11/10/2025
DOLE MU YI JINJINA GA KUNGIYAR KIRISTOCI (CAN)
A lokacin da aka gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya a kasar Amurka, an shirya wani kallon makirci da ake son yi wa Najeriya. Allah ya tsare mu daga wannan shirin.
Wani daga cikin 'yan majalisar Amurka, Bill Maher, ya yi wata hira a gidan jarida inda ya yi ikirarin cewa daga shekarar 2019 zuwa 2025, an kas£e kiristoci 200,000 kuma an rushe coci sama da dubu ashirin a Arewa maso Najeriya.
Amma wannan magana ba gaskiya ba ce. Kiristocin Najeriya sun fito sun karyata wannan zancen na Bill Maher, suna bayyana cewa ba wai kiristoci kawai ake kashewa a Najeriya ba. Duk wani ta’addanci da ake yi, ba ya la’akari da addini, domin masu aikata ta’addanci ba su da bambanci tsakanin musulmi da kirista.
Damu musulmi da kiristoci, mu gane cewa wannan irin magana na da makarkashiya, ana yinsa ne don a tada rikici tsakanin al’umma. Har ila yau, wannan zancen na Bill Maher ya zo ne a lokacin da Najeriya ke nuna goyon baya sosai ga kafa Kasar Palestine don 'yancinsu.
Saboda goyon bayan Najeriya ga Palestine, wasu kasashen ke kokarin bata sunan Najeriya a idon duniya, kuma wannan shi ne dalilin wannan karya da ake yadawa.
A irin wannan lokaci, dole ne mu jinjina wa Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) saboda yadda ta tsaya tsayin daka wajen kare martabar Najeriya da fadin gaskiya a duniya. CAN ta bayyana cewa zaman lafiya da hadin kai tsakanin addinai ya zama wajibi domin cigaban kasar mu.
Mu ci gaba da hada kai, mu kyautata zamantakewa, mu guji yada labaran karya da za su raba mu, domin Najeriya ta dore cikin zaman lafiya da cigaba.