hukumar Kankara Ta Karrama Sakataren Hukumar Ilmin...
17/08/2025

Kungiyar Concern Teachers Forum For Educational Development A Karamar Hukumar Kankara Ta Karrama Sakataren Hukumar Ilmin Bai Daya SUBEB Reshen Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina



‎Aranar 16/8/2025 Hadaddiyar kungiyar CONCERN TEACHERS FORUM FOR EDUCATIONAL DEVELOPMENT KANKARA ta gudanar taron karamawa da kuma mika wasu kayayyaki ga sakataren hukumar ilmin Bai daya reshen karamar hukumar Kankara Malam Ibrahim Sani PhD.


‎Ajawabin Comr. Nazifi Mansir Yargoje wanda shine Shugaban Kungiyar ya bayyana kungiyar ta Karrama Sakataren ne domin nuna jin dadin ta da ire iren aiyukan cigaba yake Kawowa a fannin Ilmi akaramar hukumar Kankara ta Jihar Katsina tun bayan hawan shi kujerar Shugabancin wannna Shiyyar.


‎Comr Naziru ya Kara dacewa kungiyar Concern Teachers Forum For Educational Development A Karamar Hukumar zata cigaba da bada goyon bayan ta akan dukkanin abubuwan da ya taso afannin ilmi a karamar hukumar Kankara.

‎M'ajin Kunagiyar Hajiya Aisha Lawal ta karane da godewa Sakataren Hukumar Ilmin ta Kankara abisa yake kakkarinfafannin ilmi


‎Takuma Yi fatan ya cigaba da Kawowa yankin dukkanin wasu abubawan cigaban Ilmin yakin kuma zasu marama shi baya akungiyance.


‎Bayan kammala jawabin Hajiya Aisha Comr. Aliyu Nasir ya jawabin nuna jin dadin shi da irin wannan muhimiyar nuna kauna da Kungiyar ta nunama Sakataren ilmin.

‎Aliyu Nasir Kankara ya kuma ba Shuwagabannin Kungiyar shawarwari masu mahimmanci akan yadda zasu kara hamakar Kungiyar.

‎Malam Ibrahim Sani PhD yayi jawabin godiya ga Yayan kungiyar ya bayyana matukar farin cikin shi da irin wannan muhimiyar karramawa dabai tunanin taba.

‎Malam Ibrahim Sani PhD ya yabawa Shugabani da sauran mabiya Kungiyar Zai basu cikakkiyar kulawar domin kawo cigaban Ilmi a karamar hukumar Kankara jihar Katsina.


‎Wasu daga cikin Ya'yan Kungiyar Sun kara bayyana Sakataren da mutum mai kokarin kawo sauyin a fannin Ilmi akaramar hukumar.

‎Daga cikin kayayyakin da kungiyar ta Karrama Sakataren sun hada da kyautar Karramawa ta musanman,Kalanda,Hatimi Mai dauke da Sunan shi.

HOTUNANYadda Wani Kansila Mai Suna Hon. Hassan Safiyanu Yargoje Kewa Al'ummar Mazabar Danmaidaki Aiki."Hon. Hassan Safiy...
25/07/2025

HOTUNAN
Yadda Wani Kansila Mai Suna Hon. Hassan Safiyanu Yargoje Kewa Al'ummar Mazabar Danmaidaki Aiki.

"Hon. Hassan Safiyanu Yargoje matashin dan siyane wanda yakeda zuciyar ganin Al'ummar yankin sunci gaba fiye da kanshi" Hakan yafito ne daga bakin wani mazaunin garin Yargoje ayayin ziyarar Ganin yadda ake gudanar da wani muhimmin aikin hanyar ruwa wato (DRAINAGE) atsakiyar Garin Yargoje dake Karamar hukumar Kankara.

Kamar yadda muka tarar ana cigaba da gudanar da aikin gadar tsallakawa da ababen hawa kebi, muntarar anar gudanar da ita cikin aminci da nagarta.

Munyi kokarin zantawa da Al'ummar yankin da akewa aikin inda wasu dama samu damar hakan s**a nuna matukar farin cikin su dasumawar aikin.

Haka zalika gamida godiya akan yimasu wannan Hanya ruwa mai dauke da Kwalbati, wadda arashinta abaya sun fuskanci rigingimu atsakankanin jama'a yankin da Ruwa ke bi.

