TAFI KWABO TV

TAFI KWABO TV SHAFIN YA KUNSHI: LABARAI (NEWS), WAJARMA JAMAA DAKAI, SIYASA (POLITIES), SUPPORT (WASANNI), RAAYOYI, BUSINESS, ADDINI. MATUKAR BABU ZAGI KO CIN MUTUNCHI

Tafi kwabo tv

Ƙungiyar ’Yan Takarar majalisun dokokin jihar Katsina na jam'iyyar ADC sun Gudanar taro domin ganin Jam'iyyar tayi Nasar...
26/08/2026

Ƙungiyar ’Yan Takarar majalisun dokokin jihar Katsina na jam'iyyar ADC sun Gudanar taro domin ganin Jam'iyyar tayi Nasara.

A ranar Litinin 24/8/2026, Ƙungiyar ’yan takara da masu neman takara a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina s**a gudanar da wani taron wayar dakai gabanin zaɓen shekarar 2027.

Hon. Abdulrazak Kaita, shugaban ƙungiyar shi ne ya jagoranci taron, inda ya mayar da hankali ne kan ƙulla zumunci da haɗin kai tsakanin ’yan takara, shugabanni da masu ruwa da tsaki, tare da tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi jagoranci, siyasa, yaƙin neman zaɓe da dabarun kare ƙuri’u.

Taron ya samu halartar wakilin ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina na jam’iyyar ADC, tare da wasu daga cikin ’yan takarar jam’iyyar da masu neman takara na Majalisar Dokokin Jihar Katsina.

Daga cikin akwai wakilin Dan takarar Gwamna na jam'iyyar ADC Wanda ya samu wakilcin Sanata Sadik Yar'adua, Hon. Jamilu Lion, Hon. Mustapha Audu Saulawa da dai sauransu.

A yayin taron, mahalarta sun jaddada muhimmancin haɗin kai, fahimtar juna da samar da kyakkyawar hanyar sadarwa tsakanin ’yan takara domin gina ƙungiya mai ƙarfi da tsari.

An kuma tattauna dabarun gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana, wayar da kan al’umma kan manufofin jam’iyyar, da kuma hanyoyin kare ƙuri’un da magoya bayan jam’iyyar za su kada a lokacin zaɓe.

Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar, Hon. Abdulrazak Kaita, ya bayyana cewa manufar taron ita ce ƙarfafa ’yan takara da samar da tsarin haɗin kai da zai taimaka wajen gina ADC mai ƙarfi, mai tsari kuma mai mayar da hankali kan buƙatu da muradun al’ummar Jihar Katsina.

Ya yi kira ga ’yan takara da shugabannin jam’iyyar da su fifita haɗin kai, biyayya ga tsarin jam’iyya da kuma muradun al’umma, domin samun nasara a zaɓen 2027.

Taron ya kasance wani muhimmin mataki wajen ƙarfafa haɗin gwiwa da shirye-shiryen jam’iyyar ADC domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 a Jihar Katsina.

Mutane da dama s**a tofa albarkacin bakinsu daga ciki akwai Sanata Sadik Yar'adua, Hon. Surajo Aminu Makera, Hon. Mustapha Audu Saulawa da dai sauransu.

Taron wanda ya gudana a babban ɗakin taro na Farm hotel dake birnin Katsina ya samu halartar Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ADC, wasu daga cikin ƴan takara da sauran magoya baya.

ALHAMDULILLAH! 🤲🏽🇳🇬 | KARRAMAWA DA WAYAR DA KAN JAMA’A KAN SHUGABANCI NAGARIA ranar da ta gabata, Kungiyar ’Yan Takarar ...
25/08/2026

ALHAMDULILLAH! 🤲🏽🇳🇬 | KARRAMAWA DA WAYAR DA KAN JAMA’A KAN SHUGABANCI NAGARI

A ranar da ta gabata, Kungiyar ’Yan Takarar Majalisar Jaha karkashin African Democratic Congress (ADC) ta gudanar da wani muhimmin taro da ya hada da wayar da kan jama’a kan muhimmancin shugabanci nagari, gaskiya, adalci, dimokuraɗiyya da ci gaban al’umma.

Taron ya kuma kasance wata dama ta musamman wajen girmamawa da karrama jajirtattun ’yan kungiyar da s**a nuna kwazo, sadaukarwa da jajircewa wajen fafutukar samar da ingantaccen shugabanci da kare muradun al’umma.

A yayin taron, an karrama wasu daga cikin jajirtattun ’yan kungiyar da Certificate of Honour, a matsayin nuna godiya da yabo bisa gudunmawar da s**a bayar wajen wannan tafiya ta siyasa da hidimtawa al’umma.

Daga cikin wadanda s**a samu wannan karramawa akwai:

Hon. Abdulrasheed El-Kasim,
Katsina State House of Assembly Aspirant & Candidate Forum, wanda aka karrama bisa gudunmawa, jajircewa da sadaukarwa wajen gwagwarmayar neman shugabanci na gaskiya, adalci, dimokuraɗiyya da yaki da mulkin kama-karya.

Wannan karramawa ba wai takarda ce kawai ba; alama ce ta godiya, amincewa da kuma karin nauyin da ke kan wadanda aka karrama na ci gaba da yi wa al’umma hidima.

