15/10/2025
Faɗin cewa Salatul Fatih tafi Al-Qur’an daraja, magana ce da babu wani Musulmi da zai faɗa. Salatul Fatih ma ba ta kai harafi guda daga cikin Al-Qur’an ba.
Amma abin da ake kwatanta shi a nan shi ne: Lada ko sakamakon wanda yake karatun Al-Qur’an amma baya kiyaye ladubansa, baya aiki da hukuncinsa, baya tafiya bisa shiryarwarsa, yana zaluntar kansa, da kuma lada na wanda yake yawaita salati ga Annabi ﷺ a kowace irin siga. Ga irin wannan mutum, wannan aiki wato (yin salati ga Annabi ﷺ) yafi karatun Al-Qur’ān wanda baya aiki da shi. Kamar yadda Ibn Mas‘ud ya ce: Yaya masu karatun Al-Qur’ān da yawa, amma Al-Qur’ān yana la’antar su.
Saboda haka, duk wanda yake son danganta wani magana da mutanen hanyar Tijaniyya, ya tabbatar da bincike sosai. Ba a taɓa cewa Shaykh, Allah ya yarda da shi, ya kwatanta Salatul Fātiḥ da Al-Qur’ān kai tsaye ba. Abin da ya kwatanta kawai shi ne lada tsakanin wanda yake karatun Al-Qur’ān ba tare da aiki da shi ba, da kuma wanda yake yin salati ga Annabi ﷺ yana aiki da abin da Al-Qur’ān ya koyar.
Don haka ka koma ga wannan fahimta, ka yi tunani a kai, ya Ɗan’uwa. Amma maganar cewa Salatul Fātiḥ tafi Al-Qur’ān, ko cewa tana cikin Al-Qur’ān, duk waɗannan magana ce ta ƙarya.”
— Sheikh Sharif Ibrahim Saleh.
“Kashf al-Ghumūt wa Iẓālat al-Ilbās”
~Ibrahim Khaleel Sinikom ✍️
__________________________________
Wannan Kenan. Allah Ya Sa Mu Dace 🤲
Allah Ya Ƙara Mana Son Annabi ﷺ 🤲🥰