06/07/2025
TSAYAR DA RIGISTA SIM, SWAP, KO SIM UPGRADE DA TSARIN ESIM A NAJERIYA.
1. Umarnin Hukumar NCC
A ranar 29 ga Yuni 2025 (kusan kwanaki kadan da s**a gabata), Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta bayar da umarni ga duka kamfanonin sadarwa (MTN, Airtel, Glo, 9mobile da sauransu) su dakatar da duk wani sabon rijistar SIM, swap, da upgrade.
NIMC Bata Bada Approval na BVN/NIN Verification:
NIMC ta dakatar da wasu ayyuka da s**a shafi bawa mutane damar verifying NIN ko BVN ta hanyar agent ko wasu third-party apps (musamman wadanda MTN da GLO ke amfani da su).
Ba za a iya siyan sabon SIM ba.
Ba za a iya yin swap (canjin SIM idan ta lalace ko aka rasa) ba.
Ba za a iya yin upgrade (misali canzawa zuwa eSIM ko 4G/5G) ba.
2. Ana cewa an gano matsaloli masu alaka da tsaro da bayanai, musamman game da aikin NIN-SIM linkage (wato hada NIN da layi).
An kuma gano wasu kurakurai da rashin daidaito a tsarin rajista da sarrafa bayanan jama'a.
Wannan mataki yana cikin kokarin gwamnati na tabbatar da cewa duk bayanan da ake amfani da su sun dace kuma sun tabbata, domin hana amfani da layuka wajen aikata laifukan yanar gizo, zamba da sauran laifukan tsaro.
3. Ba a bayyana ranar dawo da aikin ba tukuna, amma hukumar NCC ta ce suna aiki tare da kamfanonin sadarwa domin gyara tsarin kafin su bude rijista da sauran ayyukan da aka dakatar.