
22/10/2022
Kungiyar Hada Kan Matasan Arewa Zata Karrama Hazikin Matashi Ambasada Kaikai Da Lambar Yabo
Matashin Dan Siyasa Kuma mai bada tallafin Jin kai dan Asalin Jihar Katsina Ambasada Injiniya Abubakar Shehu Kaikai, na daya daga cikin muhimman mutane da Kungiyar Hada Kan Matasan Arewa, wato ' Arewa Youth Mobilization Forum' zata karrama a kwanan nan.
Bayanin tabbatar da karrama Injiniya Kaikai da lambar yabon na a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labaru na Kungiyar Kwamarad Yusuf Mahmud.
Kamar yadda takardar ta bayyana, za'a gabatar da lambar yabon ne ga hazikin matashin Ambasada Kaikai a lokacin wani babban taro da Kungiyar ta shirya zai gudana a Jihar Kaduna a ranar 29 ga wannan watan da muke ciki.
An dai karrama Kaikai ne bisa ga dogon nazari da bincike da Kungiyar ta gudanar akan ayyukan jin kan al'umma da yake gudanarwa, musamman a Mazabar shi ta Kankia/Ingawa/Kusada da ke Jihar Katsina.
Taron gabatar da lambar yabon zai gudana ne a 'Arewa House' kusa da Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a ranar 29 ga watan Oktoba da muke ciki da misalin karfe 4 na yamma, bayan Kammala daurin auren Shugaban Kungiyar.
Da Accuracy News ke zantawa da shi akan karamcin, hazikin matashin Ambasada Kaikai, ya nuna farin cikin shi akan yadda Kungiyar ta zabe shi daga cikin wadanda zata baiwa lambar yabon.
Injiniya Kaikai ya ce, karamcin zai kara mashi kwarin guiwa na cigaba da aiwatar da ayyukan taimakon al'umma, musamman marayu da masu karamin karfi, domin su san cewa an kula da su.
Ya yi fatan cewa al'umma zasu cigaba da taya shi addu'a akan Allah SWT ya kara bashi kwarin guiwar cigaba da taimakon mabukata.