27/05/2026
Ma'aikatar Raya Karkara Da Walwalar Jama'a Ta Shirya Walimar Sallah Ga Yara Da Ke Gidan Gyaran Hali Na Katsina
.... Gwamnatin Dikko Radda Ta Basu Gudummuwar Babbar Saniya Domin Shagalin Sallah
Ma'aikatar Raya Karkara Da Walwalar Jama'a ta Jihar Katsina, a karkashin jagorancin Farfesa Abdulhamid Ahmad, ta shirya walimar cin abincin Sallah ga yaran da ke gidan gyaran hali na Katsina.
Kwamishinan Ma'aikatar Farfesa Abdulhamid Ahmad, tare da Babban Sakataren Ma'aikatar da Darkatoci da sauran ma'aikata sun shaida wannan gagarumar walimar Sallah.
Da yake magantawa a yayin walimar cin abincin, Kwamishinan ya ce tun lokacin da Gwamna Radda ya hawo karagar mulki Gwamnatin shi ke shirya irin wannan walima ga yaran, domin su san cewa an kula da su.
A cewar shi, Gwamna Radda yana bayar da duk kulawar da ta kamata ga wadannan yara da ake kawowa a gidan, domin su fahimci rayuwa su zama mutane masu kyawawan halaye.
Daga nan sai ya yabawa Gwamna akan goyon baya da hadin kai da yake baiwa ma'aikatar a koda yaushe, tare da yin kira ga yaran akan su kasance masu hali na gari bayan fitar su gidan.
Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Muntari Kado Kurfi, ya magantu akan irin yadda Gwamna Radda ke nuna matukar damuwa da tabarbarewar tarbiyar yara masu tasowa.
Ya godewa Kwamishinan ma’aikatar Farfesa Abdulhamid Ahmad da gwamnatin Jihar Katsina, bisa irin jajircewa da ayyukan alkhairi da suke gudanarwa domin taimakon al’umma.
Haka kuma, ya yi nasiha ga yaran da ke gidan tare da ma’aikatan wajen tabbatar da ɗa’a, biyayya da kuma kyakkyawar mu’amala a tsakanin su.
Sauran wadanda s**a maganta a yayin taron sun hada da Daraktan Walwalar Jama'a Alhaji Jibrin Mukhtar da wasu daga cikin jami'an da ke kula da yaran.
Daga karshe an gudanar da addu'oi na musamman ga Gwamna Dikko Umaru Radda, akan Allah SWT ya kara yi mashi jagoranci a Gwamnatin shi.
Hoto: Katsina Post/Facebook