26/06/2023
KADA KAYI BAKINCIKI A RAYUWA.
Meyasa zakayi bakinciki, alhalin tsakanin kowace dakika zata iya zama yayewar damuwa daga ubangijin sammai?
Meyasa zakayi bakinciki, arzikikinka Allah T yariga ya rubuta shi, shekarunka a duniya an kididdige su.
Me yasa zakayi bakinciki, alhalin ubangijinka yafi tausayinka fiyeda tausayin dake tsakanin uwa da danta.
Me yasa zakayi bakinciki, alhalin Idan kayi istigfari ubangijinka sai ya azurtaka kuma damuwoyi duk su tafi.
Meyasa zakayi bakinciki, alhalin ubangijinka idan yaso wani Abu sai yace mai kasance sai ya kasance.
Meyasa zakayi bakinciki, alhalin yardarka ga ubangijinka batada makamanciya.
Meyasa zakayi bakinciki, alhalin himma da murmushi yafi bakinciki kyau sosai.
Idan zuciyarka ta karaya yi sujjada ga ubangijinka kace ya mai Dora zukata doramin, idan rayuwarka tayi duhu yi sujjada kace ya ubangiji kabani nasarar rayuwa da haskenta.
Ya Allah kasa mudace ka yaye mana bakinciki da damuwa.