03/06/2025
Zakarun musabaƙar Kur'ani da Sanata Lado ya shirya a Kano sun samu kyautar gidaje da Umrah da kuɗaɗe
Ahmad Shuaibu, wanda ya wakilci ƙaramar hukumar Shanono a musabaƙar Kur'ani da Sanata Bashir Garba Lado ya shirya a jihar Kano ya lashe gasar a izifi 60.
Shuaibu ya samu kyautar gida da kujerar Umrah da kudi Naira miliyan 1 da kuma tallafin karatu daga gwamnatin Qatar har zuwa jami'a da kuma sauran kyaututtuka.
Itama Maryam Abubakar Muazu, wacce ta wakilci ƙaramar hukumar Dala ta kuma samu nasara s izifi 60, ta samu irin wannan kyauta.
Sauran wadanda su ka zo na 2 da na 3 a duk rukunan gasar su ma sun samu kyaututtuka da dama da su ka hada da babura mai kafa uku da mai kafa biyu da kudade da shaddoji da ayamfuna da tallafi karatu da sauran su.
Da ya ke jawabi a yayin rabon kyautukan, Lado, wanda aka fi sani da Ladon Alheri ya yi kira ga iyayen waɗanda su ka lashe gasar da su tabbata an yi amfani da kyaututtukan ta inda ya dace.
Ya ce ya shirya musabaƙar ne domin tunawa da irin aiyukan alheri da mahaifiyar shugaban kasa, Hajiya Abibat Mogaji Tinubu ta yi kafin rasuwar ta.
A cewar Lado, an shirya musabaƙar ne duba da muhimmancin karanta Kur'ani da don ladan da ake samu wajen karanta shi, inda ya kara da cewa an biyawa zakarun Umrah ne domin su kara samun tsoron Allah da kyawun zuciya.
DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa an kwashe tsawon wata daya ana fafatawa a musabaƙar.