25/08/2026
YADDA ZAGAYEN MAULUDI YA GUDANA A KATSINA.
Da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Talatar 12 ga watan Rabi’ul Awwal, 1448H, wanda ya yi daidai da 25 ga watan Agusta, 2026, ’yan’uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na garin Katsina s**a fito ƙwai da kwarkwata don nuna murnarsu da zagayowar ranar haihuwar Manzon Rahma (S).
Zagayen wanda Sheikh Yakub Yahaya Katsina ya jagoranta ya samu halartar ɗimbin jama’a daga ciki da wajen garin Katsina, tun daga Malamai da Ɗaliban Fudiyoyi da Islamiyyu da Forum-Forum da Harisawa da Sha’irai da sauran ’yan’uwa Maza da Mata, kowannensu cikin kyakkyawar shiga, suna farin ciki da annashuwa. Yayin da wasu ke raba kyaututtuka, alewa, turare, da sauransu.
An fara zagayen ne daga Unguwar Madawaki, inda mahalarta s**a ratsa sassa daban-daban na tsakiyar birnin Katsina, har zuwa Filin Samji, inda a nan ne aka kammala zagayen.
Bayan kammala zagayen, Sheikh Yakub ya gabatar da jawabin rufewa a matsayin Goron Mauludi na shekarar bana. A cikin jawabin nasa, ya ja hankalin al’ummar Musulmi kan muhimmancin haɗin kai, inda ya nuna cewa; “shi haɗin kai ba yana nufin ka bar abin da kake yi ba ne ka zo ka yi nawa, haka nima, a’a yana nufin mu haɗu a wani babban jan layi ne wanda dukanmu za mu yi magana da murya ɗaya a kanshi, haka nan haɗin kan nan shi ne ƙarfinmu” — Ya bayyana.
Haka kuma a wani ɓangaren na jawabinsa ya yi kira ga al'uma a kan koyi da halayen Manzon Allah (S) irin su gaskiya da riƙon amana, wanda kowa zai yi ƙoƙari ne ya gyara kansa kafin bayyanar Imam Mahdi (A.F) wanda wannan zamanin na shi ne, kuma alamomin bayyanarsa na ta ƙara yawaita.
An yi zagayen Mauludin lafiya an kammala lafiya. Za ku iya kallon yadda zagayen ya gudana a cikin hotuna.
#مولدالنبوي
25Aug2026