Zamu cigaba da kawo maku yadda aikin ke gudana

📷
Rana24

KATSINA COLLEGE KATSINA OLD BOYS ASSOCIATION 2001/2006 GRADUATE'SƘungiyar tsofaffin ɗalibai na kwalejin Katsina watau Ka...
17/06/2024

KATSINA COLLEGE KATSINA OLD BOYS ASSOCIATION 2001/2006 GRADUATE'S

Ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na kwalejin Katsina watau Katsina College Katsina ƴan shekarar 2006 (KCK 2006), a ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar Nura Saulawa

Ana sanarwa tare da gayyatar dukkan mambobinta cewa, akwai taron sada zumunci (kamar yadda aka saba), a gobe sallah 18/06/2024.

Taron zai guda ne a harabar makarantar ta KCK, da misalin ƙarfe 4 na yamma, In shaa Allahu.

Allah Ya Bada Ikon Halarta, Amin.

Sanarwa daga jami'in huda da jama'a na kungiyar Mannir Idris Kankara

Gamayyar 'Ya'yan Jam'iyyar APC Na Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina Sun Kaiwa Maigirama Mataimakin Gwamnan Jihar Kat...
15/04/2024

Gamayyar 'Ya'yan Jam'iyyar APC Na Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina Sun Kaiwa Maigirama Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Ziyarar Barka Da Shan Ruwa.

✍️Mannir Idris Kankara

A ranar 14/4/2024 'Ya'yan Jam'iyya mai mulki a Jihar Katsina ta APC reshen karamar Hukumar Kankara ta ziyarci Maigirama mataimakin Gwamnan jihar Malam Faruk Lawal Jobe (Sarkin Fulanin Joben Katsina)
K
Jagoran tafiyar Alhaji Kabir Jagwa, ayayin jawabin shi ya bayyana sun kaiwa Mataimakin Gwamnan jihar Malam Faruk Jobe ne domin yimashi Sarka da Shan Ruwa.

Jagoran tafiyar yakara dacewar wannan Ziyarar nada nasaba da isar da godiyar al'ummar Karamar hukumar Kankara akan abubuwan alheri da mataimakin Gwamnan ke samarwa karamar Hukumar Kankara.

Alhaji Kabir ya kammala jawabin shi da cewa ziyarar nakara tabbatarwa Mataimakin Gwamnan jihar al'ummar Karamar Hukumar Kankara Tareda dashi dari bisa dari, yakuma jaddada mubaya'a ga duk inda mataimakin Gwamnan yace subi akowane irin matakin mukami.

Shima Sakataren Jam'iyyar APC a Kankara Basiru Busari ya bayyana godiya ga mataimakin Gwamnan duba da yadda yake kokarin kawo cigaba akodayaushe.
Sannan kuma ya kara tabbatar da yin biyayya ga mataimakin Gwamnan ata kowane fanni na siyasa.

Amadadin shuwaganin Jam'iyyar na mazabu shada dake gidan mataimakin Gwamnan Malam Sani Sarka 'Yargoje wanda shine shugaban Jam'iyyar APC a yankin 'Yargoje yace bagudu baja dabaya akan tafiyar gidan Jobe kuma ashirye suke don bada goyon baya.

Hon. Abubakar Murnai kamsilan Mazabar Garagi (Yartsamiyar Jino) Wanda yayi jawabin Amadadin sauran kamsilolin Karamar hukumar Kankara ya nuna matuakar farin cikin duba da yadda tafiyar take samun cigaba fiye da yadda take abaya da kuma yanzu.

Hon. Murnai yace ba abunda zasuyi Allah illa ba godiya ba.

Shima Hon. Aminu Suleiman Wanda yayi magana Amadadin dattawa ya bayyana yanayin mubaya'a ga al'ummar Karamar hukumar Kankara ga mataimakin Gwamnan jihar Katsina abun ayabane matukar Kuma yakara jaddada ba gudu ba ja da baya akan hi

28/03/2024

Jawabin Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Maigirma Faruk Lawal Jobe Yayin Kaddamar Da Rabon Tallafin Da Hon. Shehu Dalhatu Tafoki Yabayar Ga Kananan Hukumomin Dayake Wakilta A Tarayya A garin Kankara

28/03/2024

Mushakata ||

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal Jobe Ya Halarci Rantsar Da Sabbin Sakatarorin Dindin-din Mal. Faruk L...
28/03/2024

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal Jobe Ya Halarci Rantsar Da Sabbin Sakatarorin Dindin-din

Mal. Faruk Lawal Jobe HCIB, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina na daga cikin jiga-jigan jiga-jigan da s**a halarci gagarumin taron rantsar da sabbin Sakatarorin dindindin na Ma’aikatan Jihar guda shida da aka nada.

Mal. Dikko Umaru Raddah, Maigirma Gwamnan Jahar ya rantsar da sakatarorin din-din-din a Red Chamber na Gidan Muhammadu Buhari Katsina.

