22/07/2025
2027: Babu wata gamayyar siyasa da za ta iya kada Tinubu - Gwamnan Ebonyi
Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayyana cewa babu wata gamayyar siyasa da za ta iya kada Bola Tinubu a zaben 2027.
Ya bukaci 'yan adawa da masu neman takara su hakura da buri, su kuma goyon bayan gwamnatin da ke ci yanzu.
Da ya ke jawabi a taron shugabannin jam’iyyar APC na Kudu maso Gabas da aka gudanar a Abakaliki, Gwamna Nwifuru ya ce fitowar Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023 nufin Allah ne ba nufin dan Adam ba, kuma ya jaddada cewa babu wani kawance ko hadakar ‘yan adawa da za ta iya hana nasarar Tinubu a 2027.
Ya yabawa Tinubu bisa sauye-sauyen tattalin arzikin da ya ke yi, inda ya bayyana shi a matsayin jarumin shugaba mai karfin zuciya da iya yanke shawara mai tsauri domin farfado da kasa. Nwifuru ya roki ‘yan Najeriya, musamman ‘yan Kudu maso Gabas, da su ci gaba da hakuri tare da mara wa shugaban kasa baya.