02/06/2022
Daya daga cikin hadiman shugaba Buhari ya fasa kwaii a wata zan tawada yan jarida s**aii dashii
Daya daga cikin manyan hadiman Shugaban kasa ya bayyana abinda shugaba Buhari ke boyewa, wanda ake sha'awar Jam'iyar APC ta tsaida a matsayin Dantakar Shugaban kasa, a zaben fidda Gwanin da Jam'iyar zata gudanar a makon gobe.
Da yake zantawa da Jaridar press-express, babban Hadiminnasa wanda aka sakaya sunan sa ya bayyana cewar, shugaba Buhari yafi son a tsaida Mataimakin sa watau Farfesa Yemi Osinbajo, a kaffatanin y'an takarar da ke neman Kujerar, domin yayi aiki tare dashi tun daga shekarar 2015 har ya zuwa yanzu, domin fahimci irin kwarewar sa akan harkokin shugabanci, kuma zai dora daga inda Gwamnatin Buhari zata tsaya.