Chake Online Media

Chake Online Media Wannan Shafin Na Chake Online Media Zai Rinka Kawo Maku Ingantattun Labarai, Da Kuma Labaren Nishad A Chake Online Media.

Wannan Shafin Na Chake Online Media Zai Rinka Kawo Maku Ingantattun Labarai, Da Kuma Labaren Nishadi Na Yau Da Kullin. Bazan Muci Mutuncin Kowa Ba, Zamuyi Aiki Akan Abinda Muka Sani Ko Kuma An Tabbatar Mana Da Gaskiyar Labari

Ku Kasance Da Mu Koda Yaushe.

16/07/2025

"Ka Tsoraci Mu'amala Da Mutumin Da Baya Iya Yafewa Matacce"

05/02/2025

👉👂

Sakon Prof. Usman Yusuf Daga Kurkukun KujeAssalamu Alaikum jama’a.Ina gaisuwa daga gidan yarin Kuje. Na gode wa kowa da ...
05/02/2025

Sakon Prof. Usman Yusuf Daga Kurkukun Kuje

Assalamu Alaikum jama’a.

Ina gaisuwa daga gidan yarin Kuje. Na gode wa kowa da kowa bisa goyon baya da kulawarku.

Ina cikin koshin lafiya sosai a sashin VIP, inda muke cin abinci tare da yin ibada cikin natsuwa, nesa da hayaniyar taron jama’a. Ina da isashen lokaci na hutawa, bacci, da karatu.

Allah ya fada a Suratul Baqara cewa:
"Allah ba ya dorawa kowa nauyin da ba zai iya dauka ba."

Tun da dadewa na daga hannuwana na ce wa Allah zan iya daukar nauyin fadin gaskiya kan zalunci, don haka ya taimake ni. Yanzu na samu kwanciyar hankali da natsuwa fiye da kowane lokaci a rayuwata.

Iyali na suna cikin koshin lafiya kuma suna da ƙarfin gwiwa.
Na gode wa kowa da kowa.

Shugaban JIBWIS yayi ƙira da a daina yaɗa hoton bidiyon matar albani Zariya.Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau, y...
03/02/2025

Shugaban JIBWIS yayi ƙira da a daina yaɗa hoton bidiyon matar albani Zariya.

Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi ƙira ga 'yan uwa masu yaɗa hoton bidiyon matar marigayi Sheikh Auwal Albani Zariya a kafafen sada zumunta da suyi haƙuri su daina yaɗa wannan hoto. Sheikh Bala Lau ya ƙara da cewa, zai naɗa kwamiti cikin sauri da zasu bibiyi lamuran domin kawo ƙarshen dambarwan.

A ƙarshe ya baiwa dukkan bangarorin haƙuri, yace su jira har zuwa lokacin da kwamitin zasu iso domin fara ayyukan nasu Insha Allah.

Jibwis Nigeria

Sabuwar hanyar zaluntar mutane ta “3rd Party Insurance”Daga Jaafar Jaafar Aiwatar da dokar biyan mafi kankancin inshorar...
02/02/2025

Sabuwar hanyar zaluntar mutane ta “3rd Party Insurance”

Daga Jaafar Jaafar

Aiwatar da dokar biyan mafi kankancin inshorar mota wadda ake kira “3rd Party Insurance”, manufa ce ta neman tatsar aljihun mutane.

Tun da ka ji ‘yansanda sun dage sai sun aiwatar, to kuwa ka san da dalili. Tsakani da Allah kashe-mu-raba kawai za su yi da kamfanonin inshorar, kai watakil ma wasu daga cikin manyan na da hannun jari a kamfanonin. Kwata-kwata ba kishin aiki ne ya sa ‘yansanda ke ta haƙilo ba.

Ita inshorar mota wani kuɗi ne da za a biya wa duk motar da ake hawa a duk shekara ko duk wata. Amfanin kuɗin shi ne duk lokacin da aka buga maka mota, ko ka yi hatsari ko wani ibtila’i ya faru, to kamfanin inshora zai gyara, ko ya siya ma mak**anciyar ta. Duk da cewa ‘yan Nigeria na biya in za su sayi ko za su sabunta takardun mota, amma ban taɓa jin wanda kamfanin inshora ya gyara wa mota ba, b***e ya siya mai sabuwa.