Rana24 ta ruwaito wadanda aka rantsar sun hada da Jamilu Yakubu Batagarawa (Hukumar Kula da Harajin Cikin Gida), Samaila Yusuf Bindawa ( Min. of Basic And Secondary Education), da Lawal Sulaiman Abdullahi Jibia (Ofishin Shugaban Ma'aikata).

Sauran sun hada da: Hamza Mani Tafashiya daga karamar hukumar Kankia ( Min. of Basic and Secondary Education), Ahmed Hassan Mashi (min. of Finance) da Ibrahim Mu'azu Safana (min. of Finance).

A wani takaitaccen jawabi bayan rantsarwar, Gwamna Mal. Dikko Raddah ya bayyana rantsuwar a Sakatororin don ƙara ƙima ga ma'aikatan gwamnati kamar yadda ya yi musu gargaɗi game da aikata badaidaiba

Dan-majilisar Dattawa Sen. Muntari Mohammed Dandutse Ya Gwagwaje Al'ummar Karamar Hukumar Kankara Da Kudade.Daga: Mannir...
21/03/2024

Dan-majilisar Dattawa Sen. Muntari Mohammed Dandutse Ya Gwagwaje Al'ummar Karamar Hukumar Kankara Da Kudade.

Daga: Mannir Idris Kankara

A yau Laraba Dan-majalisar Dattawa yankin Katsina ta kudu Sen. Muntari Mohammed Dandutse ya rabawa mutane 400 N10,000 a karamar hukumar kankara.

Hon. Abubakar Nuhu wanda shine jagoran wakilan da s**a gudanar da rabon kudaden wadanda s**a zo daga garin Funtua ya fara da bayyanawa Mutanen das**a amfana da sakon godiya daga Danmsjilisar ga Al'immar karamar hukumar ta kankara bisa nuna kauna da goyon bayan da suke nuna mashii.

Sannnan ya kuma tabbatar da akwai wasu ayyukan alheri dake tafe zuwa garin na kankara Wanda Sanatan yasamo daga tarayya daga bisani ya lissafawa al'umma yadda tsarin rabon kudin yake zuwa kaso 4.

Kason farko akwai Malamai 100, 50,50 daga Darika da Izala, Mata 100,Dattawa 100 sainkuma matasa 100 Wanda jimillar s**a kai 400 Inda kowa yasamu kunshin N10, 000 hannu da hannu.

Malam Hamisu Donawa na daya daga cikin kwamitin rabon ya bayyana sun kasa rabon shiyyoyi 11 na mazabun da karamar hukumar ta kunsa, wanda Hakan yasa mutanen wajen gari sun amfana matuka.

Daya daga cikin Malaman da s**a amfana Malam Abdulrashid ya yaba sosai da wannan tsari domin zai ragewa mutane radadin halin da ake ciki, shima Malam Isah ya godewa Danmajilisar gamida yin addu'a ta Kara samun cigaba.

Mata da Maza dama ne s**a kasance cikin farin ciki.

Nazir Isiya wanda shine mai taimakawa wajen biyan Malamai Addini ya yaba da halin dattakon da aka nuna.

Haka zalika shima Aliyu shehu dake bangaren biyan mata ya nuna godiya da yadda matan s**a nuna yayin tantacewa.

Sauran Yan kwamitin tafiyar da rabon kudin sun hada da Bature Omo, Shamsuddeen Magaji, Abdulbasir Maihoto, Danjuma Direba da Kuma Sadiq Pauwa.

Anyi rabon batare da samun Wani tarnakiba.

MACE MAI KAMAR MAZA : Mai Baiwa Gwamnan Jihar Katsina Shawarma Akan Huddatayyar Gwamnatoci Excmo. Hadiza Hassan Maikudi ...
18/03/2024

MACE MAI KAMAR MAZA : Mai Baiwa Gwamnan Jihar Katsina Shawarma Akan Huddatayyar Gwamnatoci Excmo. Hadiza Hassan Maikudi Ta Rabawa Al'umma Buhunnan Shinkafa 40.

Honorable. Hadiza Hassan Maikudi wadda itace maibaiwa Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ta bayar da manyan Buhunnan shikafa masu nauyin 50 ga al'umma.

Kamar yadda wakilin mu ya tabbatas anyi rabon shinkafar ne Farfajiyar sabuwar Kasuwar Kankara wadda akafi sani da Modern Market dake kan titin Zuwa garin Dutsinma cikin garin Kankara. Shinkafar buhunna 40 masu nauyin 50 kowannanen su.

