31/08/2026
Gwamna Dikko Umaru Radda ya samu kyaututtuka guda uku daban-daban don girmama gudunmawar da ya bayarwa ga cigaban wasanni a jihar Katsina.
Ƙungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya, Ƙungiyar Katsina Fives Association da kuma Ƙungiyar Marubuta Gasar Wasanni ta Najeriya reshen jihar Katsina s**a bayar da kyaututtukan.
Kwamishinan Bunƙasa Rayuwar Matasa da Cigaban Wasanni, Injiniya Suraj Yazeed Abukur da kuma Mai Bada Shawara na Musamman kan Cigaban Matasa, Ahmed Lara Malumfashi ne s**a bayar da kyaututtukan ga Gwamnan a gefen taron Majalisar Zartarwa ta Jiha.
Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafar ta yaba ma Gwamna Radda bisa goyon bayan da ya bayar ga gasar share fagen kaka ta Katsina ta 2026, wadda tsohon Shugaban Ƙungiyar, Ibrahim Gusau ya shirya.
Gwamna ya cigaba da goyon bayan gasar da sauran shirye-shirye da nufin bunƙasa cigaban ƙwallon ƙafa da kuma samar da damammaki ga matasa 'yan wasa a jihar Katsina.
Ƙungiyar Katsina Fives ta kuma bai wa Gwamna Radda kyautar yabo bisa cigaba da goyon bayan da yake bai wa ƙungiyar.
Kyautar na yaba ma tallafin da ya bayar wajen shiga gasar da wata gasar a faɗin Najeriya da kuma sauran wasannin motsa jiki na ƙasa da ƙasa..
Haka nan kuma, ƙungiyar marubuta wasanni reshen jihar Katsina ta bai wa Gwamna Radda kyautar girmamawa.
Kyautar ta yaba wa goyon bayan gwamnatinsa ga ayyukan wasanni da shirye-shiryen da ƙungiyar ta shirya.
Da yake karɓar kyaututtukan, Gwamna Radda ya gode ma ƙungiyoyin bisa yaba ma gudummawar da ya bayar ga cigaban wasanni.
Ya ce da goyon bayan gwamnati da na ɓangarori masu zaman kansu, matasa za su iya lashe kyaututtuka ga jihar Katsina da Najeriya a gasar ƙasa da ƙasa.