
15/12/2024
MUNA BA ‘YAN UWANMU TABBACIN MUNA NAN DARAM A KAN ABIN DA S**A BAYAR DA JINANANSU A KAI
- Inji Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky a taron shekara tara (9) da Waki’ar Buhari ta 2015 da aka yi a Abuja
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Da yake jaddada mika ta’aziyarsa ga ‘yan uwa a yayin tunawa da kisan kiyashin Zaria da sojoji s**a yi a shekarar 2015, a ranar Asabar 14 ga watan Disamba 2024, Jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya ba da tabbaci ga wadanda aka kashe a lokacin cewa muna nan daram a kan tafarkin da s**a bayar da jinanensu a kai har karshen rayuwarmu.
Jagoran ya mika jajensa da cewa: “Muna jajantawa dukkan iyalan wadanda aka kashe; iyayen da aka kashe musu ‘ya’ya, da ‘ya’yan da aka kashe musu iyaye; da matan da aka kashe musu mazaje, da mazajen da aka kashe musu mata; da ‘yan uwan da aka kashe musu ‘yan uwansu; da masoyan da aka kashe musu masoyansu; da abokanan arziki, duk muna jajanta musu. Sannan muna kara wasiyya ga junanmu da mu daure, jarabawa ce.”
Ya kara da cewa: “Muna ba wadanda s**a sadaukar da ransu, s**a ba da jinanensu, s**a dake a wannan waki’a (ta 12-14 ga Disambar 2015) da waki’o’in da s**a biyo baya sak**akon wannan, muna ba su tabbacin cewa muna nan daram akan abin da s**a bayar da jinanensu, Insha Allah ba za mu canza ba.”
Da yake bayanin waki’ar, Jagora ya bayyana cewa, mahukuntan kasar nan sun dade suna yunkurin dirar wa Harkar Musulunci da nufin kawar da ita. “Sun dade suna tsara abubuwansu (na yunkurin kawar da mu), saboda haka wannan abu tsararre ne. To kuma mun samu wani labari, cewa za a dira mana ranar Asabar 12 ga watan Disamba, kuma lallai mu ake nufi, kuma an gama shirya soja kaf, amma ba a ce musu me za a yi ba.”
Ya bayar da misalan yadda a lokuta daban-daban aka rika kitsa ma soja abubuwa daban-daban da nufin su kawo wa ‘yan uwa hari a lokuta daban-daban, k**ar cewa an sace wani mutum, kuma soja za su kwato shi (a Gyallesu), da cewa an samu labarin (‘yan uwa) za su kitsa juyin mulki kuma soja za su hambare yunkurin. Yace; “amma duk (sojan) ba su san wannan wane aiki ne za su yi ba, har abubuwan su kwaranye.”
Yace: “To wannan karon da Allah Ya tashi tozarta su, sai ba su iya cewa komai ba, sai cewa an tsare hanya. Sai s**a shirya dirama, s**a dauki wasu mutane s**a ba su dubu biyar-biyar s**a zo suna ta ihu. Ihu sosai wanda ba wanda ya san ‘yan uwa da zai ce wadannan ‘yan uwa ne. Mutane gari ma suna cewa wadabbab va ‘yan uwa ba ne, don har sun saka ma taya wuta, wanda yake a tarihinmu na shekara 40 ba mu taba kona taya ba. Kuma sun rike sanduna wanda ba a taba ganinmu da sanduna ba. Har mutanen gari suna cewa wannan ba Shi’a ba ne. Suna ta ihu sun saka bakaken kaya. Inda ma s**a buga kenan, don Asabar din nan wanda ya yi daidai da 12 ga watan Disamba, rannan ne 1 ga watan Rabi’ul Auwal, kuma a rannan za mu canza tuta ne; za mu cire bakin tuta mu saka koriya mai rubutu fari da ‘Labbaika Ya Rasulalllah’, saboda haka rannan ranar farin ciki ne, za a shiga watan Mauludi ne, ba ranar jaje ba ne, saboda haka sun buga da s**a saka bakin kaya. Kuma s**a buga da s**a yi ihu.”
Jagora yace daga baya duk sun kai wadannan bayanan diramar tare hanyar kotunda daban-daban amma kotuna sun tabbatar da ‘yan uwa basu tare hanyar ba. Yace: “Duk sun kai wadannan diraman kotuna, sun ce gashi an tsare hanya ne. To kotuna High Court daban-daban har guda uku a Kaduna, kowannensu yace ba a tsare hanya ba! Ba ma kawai wadanda aka kawo gaban kotu ba su tsare hanya ba, sun ce tsare hanyar ma ba a yi ba! To ina mamakin har yanzu saboda bushewan zuciya, kaga mutum ya kekeshe kasa yace wai abin da ya faru sak**akon wai an tsare hanya ne. Kuma s**a ce an yi barazana ga rayuwar wani mutum wai shi Buratai. To shi ma duk sun kawo wadannan abubuwan a kotu, duk kotu tace ba a haka ba ne.”
