18/11/2025
Wata soja ta yi wuf da Sanata Kawu Sumaila
Sanatan mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya auri Aisha Isah, wata jami’ar soja da ke aiki a rundunar Sojin Saman Najeriya.
Daily Trust ta rawaito cewa an ɗaura auren ne a fadar Sarkin Rano da ke Jihar Kano a jiya Litinin da safe.
Mataimaki na musamman ga Kawu Sumaila kan yada labarai, Muttaqa Babire, ya tabbatar da wannan labari a wani rubutu da ya wallafa a Facebook, inda ya wallafa hoton sanatan tare da amaryarsa wacce ke sanye da kayan soji.
Shi ma wani mataimaki nasa, Ahmad Tijjani Salisu Kiru, ya wallafa: “JUST IN: Alhamdulillah, yau 17-11-2025, Sanata S.A. Kawu Sumaila OFR PhD ya ɗaura aure a Rano. Allah ya albarkaci wannan aure ya bada zuriya ta gari.”
Babu wata sanarwa a bayyane kafin auren, kuma hotunan daga wurin sun nuna cewa ba a yi gaiya wajen daura auren ba.