02/01/2026
Sojoji sun dakile yunkurin ‘yan bindiga na shiga yankunan Shanono a Kano
Sojojin rundunar haɗin gwiwa (JTF) sun yi nasarar dakile yunkurin ‘yanbindiga na kutsawa wasu yankuna a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano bayan musayar wuta mai tsawo.
Lamarin, wanda ya fara da tsakar daren Alhamis har zuwa safiyar Juma’a, ya auku ne a Yankwada, Babanduhu da wasu ƙauyuka makwabta a yankin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), kakakin rundunar Sojin Najeriya a Kano, Manjo Zubair Babatunde, ya ce ‘yanbindigar sun yi ƙoƙarin shiga yankunan ne a kan babura suna harbe-harbe.
Babatunde ya ce harin ramuwar gayya ne bayan da wasu daga cikin ‘yan bindigar s**a rasa rayukansu sakamakon bude wutar da sojoji s**a yi musua wata arangama da aka yi makon da ya gabata.
A cewarsa, maharan sun kutsa ƙauyukan da abin ya shafa da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lamarin da ya sa sojoji s**a gaggauta mayar da martani.
“An yi artabu da ‘yan bindigar yadda ya kamata kuma sojoji sun kore su,” in ji shi.
Babatunde ya ƙara da cewa saurin shigar JTF ya hana asarar rayuka da dukiya a yankunan da abin ya shafa.
Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa sojoji za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, tare da roƙon su su ci gaba da ba jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci.
Kakakin rundunar ya ce sojoji na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana domin hana duk wani sabon hari da kuma tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.