Arewa Media News

  • Home
  • Arewa Media News

Arewa Media News Labaran kasarmu Najeriya danake kasashen ketare

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano da ga rushe gine-gine a kan titin BUKWata babbar kotu ta hana gwamnatin jihar Kano ci ...
15/07/2023

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano da ga rushe gine-gine a kan titin BUK

Wata babbar kotu ta hana gwamnatin jihar Kano ci gaba da rushe gidajen da ke kan titin BUK a karamar hukumar Gwale ta jihar.

Kotun ta bada umarnin ne ta gaggawa bayan ƙorafin da aka shigar mai kwanan wata 4 ga watan Yuli, wanda Ibrahim Adamu, Lauyan masu kara a madadin Bashir Abdullahi da wasu 19 su ka gabatar.

Wadanda ake karar sun hada da Gwamna Abba Kabir Yusuf da babban lauyan gwamnati da kuma hukumar kasa da safiyo da ta tsarawa da raya birane ta Kano.

Mai shari’a Hafsat Yahaya Sani, ta bayar da umarnin na wucin-gadi na hana wadanda ake karar su ds kansu, ko wakilai ko ma’aikata shiga filin har sai an saurari karar da kuma yanke hukuncin a kan ƙorafin.

Misis Yahaya Sani ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 26 ga Oktoba.

Babban matsala ga Emefiele yayin da gwamnatin Tinubu ke tuhumar sa da laifin mallakar makami ba bisa dokaba.Gwamnatin Ta...
15/07/2023

Babban matsala ga Emefiele yayin da gwamnatin Tinubu ke tuhumar sa da laifin mallakar makami ba bisa dokaba.

Gwamnatin Tarayya a karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shigar da kara a cikin kasashe biyu na mallakar bindigogi da makami a kan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar ( CBN ) Gwamna, Godwin Emefiele, a gaban Babban Kotun Tarayya a Legas.

A cewar rahotannin talabijin na Channels a ranar Asabar, 15 ga Yuli, 2023, Gwamnatin Tarayya ta zargi Emefiele da mallakar bindiga mai shinge guda daya ( JOJEFF MAGNUM 8371 ) ba tare da lasisi ba. Gwamnati ta tabbatar da cewa laifin ya sabawa Sashe na 4 na Dokar bindigogi, Dokokin Cap F28 na Federationungiyar 2004, kuma ana iya yanke hukunci a ƙarƙashin Sashe na 27 ( 1b ) na wannan Dokar. A cikin ƙidaya na biyu, An zargi gwamnan CBN da ya dakatar da mallakarsa a cikin jerin gwanon 123 na ammonium ( Cartridges ) ba tare da lasisi ba, wanda ya sabawa Sashe na 8 na Dokar bindigogi Cap F28 Dokokin Tarayya 2004 kuma ana iya yanke hukunci a ƙarƙashin Sashe na 27 ( 1 ) ( b ) ( il ) na wannan Dokar.

YAKU AL UMAR KARAMAR HUKUMAR KAFUR, MUFITO KWANMU DA KWAR KWATARMU DOMIN NUNA GOYAN BAYA GA DAN TAKARAR MAJALISSAR DOKOK...
07/03/2023

YAKU AL UMAR KARAMAR HUKUMAR KAFUR, MUFITO KWANMU DA KWAR KWATARMU DOMIN NUNA GOYAN BAYA GA DAN TAKARAR MAJALISSAR DOKOKI TA JIHA, WATO HON. SHUAIBU WAKILI KUFAN TAMBO AKAR KASHIN JAM IYA MAI ALAMAR TSIN TSIYA WATO APC. KODA NAKA KASO NAKWARAI.
IDAN ALLAH YAKAIMU ARANAR 11-03-2023. MUYI APC SAK. ALLAH YA DATAR DAMU DA ALKHAIRI AMIN.

DG MEDIA MAI SHINKAFA AWARENESS FORUM 2023

Da dumi, dumi Dr. Mustapha Muhammad Inuwa tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Katsina yabar jam'iyyar Apc tare da dubban Ma...
16/10/2022

Da dumi, dumi Dr. Mustapha Muhammad Inuwa tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Katsina yabar jam'iyyar Apc tare da dubban Magoya bayansa, ya koma Jam'iyyar PDP.