Ayayin jawabin shi Wakilin Rabon Shinkafar Ingr. Abdulbasir Gambo Kankara ya bayyana "Wannan rabon shinkafa Hajiya Hadiza tayine domin tallafawa al'umma domin Allah da zummar ragewa jama'a wahalhalin alfarmar wantan wata na Ramadán.

Al'umma sun Yaba da yadda Ingr. Abdulbasir ya tsaya Kai da fata tun daga farko rabo har karshen rabon wantan shinkafa.

Maitaimakawa gwamnan jihar Katsina ta fannin samar da labarai daga karamar hukumar kankara Muhammad Sale OC (Manga) wanda shima dayane daga masu rabon wannnan shinkafa Kuma daga cikin matasan da suke goyawa Excmo. Hadiza Baya ya tabbatar cewa wantan kadan ne daga cikin alkairan da Hajiyar keda zummar samawa al'umma.

Wasu daga cikin wadanda s**a amfana da wantan shinkafa sun yaba da wantan taimako datayi musanman acikin irin want yanayi da ake ciki na rayuwa. Sun Kuma Yi addua'ar Allah ya jikan iyayenta yasa agama da duniya Lafiya.

Daga cikin wadanda s**ai aikin rabon sun hada da Malam Ibrahim Gerente, Excmo. Aminu Suleiman da Sauransu

📷Rana24

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe Ya Kai Ziyarar Ta'azziyar Ga Iyalan Shugaban Hukumar Tsaron C-Watch Na...
23/02/2024

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe Ya Kai Ziyarar Ta'azziyar Ga Iyalan Shugaban Hukumar Tsaron C-Watch Na Karamar Hukumar Kankara.

✍️Mannir Idris Kankara

A ranar Alhamis 22/2/2024 Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Maigirma Malam Faruk Lawal Jobe yakai Ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Malam Sanusi Hassan Kankara Shugaban hukumar Tsaro ta jihar Katsina.

Malam Sanusi ya yagamu da ajalin shi tahanyar harbin bindiga awata musayar wuta da aka gwabza da Yan ta'addar daji ajiya Laraba.

Ayayin ziyarar ta'aziyyar maigirma mataimakin Gwamnan Faruk Lawal Jobe ya jajantawa Iyalan Marigayin haka zalika yayi Addu'ar naman gafara ga mamacin da fatan Aljanna ce makomar shi.

Waɗanda s**a rufa mashi baya sun hada Kwaminshinan Ayyuka na musanman Alhaji Isah Mohammed, Shugaban gudanarwar na Babban Asibitin Garin Katsina Dr. Mohammed Umar Zango da sauran Al'umma.

Yakumayi Addu'ar Allah ya kawo tabbatacen zaman lafiya a karamar hukumar Kankara, Jihar Katsina da Najeriya baki daya

Gidauniyar Kankara Ke Gabanmu (KKG)Ta Daukewa Mutane 118 Nauyin Sayen Katin Ganin Likita Hadida Yimasu Awon Cututtuka A ...
17/01/2024

Gidauniyar Kankara Ke Gabanmu (KKG)Ta Daukewa Mutane 118 Nauyin Sayen Katin Ganin Likita Hadida Yimasu Awon Cututtuka A Garin Kankara Jihar Katsina.

Daga : Mannir Idris Kankara

A ranar Talata 16/1/2024 Gidauniyar Kankara Ke Gabanmu ta gudanar da aikin rabon katin ganin Likita Kyauta ga dukkan mara lafiyar da yaje da zummar ganin Likitan Asibitin kiwon lafiya matakin farko a Garin Kankara Jihar Katsina baki daya.

Rabon katin ganin Likitan daya gudana a Asibitin cikin garin Kankara ayau Talata majiyar Rana24 data ruwaito Waɗanda s**a amfana da rabon kati sun Kai kimanin su 118 ne.

Waɗanda S**a Amfana da wannan Shirin sun hada da mata da Maza wadanda s**a fito da daga sassan kauyuka da cikin garin karamar hukumar Kankara.

Haka zalika wannan gidauniyar ta dauki nauyin biyan Kuɗaɗen awon Cututtuka da s**a shafi kowace irin rashin lafiya awannan Ranar, irinsu awon matan masu dauke da juna Biyu, awon masassarar cizon sauro,tayfod,da sauran awon matsalolin da al'umma ke fuskanta.

Azantawar wakilin mu da wasu daga cikin matan da s**a samu amfana da wannan shirin fannin Mata masu ciki Sun Mai suna Murja Hashimu wadda tafito daga wajen garin Kankara ta bayyana matukar jin dadin dataji na daukar nauyin saymi mata katin Awo da biya mata Kuɗin Awon cikin da wannan gidauniyar tayi takumayi Addu'ar Allah ya bada abinda ake nema na Alheri ya kuma kara awo irin Waɗannan Kungiyoyin dake tsllafawa al'umma akaramar Hukumar Kankara.