Kungiyar ta bayyana cewa, irin wadannan shirye-shirye za su ci gaba da kasancewa wata hanya ta karfafa gwiwar matasa, wayar da kan jama’a kan hakkokinsu na dimokuraɗiyya, da kuma zaburar da masu kishin al’umma wajen shiga harkokin shugabanci.

KIFI NA GANINKA YOUTH MOBILISATION AND AWARENESS KATSINA STATE.

Muna kira ga daukacin matasa da masu kishin al’umma da su kasance masu fahimtar siyasa, zaman lafiya, hadin kai da neman shugabannin da za su yi aiki domin ci gaban al’umma.

Allah Ya kara mana hikima, hakuri da jajircewa wajen ci gaba da wannan tafiya ta neman gaskiya, adalci, shugabanci nagari da ci gaba. 🤲🏽

Hon. Abdulrasheed El-Kasim
Chairman, KIFI NA GANINKA YOUTH MOBILISATION AND AWARENESS, Katsina State

“Gwagwarmaya don Gaskiya, Adalci, Dimokuraɗiyya da Shugabanci Nagari.” 🇳🇬🤝🏽

Shin kuna ganin zaku zabeshi?
21/08/2026

Shin kuna ganin zaku zabeshi?

🤔🤔🤔 ikon Allah To meye hakan yake nufi kenan
20/08/2026

🤔🤔🤔 ikon Allah To meye hakan yake nufi kenan

19/08/2026
🌍 HAPPY WORLD YOUTH DAY! 🎉A yau, muna bikin matasa—ginshikin gina al’umma da makomar ƙasa. Matasa ba wai shugabannin gob...
12/08/2026

🌍 HAPPY WORLD YOUTH DAY! 🎉

A yau, muna bikin matasa—ginshikin gina al’umma da makomar ƙasa. Matasa ba wai shugabannin gobe ba ne kawai; mu ne ƙarfin yau da kuma masu tsara makomar gobe.

Mu kasance matasa masu kishin ƙasa, ilimi, haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba. Mu yi amfani da damar da muke da ita wajen kawo sauyi mai ma’ana a cikin al’ummarmu.

“Matasa su ne ginshiƙin kyakkyawar makoma.” 💪🌍

Ina taya dukkan matasan Katsina State, Najeriya da duniya baki ɗaya murnar World Youth Day.

Together for a Stronger, United & Progressive Youth Community. 🤝

ABDULRASHEED EL-KASIM
Chairman,
KIFI NA GANINKA YOUTH MOBILISATION AND AWARENESS, KATSINA STATE

KIRA GA ’YAN SIYASA, MUSAMMAN MATASAYa kamata mu, musamman matasa, mu fahimci cewa lokaci ya yi da za mu fara gane wanda...
10/08/2026

KIRA GA ’YAN SIYASA, MUSAMMAN MATASA

Ya kamata mu, musamman matasa, mu fahimci cewa lokaci ya yi da za mu fara gane wanda yake mana ciwo da wanda yake mana magani. Ba daidai ba ne mu ci gaba da bin ɗan siyasa kawai saboda yana da suna ko mukami, alhali kullum yana amfani da rayuwarmu da makomarmu kamar kwallon kafa.

Yau sai ya ce maka: “Wannan ce jam’iyyar da za a yi.” Ya zagi wata jam’iyya da ƙarfi, ya sa ka yarda cewa ita ce hanya mafi kyau. Amma gobe sai ka ga shi kansa ya koma wannan jam’iyyar da yake zagi, ya bar maganganun da ya yi jiya kamar ba su taɓa faruwa ba.

Mu matasa mu daina bin siyasa ba tare da tunani ba. Kai matashi ne mai burin gobe, kana da damar zama jigo, shugaba, ɗan majalisa, kwamishina ko ma gwamna a nan gaba. Kada ka bari wani ɗan siyasa ya yi amfani da kai a yau, ya lalata maka damar gobe.

Lokaci ya yi da za mu duba makomarmu, ba kawai abin da za mu samu a yau ba. Mu tambayi kanmu: Me wannan siyasar za ta kawo wa rayuwata? Me za ta kawo wa al’ummata? Kuma ina nake son ganin kaina bayan shekaru 5, 10 ko 20?

Ya kamata mu, matasa, mu yi wa ’yan kasuwar siyasa bukata tawaye. Kada mu zama kayan aiki da ake amfani da su lokacin zaɓe, sannan bayan an samu nasara a manta da mu.

Siyasa ba fada ba ce, siyasa ba zagi ba ce, siyasa ba bautar mutum ba ce. Siyasa hidima ce, siyasa makoma ce, siyasa ce ta al’umma.

Saboda haka, matasa mu farka, mu yi tunani, mu tambaya, mu tantance, mu zaɓi abin da zai amfani makomarmu. Kada wani ya yi amfani da ƙarfinmu wajen gina makomarsa, alhali yana lalata tamu.

Makomarmu tana hannunmu. Lokacin canji da tunani ya yi.

Abdulrasheed Elkasim
Chairman, KIFI NA GANINKA YOUTH MOBILISATION AND AWARENESS, KATSINA STATE
Commander Tabbatar da Fale ɗaya

10/08/2026

Address

GRA
Katsina
82L77

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TAFI KWABO TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category