DA DUMI-DUMINSA: Gwamnatin Najeriya Ta Umarci Shugabannin Jami’o'i Da Su Bude Jami’o’i, Dalibai Su Koma KaratuDaga Comr ...
26/09/2022

DA DUMI-DUMINSA: Gwamnatin Najeriya Ta Umarci Shugabannin Jami’o'i Da Su Bude Jami’o’i, Dalibai Su Koma Karatu

Daga Comr Abba Sani Pantami

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da jami'o'i (NUC) ta umarci shugabannin jami'a da su gaggauta bude makarantu kana dalibai su koma karatu.

Wannan na fitowa ne daga wata wasikar da ke dauke da sa hannun daraktan kudi na NUC, Sam Onazi a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed.

Jairdar Punch ta ce ta samu wasikar ne kai tsaye daga hukumar, inda aka umarci shuganannin jami'o'i da masu gudanar dasu da su koma bakin aiki.

Mudai ba muda abun cewa kawai namu ido da kuma bin umurni, amma dai bani tunanin hakan zai kawo karshen rikicin ASUU da gwamnatin Tarayya.

Tarihi Ya nuna yadda Sarauniya Aminan Zazzau taci Kano da yaki cikin ta da waje Jim kaɗan bayan Sarauniya AminanZazzau t...
29/08/2022

Tarihi Ya nuna yadda Sarauniya Aminan Zazzau taci Kano da yaki cikin ta da waje

Jim kaɗan bayan Sarauniya Aminan
Zazzau ta ci kano da yaƙi, sai tace ta yafe wa mata, duk matan garin su fita ta wannan ƙofa, ai kafin ƙiftawa da bismillah sai Kanawa s**a yi ta shigar mata suna bin su, s**a fita ta wannan ƙofa Suna sulalewa a Sulale.

Har sarkin Kano na wancen lokacin ance ta nan kofar ya Sulalo da shigar mata kafin sarauniyar ta yafe masa ya dawo kan mulkinsa, tun daga lokacin ake kiran wannan kofar da KOFAR MATA.

Ance wannan shine dalilin da ya sa matan zariya basu cika auren Kanawaba, sun ce a Kano wai babu Maza.
😂😂😂
Note:Dan Katsina ne ni ba dan Zaria bah Gskyc Kawae tazo dole nafada 🙏🙏🙏

"Ni mai arziki ne domin ba gidan matsiyata na tashi ba, don haka babu abin da zanyi da kuɗin Jihar Katsina nazo ne domin...
23/08/2022

"Ni mai arziki ne domin ba gidan matsiyata na tashi ba, don haka babu abin da zanyi da kuɗin Jihar Katsina nazo ne domin na taimaku ku Al'ummar Jihar"~ Inji Ɗan takarar Gwamna Yakubu Lado yayin da yake zantawa da manema labarai a katsina.

YANZU-YANZU: Ban zama mataimakin Tinubu ba don k@re martaban musulunci da Musulmai, sarkin musulmi shike da hakkin kare ...
22/07/2022

YANZU-YANZU: Ban zama mataimakin Tinubu ba don k@re martaban musulunci da Musulmai, sarkin musulmi shike da hakkin kare martaban musulunci da Musulmai,

Babban Burina shine yin aiki domen kare mutunci Najeriya da yan Najeriya baki daya, ba tare da nuna bambancin addinanci ba, Cewar Kashim Shattima, a hirar a ayi da shi da wakilin Channels TV

YANZU-YANZU: An Kara Farashin Litan Man Fetur A Fadin Najeriya Gaba DayaA jihohin Arewa maso yamma ana sa ran yanzu za a...
19/07/2022

YANZU-YANZU: An Kara Farashin Litan Man Fetur A Fadin Najeriya Gaba Daya

A jihohin Arewa maso yamma ana sa ran yanzu za a rika sayar da litar fetur kan kudi Naira 184, Naira 189 a yankin arewa maso gabas.

