01/10/2025
Bai Kamata A Yi Sulhu Da Ƴanbindiga Ba Tare Da Sun Miƙa Makamansu Ba, Cewar Jagora Mustapha Inuwa
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD, Katsina
Jagoran adawa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa, ya bayyana damuwarsa kan tsarin sulhu da ’yan ta’adda ba tare da an karɓi muggan makaman da ke hannun su ba.
Ya ce hakan na barazana ga zaman lafiyar al’umma duba da irin ayyukan ta’addanci da suke ci gaba da yi, ciki har da kisan mutane, garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, satar dabbobi da kuma ƙona kadarorin gwamnati da na jama’a a cewar Mustapha Inuwa.
A wata hira da manema labarai a Katsina,Inuwa ya ce sulhun ba zai amfani ga al’umma ba idan har ’yan ta’addan s**a ci gaba da riƙe makaman su tare da bautar da talakawa ta hanyar tilasta su yin noma ko wasu ayyuka.
Ya bayyana cewa wajibi ne gwamnati ta tabbatar da gaskiya da amanar sulhu ta hanyar karɓar dukkan makaman tubabbun ’yan bindigar domin tabbatar da ingantaccen tsaro.
Mustapha Inuwa wanda tsohon sakataren gwamnatin jihar,ya kuma ƙalubalanci gwamnatin Katsina kan ikirarin da ta yi na “inganta tsaro”, alhali rahotanni na ci gaba da nuni da hare-hare a wasu yankuna na jihar.
Ya yi zargin cewa wasu bayanai da gwamnati ta taɓa fitarwa cewa an yi nasarar kashe ’yan ta’adda 300 a ƙaramar hukumar Ɗanmusa, ba gaskiya ba ne.
Haka zalika, madugun adawar ya yi kakkausan martani kan yadda “ake kashe kuɗaɗen jama’a wajen gyaran tituna a cikin birnin Katsina, madadin a mai da hankali kan ɓangarorin ilimi, lafiya da tsaro.” Ya ce kashe kuɗi a kan waɗannan fannonin su ne ke da matuƙar amfani ga talakawa musamman a ƙauyuka.
Mustapha Inuwa ya kuma bayyana cewa ƙoƙarinsa na yin maganganu kan matsalolin da al’umma ke fuskanta, ba wani salo ne na shirye-shiryen siyasar 2027 kamar yadda wasu ke zargi ba, illa dai kishin jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya. Ya ƙara da cewa yana da alhakin fitar da damuwar jama’a, tare da shawartar gwamnati kan matsalolin da ka iya zama barazana ga rayuwar al’umma, don tabbatar da samun ci gaba da zaman lafiya a jihar da ƙasa baki ɗaya.
A wasu ƙananan hukumomi da su kai zaman sasanci an hango yan ta’addan ɗauke da makaman su a lokacin da ake zaman sasanci.
Majiya: Blueprint Manhaja