10/06/2022
MU NA NAN A APC...
Daga Lawal Hudu Dandume.
Kasan wani baida gadonka amma yana da gadon maganar ka, cece-kuce yayi yawa akan batun wai Baba Hon Haruna Goma ɗan majalisar mu mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɗandume karo na biyu kuma shugaban kwamitin muhallin jihar Katsina ya bar Jam'iyyar APC...
Wannan labari ne mara tushe kuma shaci faɗi da wasu waɗanda suke ganin in sune a matsayin shi to haka zasuyi, niko nasan in har Baba ya bar APC to Insha Allah bana tunanin zan wuce mutum goma na farko da zasu fara sani....
Koda ma mukayi magana da Baba Hon Haruna Goma sai ya kashe mun jiki da cewa " Karka manta fa munyi takara a 2015 mukayi nasara, muka nemi tazarce 2019 mukayi nasara, muka ɗaga hannun Alh Yahaya Nuhu Mahuta shima yayi nasara, muka nemi kujerar reps Allah ya bawa waninmu, to kenan in muka bar Jam'iyyar me muke nufi kenan? Shin Ubangijin dake badawa a APC kenan bashi bane a sauran jam'iyyun? Kenan mun munanawa Allah zato cewa sai a wani wuri zai bamu, ba zamuyi haka ba" Inji Baba....
Muna nan daram a APC damu aka ƙirƙireta kuma asalima nina fara cin gajiyarta a duk faɗin ƙaramar hukumar Ɗandume don kuwa ni na fara cin zaɓen fidda gwani a cikinta gaba ɗaya...
Ba kuma zamu zama irin wasu da s**a bar tasu jam'iyyar s**a dawo wata ba saboda rasa mulki cikin yan satittika ba kamar yadda ya faru a baya..
"Sai dai ba dalilin da baka nememu a hidimarka ba mu shiga ko mu tura yaranmu su shiga wannan kam ba dalili"...
"Kuma ma a halin da muke ciki ya kamata ne duk mai takara a APC ya himmatu wurin neman hanyar nasarar jam'iyyar ba wai cin zarafin wanda kayi takara tare dasu ba"..
"Akwai matakai da yawa da zamu taimaki APC a matsayinta na jam'iyyar mu wanda yasha banban da irin taimakon da ɗan takara kuma zai iya samu, don munyi gogewar rarrabe su a ma'auni na siyasa".. Inji Baba..
"Duk bamu san me Allah zaiyi gobe ba amma dai maganar barin APC ba gaskiya bane kuma muna cikinta kuma muna tare da waɗanda s**a ga cewa muna da muhimmiyar rawa da gudummawar da zamu basu ba cin mutumci ko cin zarafi ko habaici ko yafice ko muzgune b***e kuma zagi da ƙazafi"...
Allah ya tabbatar mana da dukkan alkhairi ya kuma ƙara dauwamar mana da zaman lafiya a dukkan ƙasarmu da sauran ƙasashen Musulmi Amen.