12/02/2026
Tawagar Sabon Sarkin Muduru Ta Kai Ziyarar Godiya Ga Sarkin Katsina Alh. Dr. Abdulmuminu Kabir Usman tare da Gwamnan Jihar
… Sabon Sarkin Muduru, Hakimin Muduru, Alh. Abubakar Dardisu, ta kai ziyarar godiya ga Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Abdulmuminu Kabir Usman, CFR tare da Gwamnan jihar Mallam Dikko Umar Radda PhD CON.
Mai Martaba Sarkin Katsina ya karɓi tawagar a fadarsa da ke cikin Birnin Katsina a ranar 11 ga watan Fabrairu, 2026.
Kamar yadda jaridar Katsina Post ta samu, tawagar ta zo ne ƙarƙashin jagorancin Sardaunan Katsina, Ambasada Ahmad Rufa’i Abubakar, tare da manyan jami’an Hukumar NIA da sauran masu riƙe da muk**an gwamnati daga ƙaramar hukumar Mani da sauran sassan jihar Katsina da kasa baki ɗaya.
Makasudin ziyarar shi ne domin miƙa godiya ga Mai Martaba Sarkin Katsina bisa ba Alh. Abubakar Dardisu sarautar Sarkin Muduru, bayan amincewa da ƙara faɗaɗa masarautu a jihar Katsina.
Da yake jawabi, Mai Martaba Sarkin Katsina ya bayyana cewa ziyarar godiya al’ada ce ta nuna biyayya da girmamawa ga masarauta. Ya taya sabon Sarkin Muduru murna tare da yi masa fatan alheri a sabuwar sarautarsa.
Tunda farko da yake jawabin Amb. Ahmad Rufa’i Abubakar ya ce “mun zo ne domin yin godiya tare da taya murna ga ɗan’uwanmu kuma abokinmu bisa wannan sarauta da Allah Ya ba shi a wannan masarauta tamu mai albarka. Ba mu da abin cewa face ƙara godiya bisa yadda al’umma s**a halarta domin nuna farin ciki da taya murna.”
Haka zalika, da yake nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana farin cikinsa bisa yadda aka bayar da sarautar a inda ya dace. Ya ce yana da yaƙinin cewa sabon Sarkin Muduru zai riƙe sarautar yadda ya k**ata.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa shi ma yana daga cikin ahalin Muduru, inda ya yaba wa Masarautar Katsina bisa matakin da ta ɗauka na ba da sarautar ga wanda ya cancanta.
Tawagar da ta halarci ziyarar ta haɗa da Amb. Dr. Ahmad Rufa’i Abubakar (Sardaunan Katsina), Amb. E. E. Imohe, mni, Amb. E. O. Okafor, mni, Amb. Mu’azu Mohammed, mni, Amb. B. M. Rano, mni, Amb. Lawal Kazaure (Danmasanin Kazaure)
Amb. Attahiru Halliru, Engr. Bala Almu Banye (Zarma), Amb. Sani Bala (Wambai), Amb. Ilyasu Paralgada, Alhaji Umar Bafalle, Professor Michael Ogrima (Provost, College of Medical Sciences, Federal University Lokoja), Alhaji Rabiu Abubakar (Dallatu),
Dr. Farouk Aminu, Alhaji Dalhatu Isah, Benjamin Kiksenenso, Amb. Kabiru Sadauki, Alhaji Sani Kukasheka, mni, Shata, Nasir Ladan, mni, Mr. Hannafi Bamalli (Director Protocol, Makia Kano), da Mr. Adamu Kazir (Retired Controller of Customs).