Jaridar Daily Trust wacce ta ce ta samu tabbacin karin a Talatar nan, ta ce za a rika sayar da litar fetur a Naira 169 a Lagos, Naira 174 kuma a Abuja.

07/07/2022

GADAR DA MAIGIRMA GWAMNAN JAHAR KATSINA YAKE GINAWA KENAN A KATSINA KOFAR KAURA...

Wani matashi ya Mika takardar korafi ga Gwannatin jihar katsina, kan zargin TSB da saida offer tare da wasu korafe-koraf...
27/06/2022

Wani matashi ya Mika takardar korafi ga Gwannatin jihar katsina, kan zargin TSB da saida offer tare da wasu korafe-korafe.

A ranar 14june2021 Wani matashi ya gabatar da takardar korafe-korafen Saba ka,ida da rashin bin dokar daukar aiki na malaman sakondire ga Gwannatin jihar katsina. Matashin mai suna shamsuddeen Lawal karbaba, Dandume, ya sha wallafa zarge-zarge ga hukumar daukar malaman sakondiri TSB, akan rashin yin daidai da kuma sabawa tare da karya dokokin daukar maaikata na kasa da kuma na jihar katsina.

Acikin takardar korafin wadda ya mika a ofishin Gwamnan na katsina, Shamsuddeen karbaba, ya roki Gwannatin jihar katsina da ta dubi korafin su da idon rahama, wajen ceto katsinawa daga kama-karya, da zargin saida takardar daukar aiki(offer), tare da nuna fifiko ga yan uwa da abokai, wajen daukar aiki.

Matashi ya nuna cewa, ansan Gwannatin jihar katsina da bada mahimmanci ga harkar ilimi, tare da bin dokokin da tsari wajen ayyukan ci gaban al,umma, amma seda kash, hukumar TSB tana San ta zubar ma katsinawa kima a idon yan Nijeriya. Sannan tana so ta zubar da mutuncin Gwannatin jihar katsina, duk da kokarin Gwannatin wajen kawo tsare-tsare masu amfani da cigaban katsinawa.

Acikin takardar korafin, shamsuddeen karbaba, ya kara da cewa, ya kai kusan shekara Goma yana koyarwa ta wucin gadi(casual teaching staff), Abin mamaki wasu daga daliban da ya koyar a sakondiri, har sun samu aikin koyar wa mai cikakken albashi (permanent and pensionable), amma su haryanzu suna casual, tare da cewa ya kammala NCE Kimanin shekara goma, kana ya kammala digiri kimanin shekara biyar. Dalili kuwa shine, kamar yadda yayi zargi, yawancin mutane a yanzu basa samun aiki da TSB hakanan ta hanyar interview, saidai a saida masu da takardar daukar aiki, ko kuma suna da uwa a gindin Murhu.

kazalika, matashin ya roki Gwannatin jihar katsina, da ta kafa kwamiti na kwararru, da zasu binciki lamarin, tare da yin garanbawul ga huku

YANZU YANZU: Yan takarar Gwamnan Jihar Sokoto Akar kashin Jam iyar APC sunkoma Jam iyar PDPHakan Yabiyo bayan Faduwa Zab...
26/06/2022

YANZU YANZU:

Yan takarar Gwamnan Jihar Sokoto Akar kashin Jam iyar APC sunkoma Jam iyar PDP

Hakan Yabiyo bayan Faduwa Zaben Fidda Gwani wanda Jam iyar ta gudanar Acikin watan dayawuce

MAJIGIRI SAI TSAYA TAKARAR DAN MAJALISSAR TARAYYA MASHI DA DUTSIAkwai yiyuwar Alhaji Salisu Yusufu Majigiri shugaban jam...
25/06/2022

