HT Africa

Anga watan ramadan a kasar saudiya a yau 28 Fabairun 2025
28/02/2025

Anga watan ramadan a kasar saudiya a yau 28 Fabairun 2025

Yanzu yanzu: Kotu Ta Bayar Da Belin Farfesa Yusuf Usman....Kotu ta 44 dake birnin tarayyar Najeriya Abuja ta bayar da be...
27/02/2025

Yanzu yanzu: Kotu Ta Bayar Da Belin Farfesa Yusuf Usman....

Kotu ta 44 dake birnin tarayyar Najeriya Abuja ta bayar da belin Farfesa Usman Yusuf bayan kimanin kwanaki Ashirin da Hudu 24 a hannun jami‘an tsaro bisa zargen-zargen aikata ba daidai ba a hukumar Inshorar lafiya ta ƙasa wanda hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ke masa.

Ladan Salihu yace ƙa'idar da aka bada wajen bada shi zasu iya cika ta cikin awa Guda.

Muhammad Aminu Kabir

Yanzu Yanzu: Wani Bawan Allah Ya Aiko Mani Da Wannan Bayanin Akan Brigadier Janaral Ahmed Muhammad Daku...Assalamu Alaik...
08/02/2025

Yanzu Yanzu: Wani Bawan Allah Ya Aiko Mani Da Wannan Bayanin Akan Brigadier Janaral Ahmed Muhammad Daku...

Assalamu Alaikum Barka da Asuba, naga rubutun da akayi a media kan Ahmad Daku, Ba gaskiya bane don shi bai ma ɗauka ba, b***e ya maida.

Ni nayi aiki da tsohuwar Matar shi da ya zauna Kano da Sokoto da ita, munyi firarshi sosai.

Wata rana tace zata zo Katsina kuma Personal Car ɗin shi bata iya zuwa, sai dai aka kai ta da Motar haya daga Sokoto zuwa Katsina.

Basu da wata motar gida banda Personal car ɗin shi, idan ya tashi Office baa ƙara hawan motar office sai lokacin aiki.

Ko lokacin aiki ba a Personal buƙatar wani ko ta gidan shi.

Tace min wata rana Mamarshi taje Kano yana Gwamna aka ɗauke ta da Motar Office, ya kori driver motar, yayi ta istigifari akan wannan kawai, tace k**ar ma har azumi yayi na neman yafiyar Allah akan wannan, Abin nashi kam yana da yawa.

Kazalika naga Malam Ibrahim Sheme shima ya musanta wannan zargin a shafin shi harma ya bada labarin haɗuwar su a ƙasar Israel yayin da yaje rakiyar Alhazai kiristoci.

Muhammad Aminu Kabir

Ina kira ga Gwamnonin Arewa su guji yin Sasanci da Ɓarayin Daji" --Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha...
08/02/2025

Ina kira ga Gwamnonin Arewa su guji yin Sasanci da Ɓarayin Daji" --Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha Inuwa.

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha Inuwa wanda ya kasance jigo a Jam'iyyar Adawa ta PDP a Jihar Katsina, ya yi kira ga Gwamnatocin arewa da su guji yin sulhu da ƴan ta'addan daji a cewar sa, hakan wata hanyar yaudara ce da ƴan ta'addan ke amfani da ita a duk shekara.

Kamar yadda ya bayyana, a duk shekara ƴan ta'addan na ɓullowa da yaudarar neman Sasanci da Gwamnati, sak**akon irin halin matsi da suke shiga a rayuwar Daji, saboda rashin abinci da kuma tsirrai a matsugunnan da suke ɓoye.

A cewar barayin dajin suna neman sulhu ne domin su samu damar shigowa cikin gari cin kasuwanni da kiwata dabbobinsu.

Katsina Reporters

Matafiya Sun Koka Yadda Suke Shan Wuya A Tall Gate Na Hanyar Keffi Zuwa Akwanga Jihar Nasarawa.....A ƴan kwanakin nan gw...
08/02/2025

Matafiya Sun Koka Yadda Suke Shan Wuya A Tall Gate Na Hanyar Keffi Zuwa Akwanga Jihar Nasarawa.....

