24/08/2026
Maigirma Sanata Dandutse Ya Jagoranci Taron Wayar Da Kai Kan Lamunin Karatu A Jami’ar Uyo
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Manyan Makarantu Da Tetfund, Sanata Muntari Muhammad Dandutse, Ya Jagoranci Wani Mahimmin, Taron Wayar Da Kai Kan Shirin Lamunin Karatu Na Gwamnatin Tarayya A Jami’ar Uyo, Da Ke Jihar Akwa Ibom.
Sanata Dandutse, Wanda Ke Wakiltar Mazabar Katsina Ta Kudu A Majalisar Dattawa, Ya Jagoranci Taron Wayar Da Kan Jama’a Kan Asusun Lamunin Ilimi Na Najeriya (Nelfund), Wanda Ya Haɗa Masu Ruwa Da Tsaki A Fannin Ilimi Daga Sassa Daban-daban Na Ƙasar.
An Gudanar Da Taron Ne Ƙarƙashin Taken: “faɗaɗa Damar Samun Ilimi Mai Zurfi Ta Hanyar Samar Da Ingantaccen Tsarin Tallafin Kuɗin Karatun Ɗalibai.”
Taron Ya Mayar Da Hankali Ne Kan Yadda Za A Ƙara Fahimtar Shirin Lamunin Karatu Na Gwamnatin Tarayya Da Kuma Faɗaɗa Damar Ɗaliban Najeriya Samun Kuɗin Da Za Su Taimaka Musu Wajen CI Gaba Da Karatu.
A Jawabinsa, Sanata Dandutse Ya Ce Wayar Da Kan Ɗalibai Da Cibiyoyin Ilimi Game Da Shirin Na Da Muhimmanci, Domin Su Fahimci Yadda Tsarin Yake Da Kuma Matakan Da Ake Buƙata Domin Cin Gajiyarsa.
Ya Ce Haɗa Masu Ruwa Da Tsaki Daga Shiyyoyin Siyasa Shida Na Ƙasar Zai Taimaka Wajen Ƙara Wayar Da Kai, Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Tsakanin Cibiyoyin Ilimi Da Kuma Faɗaɗa Damar Samun Tallafin Kuɗin Karatu Ga Ɗalibai.
Jami’ar Uyo Ce Ta Karɓi Baƙuncin Taron, Wanda Ya Samu Halartar Wakilin Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Kwamishinan Ilimi, Farfesa Ubong Umoh, Da Shugabannin Manyan Makarantu, Magatakarda, Shugabannin Tsangayu, Farfesoshi Da Sauran Masu Ruwa Da Tsaki A Fannin Ilimi.
Bayan Kammala Taron, Shugaban Kwalejin Ilimi Ta Tarayya Da Ke Ididep, Dakta Wilson Udo Udofia, Ya Yaba Wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu Bisa Ƙaddamar Da Shirin Nelfund.
Dakta Udofia Ya Ce Shirin Zai Taimaka Wajen Rage Matsalar Kuɗin Karatu Da Wasu Ɗalibai Ke Fuskanta, Musamman Waɗanda S**a Cancanta Amma BA Su Da Isassun Kuɗaɗen CI Gaba Da Karatunsu.
Ya Ce Kwalejin Ilimi Ta Tarayya Da Ke Ididep Za Ta Yi Aiki Tare Da Nelfund Da Sauran Hukumomin Da Abin Ya Shafa Wajen Wayar Da Kan Ɗalibai, Domin Tabbatar Da Cewa Waɗanda S**a Cancanta Sun Samu Bayanai Da Jagorancin Da Ya Dace.
Shugaban Kwalejin Ya Kuma Yaba Wa Mataimakin Shugaban Jami’ar Uyo, Farfesa Chris Ekong, Da Sauran Jami’an Jami’ar Bisa KarɓAR Baƙuncin Taron.
Ya Ce Irin Waɗannan Shirye-shirye Na Samar Da Damar Da Cibiyoyin Ilimi Da Ɗalibai Ke Samu Wajen Fahimtar Shirin Lamunin Karatu Da Kuma Yadda Za Su Amfana Da Shi.
Dakta Udofia Ya Jaddada Cewa Kwalejin Za Ta CI Gaba Da Mayar Da Hankali Wajen Horas Da Malaman Najeriya Na Ƙarni Na Gaba, Yana Mai Cewa Saka Hannun Jari A Ɗalibai Na Daga Cikin Hanyoyin Gina Makomar Ƙasar.
Shugaban Kwalejin Ya Samu Rakiyar Ma’aji Samuel Oyighocho, Magatakarda Wanda Mista Godwin Solomon Enang Ya Wakilta, Shugaban Harkokin Jin Daɗin Ɗalibai, Dakta John Paul, Mukaddashin Daraktan Fasahar Sadarwa Da Sauran Jami’an Kwalejin.
Ana Sa Ran Taron Zai Ƙara Wayar Da Kan Manyan Makarantu Da Ɗalibai A Shiyyar Kudu Maso Kudu Game Da Shirin Nelfund, Tare Da Ƙara Yawan Ɗaliban Da Za Su Amfana Da Tallafin Kuɗin Karatu Na Gwamnatin Tarayya.
Dandutse Media Reporter Funtua Zone