
02/03/2025
GASAR GAJERUN LABARAN HAUSA MAI TAKEN: AIKI DAI MALAM...
GABATARWA.
An shirya da samar da wannan gasa domin zaburar da marubutan Hausa da fayyace kyawawan ayyuka da manufofin mai girma gwamnan jihar Jigawa H. E Mallam Umar Namadi Ɗan Moɗi ta hanyar ayyanawa cikin tsari da salo na samar da labari irin na zube.
JIGO/MANUFA.
Faɗaɗa bincike tare da burtso ayyukan gwamnan jihar Jigawa da yadda s**a canja da taɓa rayuwar al'umma.
DOKOKIN GASAR.
1. Za a fara aiko da tsakuren labarin da bai zarta kalma 1500 ba, kafin daga bisani za a zaɓi labaran da s**a hau layi a musu bita kana su aiko da cikakken labarin da bai haura kalma 3000 ko ƙasa da kalma 2500 ba.
2. Lallai ne labaran su kasance sabbi, ba a taɓa bugawa ko wallafa su a kowace kafa ba.
3. Mutum biyu za su iya haɗin gwiwar samar da labari guda.
4. Za a yi la'akari da duk ƙa'idoji na rubutu, k**a daga kan haruffa masu lanƙwasa.
5. Za a tura labaran a tsarin Microsoft Word ko PDF files ta wannan email ɗin: [email protected]
6. Bayanin marubuci (suna, lambar waya da saura) za a tura su daban a cikin mail ɗin ba a cikin labarin ba.
7. Za a aiko da tsakuren labaran daga 02/03/2025 zuwa 02/04/2025.
8. Wanda s**a samu nasarar zagaye na farko ne (mutum ashirin ) kawai za a tuntuba da ba su bita domin su aiko da cikakkun labaran.
9. Za a wallafa da buga duk labaran ashirin a bikin ƙaddamar da littafin da bayar da kyaututtuka ga zakarun gasar.
10. Hukuncin alƙalai na ƙarshe shi ne hukunci, ba za a kuma duba, canja ko tattaunawa a kansa ba.
11. Duk labaran da aka shiga gasar da su mallakin gasa ne, ba a yarda a yi amfani da su ta kowace fuska ba.
KYAUTUTTUKA.
1. Na daya ₦500,000.
2. Na biyu ₦300,000.
3. Na uku ₦200,000.
4. Na 4 -10 ₦100,000 kowane.
5. Na 11-20 ₦50,000 kowane.
Domin ƙarin bayani ko tuntuɓa a nemi wannan lambobi:+2348151622690, +2348038093037, +2347065759892, +2347037852514
+2347066419663
© Jigawa New Media Office
Bamai Dabuwa