23/04/2025
Gwamna Raɗɗa Ya Ƙaddamar Da Manufofin Jihar Katsina Akan Sauyin Yanayi
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD, ya ƙaddamar da manufofin da za su kai jihar Katsina tudun mun tsira akan abun da ya shafi sauyin yanayi a ranar Laraba 23/04/2025, taron ya wakana a ɗakin taro na masaukin baƙin Transcorp Hilton da ke birnin tarayya Abuja.
An bayyana manufofin ne a lokacin taron ƙaddamar da lalubo hanyoyin da zasu samar da muhalli mai kyau a jihar Katsina wanda aka yi ma suna "Katsina State Green Growth Agenda (KAGGA)" wanda ke da manufar samar da tsirrai da nufin daƙile matsalar sauyin yanayi.
A lokacin da yake jawabin ƙaddamar da shirin Gwamna Raɗɗa ya ce akwai matsalolin sauyin yanayi da dama da ke tunkarar jihar Katsina, inda kaso 80% cikin ɗari na mutanen jihar sun dogara ne da noman damuna kawai, duk da barazanar kwararowar hamada, ƙarancin ruwan damuna, da kuma yanayi mai zafi da jihar ke fama da shi.
" Wan nan sauyin yanayin zai haifar da ƙarancin kayan gona, raguwar halittu, ƙarancin albarkatun ƙasa, tare da haifar da rashin tabbas ga matasan mu wajen hijira domin neman mafaka.
Da yake magana akan yadda za'a magance matsalar sauyin yanayi, Gwamna Raɗɗa yace sun yi shiri wanda zai wadatar da ruwa a jihar Katsina.
" Mun fahimci cewa wadatar da ruwa kamar magance matsalar sauyin yanayi ne, Inji Gwamnan, shiyasa kuma muka samar da hukumar noman rani wadda ta samar da famfunan ban ruwa masu amfani da hasken rana 4,000, tare da rijioyin ban ruwa 204, mun kashe Naira Biliyan ₦10.8 domin gina madatsar ruwa a Dam ɗin Jibia, an kashe Naira Biliyan ₦11.2 domin samar da manyan hanyoyin ruwa a cikin garin Katsina, haka kuma gwamnatin mu ta kashe Naira Biliyan ₦2.4 domin samar da famfuna masu amfani da hasken rana 120, tare da wasu guda 60 da ake tsaka da ginawa.
Haka kuma Gwamnan ya bayyana irin ƙoƙarin da ya yi a fannin noma inda yace ya samar da taraktoci 38, tare da samar da taraktocin na hannu 320, wanda kuɗin su ya kai Naira Biliyan Uku, tare da samar da hektocin noma 1,115, kuma gwamnati ta yi yarjejeniya da kamfanin Genesis ta Miliyan $500 domin samar da lantarki mai amfani da hasken rana a gidan Gwamnati da Babban asibitin Katsina.
Sannan kuma an koyar da mata da matasa sama da 5000, dabarun noman zamani mai suna "Waste-to-wealth".
Babban muhimmancin ƙaddamar da wannan shiri na manufofin jihar Katsina akan sauyin yanayi (KAGGA), shine domin samo hanyar da zata bunƙasa da kare rayuwar halittun dabbobi da tsirrai.
Wannan shirin manufofin kuma yana da ginshiƙai guda huɗu da s**a haɗa da samar da tsarin noma na zamani, shugabanci a ɓangaren samar da makamashi na zamani, dawo da martabar tsarin muhalli, da kuma wadatar da tsirrai ko dashen Itatuwa.
Domin samun nasarar aiwatar da wannan shiri, Gwamna Raɗɗa yace za'ayi doka akan manufofin sauyin yanayin cikin watanni 12, tare da ware kaso 30% na kasafin kuɗin jihar akan kawo ƙarshen matsalar sauyin yanayi, haka kuma za'a samar da asusun kuɗin kula da sauyin yanayi wanda yanzu haka an saka mashi Naira Biliyan ₦5.
Gwamna Raɗɗa ya kuma yi amfani da damar wajen gayyato masu saka hannun jari domin kawo masu saka makamashi na zamani masu amfani da hasken rana domin inganta noma da rainon tsirrai a jihar Katsina.
"A cikin shirin sauyin yanayida za'a kawo, gwamnati zata riƙa horar da mata da matasa 15,000 duk shekara, akan bunƙasa tsirrai, kuma arzikin da za'a samu wajen zai samar da aikin yi ga sama da mutane 50,000 a jihar Katsina zuwa shekarar 2030. Inji Gwamna Raɗɗa
Tun da fari a jawabin shi na maraba Kwamishinan Muhalli na jihar Katsina Hon. Hamza Sulaiman Faskari, ya bayyana cewa taron na da nufin lalubo hanyoyin da zasu kawo chanji akan matsalar sauyin yanayi, tare da bayyana irin yadda za'a bunƙasa rayuwar tsirrai da dabbobi a jihar Katsina.
Shima a nashi jawabin Ministan Muhalli Hon. Balarabe Abbas Lawal, ya yaba ma gwamnatin jihar Katsina, akan kawo wannan shirin na (KAGGA) tare da samar da majalissar kula da sauyin yanayi ta jiha, wanda ya bayyana hakan zasu taimaka ma jihar wajen magance matsalar sauyin yanayi.
A nashi ɓangaren Ministan gidaje da raya birane Arc Ahmad Musa Dangiwa, ya bayyana cewa ma'aikatar shi tana yin tsare-tsaren gini wanda zasu taimaka wajen kauce ma matsalar sauyin yanayi.
Kakakin majalissar wakillai Rt.Hon Tajuddeen Abbas, ya yaba ma ƙoƙarin gwamnatin jihar Katsina wajen magance matsalar sauyin yanayi musamman ƙoƙarin ta wajen kawo sauyi domin amfani da makamashi na zamani.
Hon. Sada Soli Jibia, a madadin ƴan majalissar tarayya 15 na jihar Katsina, yace a shirye suke domin goya ma gwamnatin Jihar Katsina baya wajen cimma ƙudurin ta na yaƙi da sauyin yanayi.
Sauran wanda s**a yi magana a wurin akwai Ministan al'adu Hannatu Musawa, wakilin tarayyar turai a Najeriya Mista Beatrice Eyong, Mataimakin sakataren majalisar ɗinkin duniya Mohammed M. Malick Fall, Jakadan ƙasar Misrah a Najeriya Mohammed Foud, da sauran su..