
07/08/2025
DA DUMI-DUMI: ‘Yan Sanda Sun Karya Wa Sowore Hannunsa na Dama, Sun Kuma Tura Shi Wani Wuri da Ba a Bayyana ba a Abuja
Rahotanni daga jaridar Sahara Reporters sun tabbatar da cewa da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar yau, wata tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin wani CSP daga sashen sa-ido na Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP Monitoring Unit) sun kutsa cikin ɗakin tsarewar Omoyele Sowore da ke hedkwatar FID a birnin tarayya, Abuja.
A yayin wannan kutse, jami’an sun yi amfani da ƙarfin tsiya, inda s**a karya hannun daman Sowore, kafin daga bisani su ɗauke shi zuwa wani wuri da har yanzu ba a bayyana ba.