A ƴan kwanakin nan gwamnatin tarayya ta kaddamar da fara biyan kuɗin hanya ko harajin amfani da hanya tsakanin mashigar gari da gari wato Tall Gate an kuma fara da Titin da ya tashi daga Keffi zuwa Akwanga ne cikin jihar Nasarawa wanda shima ba da jimawa ba aka kammala aikin shi.

Sai dai matafiya sun koka sosai yadda rashin sadarwa ya sanya suke zaman jira cikin chunkoson ababen hawa ganin cewa ance baa bukatar kuɗi a hannu komi ana son ayi shine ta hanyar yanar gizo.

Wannan lamarin ya fusata matafiya da dama yadda aka tsare su ba gaba ba baya saboda rashin sadarwa, wanda a ƙarshe ma dai a yau juma'a sai da jami'an kula da haɗurra s**a je wurin domin bada Gudummuwar su aka samu Mutane s**a wuce saboda chunkoson ababen hawa.

Motocin daga Abuja-Keffi-Akwanga-Makurdi dake bin wannan hanyar zasu biya haraji k**ar haka.

• Saloon Cars – N500,
• SUVs/Jeeps – N800,
• Minibuses – N1,000, and
• Multi-Axle Vehicles – N1,600.

Akwai kuma wasu da aka ware na Jami'an tsaro da na gwamnati da ba zasu biya wannan harajin ba.

Muhammad Aminu Kabir

ALHERIN ALLAH YA KAI WA SHEIKH ISA ALI PANTAMIGame da kadiyyar gidan marigayi Sheikh Albaniy Zaria da tuhumar da ake yiw...
06/02/2025

ALHERIN ALLAH YA KAI WA SHEIKH ISA ALI PANTAMI

Game da kadiyyar gidan marigayi Sheikh Albaniy Zaria da tuhumar da ake yiwa wasu Dalibansa na cin amana da watsi da matsalar 'ya'yansa, Saboda ya tabbatar da an yiwa kowani bangare adalci, a yau Alhamis Sheikh Professor Isa Ali Pantami yayi tattaki har garin Zaria ya tattauna da kowani bangare na Daliban Malam Albaniy da 'ya'yansa

Malam Isa Ali Pantami ya nemi ayi zaman a gidan Marigayi Sheikh Albaniy Zaria ko Darul Hadith tare da Mahaifiyarsu Abdulrahman, wato Matar Malam na farko, sai tace ba halin taje gidan ko makarantar domin masu jagorancin Darul Hadith sun kai karanta Kotu s**a nemi a haramta mata zuwa gidan 'ya'yanta, shine tace ba zata karya dokan Kotu ba a matsayinta na Uwa, to sai Malam Isa Ali Pantami yace aje gidanta gaba daya ayi zaman sulhun, kuma haka akayi

A zaman sulhun, Malam Isa Ali Pantami ya jaddada wa masu jagorancin Darul Hadith cewa dole su zauna da dukkan daliban Malam Albaniy da s**a kora daga Darul Jadith ayi sulhu a samu mafita, idan ba haka ba Malam yace da kansa zai jagoranci gurfanar dasu a Kotu har zuwa Supreme Court zai dauki nauyin shari'ah

Sannan Malam Isa Ali Pantami ya tabbatar da case din Aisha 'yar Malam Albaniy wacce aka damfareta kudi Kimanin Naira Miliyan 10, ta biya Miliyan 5 ya rage saura Miliyan 5, mun nema mata taimako ta account dinta na Stanbic IBTC, kuma jama'a kun hada mata kudi kimanin Naira Miliyan 2 da dubu dari uku da wani abu k**ar yadda zaku gani a hoto

To nan take Malam Isa Ali Pantami a gurin da ya jagoranci zama dasu ya sa PA dinsa ya tura wa Aisha sauran kudi Naira Miliyan 3 da dubu dari uku ta account dinta na First Bank k**ar yadda zaku gani a hoto