Jagora yace: “Mu kaddara an tsare maka hanya, mu kaddara kuma doka ta yi tanadin duk wanda ya tsare ma wani babban mutum hanya kashe shi ake yi. To ya za a yi kisan? Dole a k**a shi a kai shi kotu, kotu ta yanke masa hukunci ko? Ba wanda ya baka dama kawai sai ka harbe mutum, ka zartar da hukuncin, in ma hukuncin hukuncin kisa ne. To kuma idan hukuncin kisa ne, an tsare hanya, kuma kai an baka dama kana iya kashe wa, wanda na san ba za a iya baka wannan damar ba, to me ya hada ka da gyallesu? Me ya kai ka Gyallesu? Ita ma tana hanyar Sakkwato ne? – Don Husainiyyah ita ce No. 1A akan hanyar Sokoto… (da ke Zariya)
“Idan mu kaddara hukuncin wanda ya tsare maka hanya shi ne ka kashe shi, to a No. 1A-B a Sokoto Road an tsare maka hanya, to me ya kai ka (Darur Rahma da ke) hanyar Jos? Darur Rahma ba tana daidai kan hanyar Jos ba ne ma, sai ka saki hanyar Jos ka k**a hanyar wani kauye da ake ce masa gidan Rahma, wanda ta nan muka ba gurin suna Darur Rahma… Me ya kai su nan, wanda sai ka bar ma hanyar Jos? Me kuma ya hada su da Fudiyyah Center, wadda take hanyar Wusasa? Ita ma tana kan hanyar Buratai ne? Me ya kai su kuma cikin gari gidan mahaifiyata, inda na bizne ta. S**a je har s**a rusa gidan a lungun da dakyar muke shiga mota?... Har ma s**a ce za su kwakwale kabarin mahaifiyata, sai da mutanen unguwar s**a fito s**a ce sai dai a yi fada, ba za su yarda a yi wannan abin a gabansu ba. Akwai wani tsoho da yace sai dai ya mutu, ba zai yarda a yi wannan abin a gabansa ba, ya san wacece wannan da aka bizne a wajen.
“Kuma me ya kai su tsare duk hanyoyin da ake shiga cikin Zariya, daga hanyar Kano, s**a tsare wajen masallacin Annur, duk motar da s**a gani da alamar ‘yan uwa sai su harbe su. Sannan kuma ta hanyar Malumfashi, shi ma in s**a ga alaman wani mai k**a da dan uwa, ko yar uwa mai hijabi sai su watsa ma motar fetur su kona gabadaya, da direba da kwandasta da duk wadanda ke ciki kona su suke yi. Na hanyar Jos akwai wanda yake bani labarin su rika rabawa, sai su kwashe wadanda suke so, sai su kyale direba da kwandasta su wuce, sannan su shiga da wadannan cikin fadama su harbe su. Har wani soja yana ba da labarin cewa ‘mun ta harbe su suna cewa Allahu Akbar.’”
Shaikh Zakzaky ya bayyana takaicinsa ga yadda azzaluman mahukuntan kasar nan a yanzu ke takurawa Harka ta hanyar hana hatta a ba da hayan dakunan taro a Abuja, inda yace wai suna haka ne bisa hujjar wai an haramta IMN. Yace: “Yanzu duk sun bi inda aka yi taro sun gargadi mutanen kar su sake bamu wuri. Hujjarsu shi ne wai mu sunanmu IMN ne, kuma wai an yi ‘banning’ dinmu.”
Yace: “Su kansu ba su san doka ba. Ba yadda za a yi su kai wannan kalmar ‘banning IMN’ zuwa kotu, saboda babu wata doka a gaban wata kotu da tace an yi ‘banning’ wani abu wai shi IMN. Kun san wa ke doka a kasa a bisa ka’idojin doka? Kotu tana yin doka ne? An ce shi shugaban kasa an bashi dama yana iya haramta kungiya na kwana 14. To shi ne wannan abin, tsanani kwana 14 ne a kwansitushen, amma yanzu yau tun 2019 wai sun yi ‘banning IMN’.”