Isma'il Alhassan na cikin Waɗanda s**a amfana daga bangaren Maza wanda shima ya fito ne daga garuruwan Wajen garin Kankara ya yaba da Matuka da samun wannan tallafin dauke mashi biyan Kuɗaɗen awon matsalar data sashi yazo Asibitin.

Hon. Tajjuddeen Modoji Kankara wanda shima yasamu wannan taimakon gidauniyar afannin yaron wajenshi dake fama da rashin lafiya ya godewa Shugaban wannan gidauniyar da Kuma Ma'aikatan das**a gudanar da aikin bisa tsari das**a shirya.

Shuagaban Hukumar Kiwon Lafiya Amatakin Farko na Karamar hukumar Kankara Alhaji Abdulsalam Jikamshi ya yaba Matuka da Kuma yin Addu'ar Allah yakara daukaka wannan gidauniyar da kuma Kiran da acigaba kokarin akan irin Waɗannan aiyukan ahairai ga al'umma.

Shiman shuagaban kula da alluran lokaci zuwa lokaci Kuma shugaban Kungiyar Ma'aikatan Lafiya A na karamar hukumar Kankara Alhaji Aliyu Ibrahim Ketare ya Jaddada koyon baya ga kudurorin wannan gidauniyar aduk lokacin data ke Bukatar Wani Daya shafi fannin Kiwon Lafiya.

Kungiyoyi Sama Da 15 S**a Amfana Da Shirin FADAMA KATSINA NG-CARE A Karo Na 2 A Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina.Da...
05/01/2024

Kungiyoyi Sama Da 15 S**a Amfana Da Shirin FADAMA KATSINA NG-CARE A Karo Na 2 A Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina.

Daga : Mannir Idris Kankara.

A ranar 4/1/2024 aka rabawa Al'ummomi kayan dogaro dakai akaramar Hukumar Kankara Jihar Katsina Karkashin Maitaimakin Gwamnan Jihar Katsina Maigirma Malam Faruk Lawal Jobe,,(Sarkin Fulanin Joben Katsina) a shirin FADAMA KATSINA NG-CARE

Taron rabon kayan ya wakana ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mannir Halliru Jobe hadi da taimakon Malam Ishaq Bashir da wasu matasa Yan siyasa a cikin Kasuwar da ake kira Mordern Market dake kan hanyar zuwa garin Dutsinma a Kankara.

Ajawabin shi Alh Mannir Halliru Jobe wanda shine ya jagoran rabon kayayyakin yayi kira ga dukkanin Waɗanda s**a amfana da Suyi amfani da Waɗannan abubuwan Alheri kamar yadda ya dace, domin alfanon yan baya.

Mannir Halliru yakuma taya dukkanin Waɗanda s**a amfana murnar samun Waɗannan abubuwan Waɗanda kuma basu samu ba dasu kara hukuri zuwa nan gaba akwai wasu shirye shiryen makamanta irin Waɗannan dake tafe.

Kamar yadda Rana24 ta ruwaito wannan rabon abun arziki shine karo na 2 da al'ummar Karamar hukumar Kankara s**a amfana kamar sauran wasu Kananan hukumomin Jihar s**a amfana dashi.

A ruhoton da muka nakalto mako idan zaku iya tunawa ko a makon daya gabata a awaitar da rabon kayayyakin arziki Waɗanda s**a hada da Dabbobi jinsin kaji,Awaki,Injinan Markade,Injinan ban ruwa na miloyin nairori ga Al'umma garin na Kankara.

Haka zalika wakilin mu ya tabbatar ko awannan karon Kungiyoyi 15 ne masu dauke da 'ya'yan Kungiya kimanin 20 azuwa 40 da aka lalubo daga Ɓangarorin na Karamar hukumar Kankara maza da Mata s**a amfana da Injinan hudar gona na zamani 15, Injinan Markade 12, Injinan murzar tunkuza 2,kajin turawa 2000 daidai sauran kayayyakin dogaro dakai.

Jama'a da damane s**a nuna farin cikin su akan wannan Lamari na rabon kayayyakin arziki da Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina ke samarwa a Kankara.

Umar Bature Darda'u (BACHO) ya Tabbatar da godiyar shi, Mal

Address

Sabon Titin Kwado Beside Imam Plaza Katsina
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dikko/Jobe Continuity Project 2027 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share