Dugun-ma'azu Media Struggle For Survival

Dugun-ma'azu Media Struggle For Survival Community Development Organizational

Ko kun Fahimci abin da Chairman Ke yima Dariya kuwa?
09/11/2023

Ko kun Fahimci abin da Chairman Ke yima Dariya kuwa?

Wannan Sune Kalaman Da Wadannan Malaman Sukafiyi a wajan Waazi.Wane fata kuke masu?
09/11/2023

Wannan Sune Kalaman Da Wadannan Malaman Sukafiyi a wajan Waazi.
Wane fata kuke masu?

Ana maka irin wannan shagwabar ko kai ma muna mata ka kwaso?Kai! Shagwaba duniya ne! My Queen Hadiza Aliyu❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️...
08/11/2023

Ana maka irin wannan shagwabar ko kai ma muna mata ka kwaso?

Kai! Shagwaba duniya ne! My Queen Hadiza Aliyu
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Daga shafin shaharerin Dan wasa Film nan BMB

Ni yanzu na karbi tuba duk narabar da kayan danake sanyawa - murja kunya
07/11/2023

Ni yanzu na karbi tuba duk narabar da kayan danake sanyawa -
murja kunya

Cikin Hotuna: Yadda wadanda s**a jikkata a harin kisan kiyashin da yan bindiga s**a kai wa masu gudanar da mauludi a kar...
07/11/2023

Cikin Hotuna: Yadda wadanda s**a jikkata a harin kisan kiyashin da yan bindiga s**a kai wa masu gudanar da mauludi a karamar hukumar Musawa jihar Katsina suke ciki

Yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wabi a lokacin da ake tsaka da gudanar da bikin Mauludin a kauyen Kusa, a daran jiya Lahadi, inda akalla mutum 20 sun sami munanan raunuka, mutum 13 yara da manya kuma s**a mutu, k**ar yadda Shugaban karamar hukumar Musawa ya tabbatar wa BBC

Haka shima mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, ya sheda wa Daily Trust cewa rundunar yan sandan jihar Katsina ta fara gudanar da bincike game da wanda s**a kai harin, inda ya ce duk kuma wanda rundunar ta k**a da hannu a wannan kisan gillar ba tare da bata lokaci ba za su gurgurar da shi a gaban kotu

Taƙaitaccen Tarihin Malam Mamman Daura-An haife shi a garin Daura dake Jihar Katsina a Shekarar 1939. - Ya yi Karatun Fi...
07/11/2023

Taƙaitaccen Tarihin Malam Mamman Daura

-An haife shi a garin Daura dake Jihar Katsina a Shekarar 1939.

- Ya yi Karatun Firamare a Daura Elementary School.

- Ya yi Karatun Sakandare a Midil ta Katsina, ya karasa a Makarantar Lardi ta Okene (Provincial School Okene) a Shekarar 1956 yana da Shekara 17 a duniya.

- Ya fara aiki da NA ta Daura (Daura Native Authority) na yan shekaru, sai ya koma Kamfanin Sadarwa na Kasa wato Nigerian Broadcasting Corporation.

- Malam Mamman Daura yana cikin mutane 6 da Firimiyan Jihar Arewa Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ya zaba domin tafiya Karatu Ingila, inda ya samu gurbin karatu a Trinity College Dublin.

- Daga Shekarar 1962 zuwa 1967 Malam Mamman Daura ya karanci Ilmin Tsimi da Kimiyyar Siyasa a Ingila.

- Ya koma yayi digiri na biyu a bangaren kasuwanci da sanin mak**ar aikin Gwamnati a Trinity College Dublin dake Ingila.

- A shekarar 1968, ya dawo yayi aiki a ofishin Gwamnan Jihar Arewa ta Tsakiya Marigayi Birgediya General Abba Kyari a matsayin mai taimaka masa kan harkokin siyasa ko kuma Sakataren Harkokin Siyasa Na Ofishin Gwamnan.

- A 1969, ya fara aiki da Kamfanin Jaridar New Nigerian Newspaper a matsayin Babban Edita. Ya zama Shugaban Kamfanin a Shekarar 1974.

- A karshen Shekarun 1970s, Malam Mamman Daura ya zama memba a Board-Board na Kamfanoni da Manyan Ma'aikatun Gwamnati: Kadan daga ciki sune:
- News Agency of Nigeria
- Funtua Textiles Limited
- Nigerian Television Authority (Chairman Na Board) a Shekarar 1980s
- African International Bank
Da dai sauran su.

- Malam Mamman Daura yanzu haka yana nan cikin koshin lafiya, Yana da Shekara 84 a Duniya.