Ya kara da cewa: “To kuma mu bamu taba kiran kanmu IMN ba, su s**a saka mana wannan sunan. Mu mun ce muna Musulunci ne, mun ce muna addini ne mu, sunan addini ne IMN? In muka ce ma mutanen nan yaushe aka kafa IMN din? Kila su ce 1980 ne aka kafa. To shi addinin Musulunci a 1980 aka fara shi? Ashura a 1980 aka fara? Mauludin Annabi a 1980 aka fara? Wani abu ne haka nan, duk abin da muka yi na addini sai ku ce (IMN)?”
Yace: “A Zaria akwai wani alkalin Majestari da yake ma ‘yan uwa hukunci wai ya daure su wai sun shiga kungiyar IMN. To shi ne sai CJ na wancan lokacin yace a tuhume shi, ina ya ga dokar? Bisa ka’ida shi Majestari ba yana karanta doka a jarida ba ne, ana bashi dokan ne a rubuce a kotu (da ke samansa).”
Jagora ya kuma bayyana yadda azzaluman mahukuntan kasar nan da jami’an tsaronsu a lokuta daban-daban suke karya dokan kotunan kasar nan. Yace: “Karya doka suke yi. Wadansu dokoki ne basu karya ba? Kun ga alal misali, kotu tace a sake mu ba tare da gindaya sharadi ba, a biya mu ‘compensation’ (kudin ramuwa), a bamu gidan da za mu zauna a gurin da muka zaba a Arewacin Nijeriya, kuma a ajiye masu gadi don su kare mu daga hadarin da s**a ce suna kare mu daga gare shi. (Alkalin) yace, kuma wannan ba yana nufin za a je a tsare mu ne a gidan ba, muna da hurriyan mu je duk inda muka ga dama. To amma ba su bi umurnin kotun ba har yanzu (tun 2016).
“Kuma ‘yan uwa da aka saka karo na farko su 77, kotu ta basu takardar cewa kowannensu yana iya komawa bakin aikinsa, kuma a biya shi albashinsa na duk watannin da ya yi a tsare, saboda tsarewan da aka yi ba bisa ka’ida ba ne, don bai yi laifin komai ba. Amma sam gwamnati ba ta komar da su ayyukan nasu ba, kuma bata biya su ba. Haka ma kotu na biyu, duk haka nan ne.
“Irin wannan ya auku a wani lokacin Ashura a Sakkwato, sun kashe wasu ‘yan uwa, ‘yan uwa muka kai su kotu, kotu tace abin da (‘yan sandan) s**a yi ya saba ka’ida, dole su biya ‘compensation’. S**a daukaka kara. Kotun daukaka kara tace dole sai sun biya ‘compensation’, amma har yau ba su bi umurnin kotun ba!
“Nan a Abuja, sun hahharbi mutane na July, 2019, s**a dauki gawarwaki, s**a tafi ‘mortuary’ s**a ajiye, aka yi aka yi su bayar da su s**a ki. Aka kai su kotu, kotu tace su ba da wadannan gawarwakin (ga ‘yan uwa), kuma su biya ‘compensation’. S**a ki. Sai da aka daukaka kara, aka kai su wani kotu, wata kotu tace, to shi IG ya kawo dalilin da yasa ba za shi kurkuku ba saboda kin bin doka? Sannan ne sai yace a ba su gawan, amma ‘compensation’ bai bayar ba.
“A Kaduna ma kazalik, sun harbi ‘yan uwa, an kai su kotu, kotu tace lallai su biya ‘compensation’, har yau basu ba da ko kwabo ba! Duk doka su basu bi, suna karairaya doka yadda ransu ya ga dama, abin da s**a ga dama shi suke yi.” Inji Shaikh Zakzaky.
Jagoran ya kuma jaddada yabawansa ga ‘yan uwan da s**a tsaya kyam s**a dake a tsawon wadannan shekarun waki’ar ba tare da sun ja da baya ba wajen nuna yatsa ga azzalumai. “Mun ga wadanda s**a dake daram ba su ja baya ba. Har ma nake cewa, inda a ce su mutanen kasar nan duk abin da ka yi musu suna yin shiru ne. Za a ce banda su wane. Akwai wadanda za a ce su ba su yin shiru, ba sa yarda da zalunci. Har ma su mutane suna shaida, don haka ne ma, lokacin da suke fama da matsaloli (na tsadar rayuwa) suke cewa, da ‘yan Shi’a za su taimaka, da abin ya yi daidai. Ka san Dan Shi’a ba ya ja da baya, ko za a harbe shi ne. To amma shi ya san dalilin da yasa ba ya ja da bayan, yana yin haka ne da yakinin cewa yana yin addini ne, ba zai yi maka akan harigidon duniya ba.” Inji Jagora.
13/Jimada ath-Thaniyah/1446
14/12/2024