18/07/2026
An Gudanar da Taron Sauraron Ra'ayoyin Jama'a a Kaita Domin Kasafin Kuɗin 2027
An gudanar da taron sauraron ra'ayoyi, korafe-korafe da buƙatun al'ummar Kaita Ward a Hedikwatar Karamar Hukumar Kaita, domin tattara shawarwarin da za su taimaka wajen tsara kasafin kuɗin shekarar 2027.
Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki, shugabannin gargajiya, malamai, wakilan gwamnati, mata, matasa, 'yan kasuwa da sauran shugabannin al'umma. Mahalarta taron sun gabatar da shawarwari kan fannoni k**ar samar da ruwan sha, ilimi, lafiya, noma, hanyoyi, tsaro da bunƙasa matasa da mata.
Masu jawabi sun yaba da irin yadda al'ummar Kaita s**a ba da gudunmawar shawarwari, tare da bayyana cewa tsarin sauraron jama'a yana taimakawa wajen tabbatar da cewa kasafin kuɗi ya dace da ainihin buƙatun al'umma.
An kammala taron cikin nasara tare da fatan cewa shawarwarin da aka tattara za su taimaka wajen samar da ci gaba mai ɗorewa ga Kaita Ward da Karamar Hukumar Kaita baki ɗaya.