Yanzu Aisha ta samu duk kudin da zata biya mutane hakkinsu, harma da wasu kudade da s**a rage, hakan na nufin jama'ar da s**a tura taimako wa Aisha da Malam Isa Ali Pantami kun zama sanadi na fitar da Aisha marainiya daga cikin tashin hankali da fuskantar wulakanci da zaman gidan yari, Allah ne kadai Ya san irin farin cikin da na shiga Wallahi

A daren yau Aisha zata tura wa duk mutanen da suke binta kudi hakkinsu, kuma zata fitar da receipt na evidence of payment, zamuyi posting domin ku gani Insha Allah

Zan iya cewa tunda nake a rayuwana Malam Isa Ali Pantami bai taba burgeni k**ar yau ba, ba ka gane waye asalin masoyinka sai ranar da ka shiga cikin jarrabawa, Malam ya tabbatar wa duniya cewa shi cikakken adali ne masoyin Malam Albaniy Zaria, ba k**ar sauran Malamai da suke tare da bangaren wadancan maciya amana ba, inda s**ayi ta magana ba tare da sun zauna da kowani bangare ba

Da wadanda s**a zagemu s**a zagi Aisha s**a mata kazafi duka mun yafe wa kowa, mu wannan hanyar dama mun saba binta, muna ganin nasara a kowani yanayi, abin bukata kawai shine mutum yayi saboda Allah

Allah Ya saka wa kowa da gidan Aljannah

Datti Assalafy

Ƴan Ta'adar Daji Sun Kai Hari Tsiga Sun Kuma Yi Awon Gaba Da Dattijo Rtd Brig. General Maharazu Ismail Tsiga...Bisa ga b...
06/02/2025

Ƴan Ta'adar Daji Sun Kai Hari Tsiga Sun Kuma Yi Awon Gaba Da Dattijo Rtd Brig. General Maharazu Ismail Tsiga...

Bisa ga bayanan da s**a fito bayan mummunan harin ƴan bindiga da s**a kai garin tsiga daren jiya laraba 5th, February 2025 a garin tsiga ta ƙaramar Hukumar Bakori.

Barayin sunyi nasarar garkuwa da mutane biyu daga ciki akwai matashi daya da Dattijo Rtd Brig. General Maharazu Ismail Tsiga tsohon Director General na NYSC.

Muhammad Aminu Kabir

06/02/2025

🚨 | Yadda Ake Dillancin Kananan Mata

A ‘yan kwanakin nan, ina samun kalubale sosai daga mabarnata, wanda irin wannan exposé ɗin yake batawa kasuwa. A yau ma, zan sake kawo muku wasu wurare da bincike ya nuna ana dillanci da kuma farautar mata, musamman kananan ‘yan mata waɗanda ba su gama sanin rayuwa ba. Na yi wannan rubutu ne don na farkar da iyaye da kuma waɗanda amanar ‘ya’ya take hannunsu, don su san abin da yake faruwa kuma su kiyaye.

ℹ️ Disclaimer : Kafin na shiga wannan bayani, ina so mai karatu ya sani—kar don ka ji na ambaci wani guri ka ɗauka na yi ne don targeting wasu ko wata sana’a. Har wa yau, akwai mutanen kirki kuma masu k**antawa.

Gabatarwa.

A yau, mun wayi gari an samu wasu batagarin da aikinsu shine saka matasan ‘yan mata a cikin harkoki na banza, irin su lesbianism da kuma karuwancin gaban iyaye. Yarinya tana gaban iyayenta amma karuwanci take. Ku biyo ni a hankali don jin yadda irin waɗannan abubuwan suke kasancewa.

1. Masu Daukar Hoto

Yanzu abin da wasu batagari daga cikin masu daukar hoto suke yi shine kai ziyara duk wani wuri da ake biki ko tarukan mata, especially event centres. Kuma suna zuwa ko ka gayyace su ko ba ka gayyace su ba. Da zarar sun shigo, sai su fara farautar mata ƙanana marasa yawo. Daga nan sai su ɗauke su hoto kyauta, sai su karɓi lambar waya da sunan idan hoto ya zama ready za a tura musu.