MAJIGIRI SAI TSAYA TAKARAR DAN MAJALISSAR TARAYYA MASHI DA DUTSI

Akwai yiyuwar Alhaji Salisu Yusufu Majigiri shugaban jam iyyar PDP a yanzu kuma Wanda ya sha kaye a zaben fitar da Dan takarar gwamna a PDP, ya koma yayi takarar Dan majalisar tarayya a kananan hukumomin Mashi da Dutsi.
Majiyarmu a cikin jam iyyar PDP ta tabbatar mana yanzu haka tattaunawa tayi nisa akan hakan.
A tsarin Wanda yaci zaben takarar a PDP Alhaji sule Yusuf shabeji daga karamar hukumar Dutsi zai janye ya rubuta ma hukumar jam iyyar sa da hukumar zabe.su kuma jam iyyar zasu maye sunan sa da majigiri.
Wata majiya ta tabbatar mana har anyi hakan a satin da muke ciki.majiyarmu tace tsakanin talata zuwa Alhamis hedkwatar jam iyyar PDP ta kasa ta aika ma suna INEC da sunan Majigiri a matsayin chajin sule Yusufu. Bisa kaidar da dokar zabe ta tanada.
Wani na kusa da Majigiri ya tabbatar mana da labarin, cewa ana wannan maganar amma ba a kammala ta ba.
Yace Majigiri Dan siyasa ne, mai son jama arsa da cigaban su amma ba girman Mukami ba.
Yace majigiri yana neman ya zai kawo cigaba ne ga al umma ba wai wane girman mukami ba,shi ya sa muka Sanya ya amince da wannan tsarin.
Ya kara da cewa shima Wanda yaci zaben takarar Alhaji sule Yusufu ba ya shigo siyasa bane don mukami ya shiga ne don taimakon al umma .
Idan wannan takarar ta tabbata, majigiri zai shiga kundin tarihi.na yayi rike shugaban jam iyya,yayi takarar mataimakin gwamna.yayi ta gwamna.yanzu zai yi ta Dan majalisar tarayya.
Majigiri zai kara da Babban yaron shi a siyasa,Alhaji Mansur Ali mashi a jam iyyar APC. Mansur Ali mashi ya koyi horon siyasa ne a wajen Majigiri.
Don haka akwai yiyuwar a zaben 2023 a yi karon battar karfe tsakanin yaro da ubangidansa a zaben Dan majalisar tarayya na mashi da Dutsi.

HUKUMAR DSS NANEMAN WANDA YAYI WAKAR BATANCI GA MATAN KANNY WOODBiyo bayan wani korafi da wasu matan Kannywood s**a aike...
25/06/2022

HUKUMAR DSS NANEMAN WANDA YAYI WAKAR BATANCI GA MATAN KANNY WOOD
Biyo bayan wani korafi da wasu matan Kannywood s**a aikewa Shugaban MOPPAN na Kasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, mai taken: “KORAFIN CIN ZARAFI DA WANI MAWAKI MAI SUNA ‘SUFIN ZAMANI,” a cikin takarda, wadda tsohuwar jarumar fim Wasila Isma’il ta sanya wa hannu, a madadin Matan Kannywood, MOPPAN, a cikin gaggawa ta tsunduma cikin binciken korafin, daga bisani, ta rubutawa Hukumar DSS, domin ta yi abin da ya dace.

Bayan da MOPPAN ta aikewa hukumar ta DSS ne, hukumar ta yi nata ayyuka din, kana ta nemo gami da cafke mawakin.

A ranar Larabar nan 22 Yuni ne, hukumar ta kamo Sufin Zamani, kana kuma ta bayar da belinsa a ranar Alhamis (23 ga Yuni), bisa wadannan sharudda:

1. Zai yi bidiyo da Audio na ban hakuri da kuma karyata kansa game da wakar batancin da ya yi.

2. Zai yi waka kishiyar wacce ya yi, wato ya bi matan kannywood, ya fadi alherinsu kuma ya nuna masu zaman aure ne.

3. Zai rubutawa MOPPAN takardar ban hakuri

4. Zai rubutawa hukuma undertaking cewar ba zai kuma yin batanci ga duk wani dan fim ba.

5. Bayan yayi wannan kuma hukumar DSS za ta yi masa hukunci da ya dace, domin yayi musu karya a farkon kamun da aka yi masa.

Duk wannan ya biyo bayan amincewa da ya yi cewa ya aikata laifin.

Sa hannun
Al-Amin Ciroma
Kakakin MOPPAN na Kasa

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Media News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Media News:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share