30/01/2023
Munyi karo da wani labari na wata mata ta yi matukar
mamaki a ranar auren danta, yayin da ta gano cewa ashe
amaryar ’yarta ce wacce ta bace tun shekara 20 baya.
Hakan ya sa mahaifiyar amaryar wacce a rashin sani ta kusa
ta zamar mata surika s**a fara zubar da hawaye, ita da
amaryar da angon, tun bayan da s**a gano cewa ita ce
’yarta wacce ta bace da dadewa kuma yanzu take auren
danta.
An dai gudanar da wannan bikin ne a garin Suzhou, da ke
lardin Jiangsu na kasar China a ranar 31 ga watan Maris.Sabuwar surikar ta gano ’yar tata ce a lokacin da ake cikin
tsakiyar biki, inda ta tabbatar da ’yarta ce ta hanyar gano irin
hannunta, kamar yadda kafar yada labarai ta Times Now
News ta ruwaito.
Ita dai wannan matar ta fuskanci wadanda suke ikirarin su
ne iyayen amaryar, sannan ta tambaye su ko su ne masu
rainon amaryar, sai ’yan uwan amaryar s**a yi mamakin
tambayar da mahaifiyar ke yi masu, duk da yake labari ne
mai tsawo.
Daga nan sai s**a fara bayyana abin da ya faru da amaryar
tun tana jaririya kamar haka: “Wadanda s**a raini amaryar
sun ce, sun tsinci jaririya a gefan hanya, sai s**a dauke ta
suna rainonta har ta girma. Kuma sun raine ta kamar ’yar da
s**a haifa.”
Ita dai wannan batacciyar yarinya ta bayyana yadda ta yi
murnar haduwarta da mahaifiyarta fiye da murnar ranar
bikinta.
Bayan ta gano abin da ya faru, sai ta nuna damuwarta game
da auren, duk da yake shi ma angon dan riqo ne, inda ta
karkata ga dan uwan nata.
Angon ya bayyana aniyarsa na auren matarsa kuma ya ce,
ba wani dalili na sauya kudirinsa.
A bangaren mahaifiyar, ta ce ba wata matsala a auren tun
da ba ’yan uwa ba ne na jini domin kuwa shi ma angon dan
riko ne da aka dauko tun yana karami.
kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga
abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku
ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa
dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng
dakunkayi