
16/07/2025
DA DUMI-DUMI: Shugaban 'yan kasuwar kayan miya (Kayan Gwari) na babbar kasuwar jihar Gombe Alhaji Sani Waya, ya ajiye mukaminshi na shugabancin kasuwar.
...Inda mutane da yawa Dattijai, maza da mata s**a dinga zubda kwalla kan jiye shugabancin nashi.
Haka zalika tsohon shugaban ya damka shugabancin kasuwar hannun kwamitin da zasu jagoranci yin zabe ga 'yan takarar neman shugabancin kasuwar domin a tabbatar da adalci na ganin wanda 'yan kasuwar suke so ya zama sabon shugaban kasuwar.
Tsohon shugaban kasuwar Alhaji Sani Waya, ya bayyana irin dumbin nasarorin da s**a samu tare da tarin kadarori da abubuwa masu yawa da s**a yi nasarar siyawa kasuwar a tsawon shekarun da s**a shafe sun shugabantar kasuwar.
Daga Abba Sani Pantami