- Malam Mamman Daura Dan Uwa ne ga Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari GCFR.

Allah Ya Ƙara Lafiya Da Nisan Kwana!

Daga Imrana Daura

Ana sa ran yau ɗin nan gwamna Dikko Raɗɗa zai gabatar da ƙudurib kasafin kudinsa ba farko, na shekarar 2024 mai k**awa d...
07/11/2023

Ana sa ran yau ɗin nan gwamna Dikko Raɗɗa zai gabatar da ƙudurib kasafin kudinsa ba farko, na shekarar 2024 mai k**awa don yi wa al'ummar jihar Katsina aiki da su, a zauren Majalisar Dokokin Jihar Katsina

Mi za ku so ji, a cikin jawabin gwamnan ya ambato a yau?

Wane ɓangare za ku fi so gwamnan ya fi ware wa kudi don amfanuwar al'ummar jihar Katsina.
daily Post

Yanzu fa a Kano, da zaran Dare yayi an hango wannan motar, hantar kowa kadawa take yi. Ina kanawa suke, shin kuna goyon ...
07/11/2023

Yanzu fa a Kano, da zaran Dare yayi an hango wannan motar, hantar kowa kadawa take yi. Ina kanawa suke, shin kuna goyon bayan sumamen da hukumar Hisbah take gudanarwa cikin kwanakin nan?
Wanne Fata Zaku Hukumar Hisba

Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi Raji'un: 'Yan bindiga sun shigo gida-gida a Sayaya ta karamar hukumar Matazu sun kashe mutum...
07/11/2023

Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi Raji'un: 'Yan bindiga sun shigo gida-gida a Sayaya ta karamar hukumar Matazu sun kashe mutum 5 ciki har da mahaifina - Inji Ahmad Ibrahim

Cikin daran jiya Litinin wayewar garin yau Talata yan bindiga sun afko cikin garinmu Sayaya dake nan yankin karamar hukumar Matazu, jihar Katsina sun bi gida-gida, har sun kashe mana mutum biyar, wallahi ciki har da mahaifina.

Sannan sun kore shanayen mutane masu yawa, ga hoton mahaifin nawa nan da s**a kashe mana na turo maku" Inji wani mazaunin garin mai suna Ahmad Ibrahim da ya aiko wa Katsina Daily News, inda ya bayyana yadda wannan mummunan alamar ya faru a garin nasu, da yan bindiga s**a kashe alaƙalla mutum 5 ciki har da babansa

Wannan na zuwa ne bayan a daran ranar Litinin kuma wasu yan bindigar s**a bude wa masu biki mauludi wuta, a yankin karamar hukumar Musawa dake makwabtaka da Matazun, inda ko a nan ma sai da yan bindigar s**a kashe mutum 13, tare da jikkata kusan mutum 20 da munanan raunuka na harbin bindiga.

Katsina Daily News

15/04/2023

Yau ake gudanar da zabukan cike gurbi a garuruwa daban-daban da ba kammala zabensu ba a Nijeriya

Ana dai kammala zaben gwamna a jihar Adamawa da Kebbi, sannan ana kammala na yan majalisar dattawa a Sokoto, Zamfara da kuma wasu na yan majalisar wakilai da na dokokin jihohi da dama a fadin kasar nan, ciki har da guda uku a jihar Katsina.

Yan bangaren Shema a PDP sun fara komawa APC, yayin da Masari ya yi wa Alh Sani Anani da tsohon shugaban karamar hukumar...
21/02/2023

Yan bangaren Shema a PDP sun fara komawa APC, yayin da Masari ya yi wa Alh Sani Anani da tsohon shugaban karamar hukumar Kankara Hon Abdulhadi Kankara wanka da s**a sauya sheka daga PDP zuwa APC yau a fadar gwamnatin jihar Katsina.

A karo na biyu Sheikh Sani Yahaya Jingir ya roki Sarkin Musulmi kan ya sa baki a yi Muslim Muslim Ticket  inda ya ce "Da...
21/02/2023

A karo na biyu Sheikh Sani Yahaya Jingir ya roki Sarkin Musulmi kan ya sa baki a yi Muslim Muslim Ticket inda ya ce

"Dan Girman Allah Mai Alfarma Sarkin Musulmi ka gaya wa na tare da kai da dukkanin sauran Musulmai da su zabi Muslim-Muslim Ticket'"

Address

Dugun-mu'azu Sabuwa Local Government
Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dugun-ma'azu Media Struggle For Survival posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dugun-ma'azu Media Struggle For Survival:

Share

Category