24/08/2026
Kada ka yarda da duk wanda zai ce maka: “Ni zan shigar da kai Aljanna.”
Ka kalli Sahabban Manzon Allah ﷺ—mutanen da s**a yi imani, s**a yi hijira, s**a yi jihadi, s**a ciyar da dukiyoyinsu, s**a yi ibada, kuma Annabi ﷺ ya yi musu bushara da Aljanna—amma duk da haka sun kasance masu tsoron Allah da tsoron ranar da za su hadu da Shi.
Sun san cewa Aljanna da wuta suna hannun Allah ne, kuma hukuncinSa ba wasa ba ne.
Wasu daga cikin maganganun Salaf ma suna nuna irin tsoron da suke da shi; mutum yana ganin ayyukansa ba su isa su sa shi ya yi wa kansa tabbacin tsira ba, sai dai ya dogara ga rahmar Allah.
Don haka idan Sahabbai da Salaf s**a kasance cikin tsoron Allah duk da irin ayyukan alherin da s**a yi, ta yaya wani mutum zai zo ya gaya maka cewa shi ne zai tabbatar maka da Aljanna?
Ka nemi Allah, ka yi biyayya gare Shi, ka yawaita ayyukan alheri, ka nisanci zunubi, kuma ka roƙi Allah rahama da kyakkyawan ƙarshe.
Aljanna mallakar Allah ce. Ba wani mutum ne yake raba ta ba.
Allah Ya sa mu dace da rahamarSa, Ya gafarta mana, Ya sa mu cika da imani, kuma Ya shigar da mu Aljannatul Firdausi. 🤲🏽