A nan Ingila duk wata mu ke biyan inshorar mota, sai dai in ka zaɓi ka biya gaba ɗaya. Kuma kamfanonin ba sa ƙasa a gwiwa wajen gyara ko siya wa mutum sabuwar mota. Ni karan kaina duk watan duniya sai na biya wa mota ta inshora kimanin naira 260,000 kuma duk watan duniya sai na biya mata harajin hanya kimanin naira 30,000 kuma duk shekara sai na biya kimanin naira 110,000 domin duba lafiyarta.

Amma me ya sa mutum zai biya inshora a Nigeria tunda kamfanonin inshora ba sa gyara ko siya wa mutum mota in ta yi haɗari? Rashin gaskiya ya yi mana katutu a Nigeria, tun daga kan hukumomi har jama’a. Baya da haka, a Nigeria ba a yin gwajin lafiyar mota (MOT test) duk shekara. A shekaru da su ka gabata da na san a Nigeria ana sa wa motar da bai k**ata ta hau t**i ba “OFF THE ROAD”, amma ba na jin yanzu ana yi. Dalilin haka shi ne, idan motar ta lalace a kan hanya, za ta iya jawo haɗarin zai iya sa wa a yi asarar rai.

A ƙasar Ingila idan sahihin garejin gwajjn lafiyar mota (MOT centre) bai tabbatar da lafiyar mota ba kuma bai ba da satifiket ba, to ba za ka hau motar ba. Duk motar da ba ta inshora ko MOT ko haraji, tana gittawa ‘yansanda za su gani a sikanar da ke motocinsu, kuma za su k**a motar.

A ƙasashen da su ka ci gaba, idan motarka ta faɗa ‘pothole’ ta lalace, za ka iya neman gwamnati ta biya ka diyya. A Nigeria fa? A lokacin da ina Nigeria, zai wahala na je Kano daga Abuja sau uku ban fasa taya ko shakzoba ba.

Batun gaskiya shi ne, su kan su kamfanonin inshora a Nigeria sun san karya ce kawai. Domin idan tsakani da Allah za su riƙa biya, faɗuwar (risks) ta fi ribar yawa. Babu kamfanin kasar waje da zai yadda ya yi harkar inshora a kasar da ba a koyon tuki bisa kaida, ba a ƙayyade gudu a kan t**i, babu kyamarar k**a wanda ya wuce ƙa’idar gudu, babu alamu a gefe, babu zanen layi radau a kan tituna, sannan kuma ga ramuka fal hanya.

Buƙatar sakin hambararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum na ƙara ƙaruwa a faɗin duniya, tsakanin lauyoyinsa, ƴan gwagwar...
01/02/2025

Buƙatar sakin hambararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum na ƙara ƙaruwa a faɗin duniya, tsakanin lauyoyinsa, ƴan gwagwarmaya da hukumomin ƙasa da ƙasa, a wani yanayi da tuni takardar koken da ke buƙatar sakinsa ta isa birnin Washington.

Sayyuduna Rasulillahi ( ﷺ ) Yace: “Ku TAusayawa Marayu (Hakan Zai Sanya) Allah Madaukakin Sarki Ya Tausaya Mana Sannan K...
15/09/2023

Sayyuduna Rasulillahi ( ﷺ ) Yace: “Ku TAusayawa Marayu (Hakan Zai Sanya) Allah Madaukakin Sarki Ya Tausaya Mana Sannan Ku Tuba Zuwa Ga Allah Madaukakin Sarki Daga Dukkan Zunubbanku

Sannan Kuma Ku 'Daga Hannuwanku Da Addu’o’i A Lokuttan Sallolinku Domin (Lokuttan Sallolinku) Sune Sa’o’in Da S**a Fi Falala Allah Madaukakin Sarki Zai Dubeku Da Rahamara

Ya Ubangijin Annabi Muhammadu ( ﷺ )! Ka Bamu Ikon Farantawa Marayu Da Sauran Al'ummar Sayyuduna Rasulillahi ( ﷺ )🙏

