31/08/2025
Bayani game da “FINANCE SECTION” dake cikin Opay wallet
1. OWealth
Wannan wani sashin saka jari ne da Opay ke bayarwa tare da BlueRidge Microfinance Bank.
Idan ka saka kudi a ciki, zaka rika samun riba kullum (daily returns/Interest).
Abin da ya fi kyau shi ne zaka iya cire kuɗin ka a kowane lokaci (ba sai ya kai wani lokaci mai tsawo ba).
Ana iya cirewa daga Autosave, sannan ana iya cire Interest da ake samu ta hanyar kashewa.
2. Targets
Wannan yana baka damar saita manufa (goal), misali:
- Tara kuɗi don aurarwa,
- Tara kuɗi don sabuwar waya,
- Ko tafiya.
Zaka iya saita ta daily, weekly, ko monthly contribution har sai ka cimma burinka. za ka saita adadin yawan kuɗin da kake so ya taru da tsawon watannin da kake su yayi kafin ka cire kuɗinka.
3. SafeBox
Wannan yana k**a da ajiyar kai–tsaye (automatic savings).
Zaka iya saita shi ya rika ɗaukar wani kason kuɗin ka kullum, ko mako–mako, ko wata–wata ya ajje maka a cikin SafeBox.
Banbancinsa da target shine; shi sau huɗu kawai ake iya cire kuɗin cikinsa a shekara (Quarterly)
4. Fixed
Wannan shi ne ajiyar da ake kullewa (Fixed Deposit).
Min. ₦1000 zaka iya saka, kuma zaka iya kulle shi daga 7 zuwa 1000 days.
Idan ka cire kafin lokacin da ka saita, akwai yiyuwar ka rasa wani kaso na ribar ka tare da charges da za a maka saboda karyawa.
5. Spend & Save
Wannan yana aiki ne da tsarin "spend small, save small".
Duk lokacin da kayi amfani da wallet ɗin ka wajen kashe kuɗi, wani ƙananan kaso zai rika zuwa ajiyar Spend & Save.
Kai da kanka za ka saita adadin da kake so kana saving bayan kowace transaction da kayi da wallet naka.
Ana iya cire kuɗin da akayi saving a kowane lokaci.
6. Savings Report
Wannan yana baka damar ganin tarihin ajiyar ka da ci gaban da kayi.
Zaka iya ganin yadda kake yin saving a baya da yadda kake tafiya yanzu.
Amfanin Opay wallet Finance section a taƙaice:
👉 Yana ƙarfafa mutane su ajiye kudi ta hanyoyi daban–daban.
👉 Yana taimakawa wajen samun ƙarin kuɗi ta riba daga ajiyar ka.
👉 Yana koya maka discipline a harkar kuɗi don cimma manufofin ka.
Duk abin yana cikin app ɗin ka ba tare da wahala ba.
Zanyi bayanin yadda za ka yi amfani da kowanne dalla-dalla ta hanyar amfani da screenshot. Tare da bayanin amfaninsu, har ma da labarin yadda ya taimakawa mutane da dama wajen iya ajiye kuɗin haya, makaranta, sayan waya, kayan lefe da sauransu In sha Allahu 😊