Bayan an tashi biki, shi mai photo yana da shafi a Instagram. Sai ya je ya saka waɗannan hotuna don kawalai da ‘yan iska su gani. Idan mutum ya ga yarinyar da ta masa, sai ya kirata a waya ya ce tazo karɓar hoto. Idan ta zo, sai ya ba ta hoton sannan ya kawo kuɗi masu kauri ya bata, ya ce gashi, wani ya ganki yana son ki. Wasu ma har iPhone ake ba su, a ce gift daga wani unknown admirer. To shikenan, daga nan sai a ce tazo wuri kaza, daga nan magana ta kare—sai wanda Allah ya so da rahama. Irin wannan ta faru bila’adadin. Shi mai hoto ya gama aikinsa, sai a biya shi kudin hada wannan harka.

2. Gidan Makeup/Gyaran Jiki da Ire-Irensu

Suma masu gidajen makeup da gyaran jiki suna da k**anceceniya da masu gidajen hoto. Domin bayan sun yi wa mace makeup, suna da iPhone mai camera mai kyau. Sai su ɗauki hotunanki, sai a ajiye. Su kuma mata, dama ba su da wayo wasu daga cikinsu—ganin an ce za a saka ta a Instagram, sai ta fara murna. To, itama daga nan za a fara tura hotonta group-group na kawalai. Idan ta yi, sai a kirata a mata introducing wani, daga nan shikenan.

Sannan bayan haka, ‘yan le****ns sun mayar da gidan makeup k**ar wani transit station. Domin idan an zo, za a yi ta zantuttuka na ƙarya, ana nuna kuɗi, ana maganar kuɗi don yarinyar ta ji ta yi sha’awa. Daga nan sai ta riƙa ganin to su gasu suna fantamawa, itama sai ta yi sha’awa, daga nan ake recruiting ɗinta. Kafin ka ce kwabo, an kaita. Shi yasa ƙannen mu da yawa muka ƙi bari su yi training ɗin Makeup Artist, saboda gudun faɗawa. Don Allah, maza waɗanda matansu suke makeup, ku zauna da su ku tambaye su—wallahi labaran da za ku sha ba su da adadi.

Wata majiya ta tabbatar min da cewa har sawa suke a rika bi gida gida ana kawo janyo musu yara. Misali, yarinya zata rika zuwa neighbours dinsu gidan wata kawa haka. Sai ta rika mata hirar samun kudi. Da kuma kayata mata wasu abubuwa na morewar rayuwa. Ko kuma ta fadi wani abu da zai sa ayi wata fita ta musamman don kawai aje gidan wannan kawaliya. Mai bada wannan labarin tace, kawar tata zuwa tayi har gida tace mata suje wata unguwa. Da shigarsu gida sai taji k**ar dama an san za'a kawo ta. Sai ga wasu yan bariki nan sun shigo. Akai ta wasu hirarraki na banza a karshe da s**a tashi tafiya sai s**a basu 50k. Ita waccen yarinya sai aka ce ta dauki 20k sai ta barwa yarinyar 30k tunda itace bakuwa a cikinsu. Tace daga nan bata kara kula waccen ba. Domin clearly bata ta take so ayi. So, haka suke recruiting yan mata har cikin gidan iyayensu.

3. Hostels Din Jami’o’i

Hostel sai dai Innalillahi! Yanzu haka, duk inda ka san akwai wani hostel a ƙasar nan, to abubuwan da suke faruwa a wurin sai addu’a. Idan aka ce weekend ya zo, haka za a riƙa turo motoci daga wasu jahohin irinsu Abuja, Kano, Kaduna, wasu kuma kuɗin ticket ɗin jirgi ake turawa. A riƙa dibar ‘ya’yan mutane, ana kaisu Abuja, ana kwana da su.

Ranar Monday da sassafe, yarinya ta biyo jirgin farko, ta dawo school k**ar bai faru ba. Shi yasa idan ka je security offices na jami’o’i, ka yi hira da su, sai ka ji k**ar abin ba da gaske ba. Abortion cases babu adadi. Kuma ba wanda zai iya hana wannan.