Juma'at Kareem 🕌📿🕋🙏

Mai Girma Sardaunan Galadiman Katsina Alh Ibrahim Teacher Na Masari Maji Dadin Marayun Katsina

ABIŃ A YABÀ: Laylah Ali Othmań Ta Daùke Yaron Da Mahaidiyaraa Take Muzguna Masa Saboda Ba Shi Ba Lafiya, Inda Zai Cigaba...
14/09/2023

ABIŃ A YABÀ: Laylah Ali Othmań Ta Daùke Yaron Da Mahaidiyaraa Take Muzguna Masa Saboda Ba Shi Ba Lafiya, Inda Zai Cigaba Da Zama A Wajenta

Idan za a iya tunawa dai, an ga bidiyon yaron ne a social media, inda mahaifyar tasa take aibata shi da cewar aljani ne ta gaji da rainonsa, maganganu kala-kala na tozarta dan Adam saboda yaron yana da larura, bayan bidioyon ya fita hankalin mutane ya tashi ko ni sai da na yi kuka saboda halin wahala da tsangwama da yaron ke ciki kuma a hannun uwarsa.

Daga karshe Laylah Ali Othman ta ce tana son yaron, a bata shi za ta cigaba da renonsa, inda daga karshe tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Mansura Isa ta je har garin Yola ta dauko yaron daga gurin mahaifiyarsa da ta dinga kuka tana rokon a yafe mata abun da ta yiwa yaronta, yanzu dai Laylah Ali Othman ta amshi yaron ya zama danta za ta kula da lafiyarsa.

Wannan shine yaro na uku da iyayansa s**a saki a duniya Layla ta dauka ta rike a matsayin danta ta ke musu komai, muna adduar Allah Ubangiji ya saka miki da alkairi Layla, Allah ya faranta miki duniya da lahira amin.

Daga Fauziya D. Sulaiman

Ramatu Tijjani Aliyu Ta Dauki Nauyi Kawo Maku ;: Ramadan Day 7FALALAR WATANRAMADAN MAIALBARKA !!!•ALLAH mai girma dadauk...
29/03/2023

Ramatu Tijjani Aliyu Ta Dauki Nauyi Kawo Maku ;: Ramadan Day 7

FALALAR WATAN
RAMADAN MAI
ALBARKA !!!
•ALLAH mai girma da
daukaka yace: "Waccan
wata falala ce ta
ALLAH yana bayar da
ita ga wanda yaso,
kuma ALLAH ma'abocin
daukakar falala ne mai
girma"
(surah ta 62 aya ta 4)
Yana daga cikin abunda
babu sa6ani a tsakanin
malamai game da shi
cewa lallai watan
Ramadan watane mai
alkhayri da albarka
wanda ALLAH ya
ke6ance shi da falala
mai yawa, k**ar yadda
wannan bincike zai
bayyana.
•ALLAH mai girma da
buwaya ya sauqar da
littafinsa a matsayin
shiriya ga mutane da
waraka ga muminai da
hujjoji bayyanannu daga
shiriya da kuma rabewa
(tsakanin qarya da
gaskia). Yana shiryarwa
zuwa ga hujja mafi
qarfi kuma da yana
bayyana tafarkin
shiriya. An sauqar dashi
ne a daren LAILATUL
QADRI daren daraja
acikin watan Ramadan
mai alkhairai.
•ALLAH (SWT) yana
cewa: "Watan Ramadan
ne wanda ALLAH ya
sauqar da Alqur'ani a
cikinsa yana shiriya da
rarrabewar (gaskia da
qarya) to wanda ya
halarci watan daga cikin
ku sai ya azumce sa….

Rana Ta Biyar 5 Abubuwa Daya Kamata Kusani Acikin Watan Ramadan: Daukar Nauyi Daga Hajiya Dr. Ramatu Tijjani Aliyu State...
27/03/2023

Rana Ta Biyar 5 Abubuwa Daya Kamata Kusani Acikin Watan Ramadan: Daukar Nauyi Daga Hajiya Dr. Ramatu Tijjani Aliyu State FCT Minister.

1. Azumin watan Ramalana daya ne cikin rukunan Musulunci guda biyar.

2. A cikinsa ake samun daren Lailatul Qadri wanda falalarsa tafi na darare dubu, kimanin daren shekara 83 da wata hudu.

3. Tun daga farkon watan zuwa karshen ake bude kofofin Aljannah a rufe kofofin Wuta a sanya Shaidanu cikin dabaibayi.

4. Azumtar Watan Ramalana ke sanyawa a gafartawa Mutum abin da ya gabata na kura-kuransa.

5. A cikin Watan Ramalana a Daren Lailatul Qadr Allah ke saukar da bayanin abin da ya hukunta faruwarsa na shekarar bana zuwa shekara mai zuwa k**ar yadda Al'qurani ya ambaci hakan a Suratul Qadri. (INNA ANZALNAHU FI LAILATIL QADRI)

6. Sadaka a watan Ramalana ta fi lada. An tambayi Annabi kan wace Sadaka ce ta fi? Sai ya ce: "Sadaka a Watan Ramalana".

7. A cikinsa Allah ya saukar da Alqur'ani dungurungum zuwa Baitul Izzah a sama ta farko, daga nan aka saukar wa Annabi Muhamamdu SAW a rarrabe.

8. Shi ne watan da in ka yi tsayuwar Sallah don neman lada a dararensa Allah ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubanka k**ar yadda Annabi ya ce.

9. A cikin kowane dare na Watan Ramalana ne Allah ke 'yanta bayinsa masu dumbin yawa daga cancantar zaman Wuta zuwa Aljannah.

10. Shi ne watan da yin aikin Umara a cikinsa yake daidai da Aikin Hajji da Manzon Allah k**ar yadda Annabin ya fada a Hadisi.

Day 3 :  Wasu Daga Cikin Muhimman Abubuwa Daya Kamata Kusani Acikin Watan Ramadan: Daukar Nauyi Daga Hajiya Dr. Ramatu T...
25/03/2023

Day 3 : Wasu Daga Cikin Muhimman Abubuwa Daya Kamata Kusani Acikin Watan Ramadan: Daukar Nauyi Daga Hajiya Dr. Ramatu Tijjani Aliyu State FCT Minister.

1. Azumin watan Ramalana daya ne cikin rukunan Musulunci guda biyar.

2. A cikinsa ake samun daren Lailatul Qadri wanda falalarsa tafi na darare dubu, kimanin daren shekara 83 da wata hudu.

3. Tun daga farkon watan zuwa karshen ake bude kofofin Aljannah a rufe kofofin Wuta a sanya Shaidanu cikin dabaibayi.

4. Azumtar Watan Ramalana ke sanyawa a gafartawa Mutum abin da ya gabata na kura-kuransa.

5. A cikin Watan Ramalana a Daren Lailatul Qadr Allah ke saukar da bayanin abin da ya hukunta faruwarsa na shekarar bana zuwa shekara mai zuwa k**ar yadda Al'qurani ya ambaci hakan a Suratul Qadri. (INNA ANZALNAHU FI LAILATIL QADRI)

6. Sadaka a watan Ramalana ta fi lada. An tambayi Annabi kan wace Sadaka ce ta fi? Sai ya ce: "Sadaka a Watan Ramalana".

7. A cikinsa Allah ya saukar da Alqur'ani dungurungum zuwa Baitul Izzah a sama ta farko, daga nan aka saukar wa Annabi Muhamamdu SAW a rarrabe.

8. Shi ne watan da in ka yi tsayuwar Sallah don neman lada a dararensa Allah ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubanka k**ar yadda Annabi ya ce.

9. A cikin kowane dare na Watan Ramalana ne Allah ke 'yanta bayinsa masu dumbin yawa daga cancantar zaman Wuta zuwa Aljannah.

10. Shi ne watan da yin aikin Umara a cikinsa yake daidai da Aikin Hajji da Manzon Allah k**ar yadda Annabin ya fada a Hadisi.

24/03/2023

Muna Daukacin Al-ummar Musulmi Barka Da Shigowar Wata Mai Alfarma. Muna Rokon Allah Ya Amsa Mana Ibadinmu Ameen Ya Allah.

Wannan Sako Ne Daga Hon. Minister Of Finance Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna.

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Chake Online Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Chake Online Media:

Share