Kawai mafita shine yarinya ta zauna a gidan ubanta, ta yi karatun nan. Idan kuma ba ka da gida a garin, ka nemi wani naka, ta zauna a gurinsa. Kuma idan kuna ganin k**ar ba gaskiya bane, idan ka san wata mai zama a hostel, ka tambayeta labarin abin da yake faruwa a hostels, za ka sha mamaki.

Akwai case na wata yarinya da ta rasu. Ita mazauniyar wani hostel ne a daya daga cikin jamioin kasarnan. Kuma irinta suna sa yawa. Cewa iyayenta yayi zasu tafi SIWES. Ashe wani Alhaji ne yake so su tafi Dubai shakatawa. Haka kuwa akai - s**a tafi wajen watanta biyu a hotel room a Dubai. Ciwon ajali ya same ta kafin azo gida ta rasu. Kuma da mutum ya rasu case ya zama babba. A karshe dai iyayenta sun cika da mamaki yadda wadda take zaune a Hostel tana SIWES amma gata a Dubai ta mutu.

📍 Sannan iyaye ku rika kaiwa yayanku ziyarar bazata domin muna da labarin cewa mata da yawa da suke cewa suna zaune a Hostel ba a hostel din suke ba. Zuwa suke su k**a dakuna a wajen makaranta tare sa samari su rika kwana tare. Komai tare. Wasunsu sunyi ciki yafi a kirga. Daga 100 level har final year. Idan ya gaji da ita kuma sai ta sake sabon saurayi shima ya karbi nasa rabon. Haka suke wa kawunansu.

Jama’a, sai mun ƙara dagewa da addu’a da kuma saka ido. Muna cikin musiba. Allah ya kare zuriyar mu daga wannan fitintinu.

---
Muhammad Ubale Kiru
Copyright Reserved ©

Shugaban Kasar Nijeriya Bola Ahmad Tinumbu Ya Kara Kudin Kasafin Nijeriya Daga Tiriliyan 49.7 Zuwa Tiriliyan 54.2
05/02/2025

Shugaban Kasar Nijeriya Bola Ahmad Tinumbu Ya Kara Kudin Kasafin Nijeriya Daga Tiriliyan 49.7 Zuwa Tiriliyan 54.2

Ba Gudu Ba Ja Da Baya, 'Yanci Yana Samuwa Ne Sak**akon GwagwarmayaCewar Dan Gwagwarmaya Barista Selemon Dalung, A Yau 5 ...
05/02/2025

Ba Gudu Ba Ja Da Baya, 'Yanci Yana Samuwa Ne Sak**akon Gwagwarmaya

Cewar Dan Gwagwarmaya Barista Selemon Dalung, A Yau 5 Fabarerun 2025, Bayan Kai Ziyara Gidan Gyaran Hali Na Kuje Dake A Cikin Kwaryar Garin Abuja, Ziyarar Tasu Kacokam Akan Farfesa Usman Yusuf Da EFCC Ta Kai Kotu Ajiya A Bisa Tuhumar Karkatar Da Kudi Ba Akan Ka'ida Ba Har Kimanin Naira Miliyan Casa'in 90,

Barista Salemon Dalung, Yace Sun Same Shi Cikin Koshin Lafiya Da Yanayi Mai Kyau.

Majalisar zartarwa a Nijeriya FEC ta amince da kashe naira tiriliyan 1.334 don fara aikin babbar hanyar Calabar,Akwa Ibo...
05/02/2025

Majalisar zartarwa a Nijeriya FEC ta amince da kashe naira tiriliyan 1.334 don fara aikin babbar hanyar Calabar,Akwa Ibom zuwa Legas

DCL HAUSA

Shugaban Kasar Amurka, Donal Trump Ya Lashi Takobin Mayar Da Gaza A Karkashin Yankin Amurka,Daga Bangare Guda Kuma Kasar...
05/02/2025

Shugaban Kasar Amurka, Donal Trump Ya Lashi Takobin Mayar Da Gaza A Karkashin Yankin Amurka,

Daga Bangare Guda Kuma Kasar Saudiya Ta Nuna Kin Amimcewarta Akan Wanan Kudirin Na Shugaba Donal Trump

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HT Africa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HT Africa:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share