DDR News

DDR News WANNAN SHAFI ANYISHINE DOMIN KAWO MAKU LABARAI DA AL'AMURUKAN YAU DA GOBE

Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar katsina tayi Allah wadai da cin zarafin da Jami'an KASSAROTA keyima Al'ummar jih...
07/04/2025

Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar katsina tayi Allah wadai da cin zarafin da Jami'an KASSAROTA keyima Al'ummar jihar katsina wajen karbe masu ababen hawa ba bisa ƙa'ida ba

Kungiyar tace doka bata ba jami'an na KASSAROTA damar k**a kowa ba ballantana su sanyama wani ɗan kasa tara mai yawa ba

Hakazalika ƙungiyar ta lauyoyin karkashin jagorancin shugabanta na jihar katsina Barr. Shafi'u Umar tayi kira ga gwamnatin jihar katsina da tayi kokarin dakatar da faruwar hakan don gudan tada hankalin jama'a.
𝑭𝒐𝒍𝒍𝒐𝒘𝒆𝒓𝒔.
KATSINA OKATSINA ONLINEr

Shugaban ƙasar Burkina Faso, Ibrahim Traore, yace" Nahiyar Afirka bata buƙatar bankin duniya (World Bank), asusun bada l...
12/01/2025

Shugaban ƙasar Burkina Faso, Ibrahim Traore, yace" Nahiyar Afirka bata buƙatar bankin duniya (World Bank), asusun bada lamuni na majalisar ɗinkin duniya (IMF), nahiyar Turai ko Amurka, kafin nahiyar ta cigaba.

Ya ce a Afirka ana da duk abinda ake buƙata domin a ƙarfafi tattalin arziki ba tare da cin bashi ba.

"Ba zamu taba bari ana mana mulkin mallaka na zamani ta hanyar bamu bashi daga bankin duniya, IMF ko nahiyar Turai ba." Ina ji Traore

06/01/2025
Bayyana Kyautar Motar Da Yara 'Yan Matan Nan Suke Yì, Ya Fi Illa Fiye Da Àbìnda Suke Zuwa Yi Ake Ba Su MotarNi Wallahi y...
06/01/2025

Bayyana Kyautar Motar Da Yara 'Yan Matan Nan Suke Yì, Ya Fi Illa Fiye Da Àbìnda Suke Zuwa Yi Ake Ba Su Motar

Ni Wallahi yaran nan da ake bawa mota fitowa da suke yi suna nunawa ya fi illa akan abinda suke zuwa ýi ake ba su.

Yanzu sun yi influencing yara kanana na ťìķțok har ya kai ga burin yarinya kawai ta yi ìşķançì a ba ta kudi, yara sun fara fandarewa.

In an basu suyi hakuri su daina zuwa suna posting don yadawa duniya.

Ku kuma 'yan mata da kuke kallon wadanda ake bawa gida da mota as role model har suke burge ku ku sani ba haka kawai ake ba su kudin ba, wani abun ya wuce kudin da saurayi zai bawa budurwa sabida soyayya ko sabida ya yi źìñà da ita, yawanci kudin ķùñģiya ce, bayan wasu shekaru za a a nemi wadanan dukiyar a rasa ka zama abun tausayi.

Zan iya misalai da 'yan fim dayawa wadnda ma s**a tare kasar waje s**a yi suna, s**a yi kudi amma karshen su yanzu bai yi kyau ba.

Ku zauna inda Allah ya ajiye ku ku ci kudinku na halal, suna zuwa social media ne suna fada an basu don su sami karin mutane da za su tagayyara tare.

Don Allah don Annabi ku yi hakuri da talaucin ku, ku kare mutuncinku da na iyayenku.

Jamila Ibrahim

Yayin gabatar da kasafin kuɗi, Tinubu ya faɗawa ƴan majalisa cewa duk za su lashe zaɓen su a 2027Shugaban kasa Bola Ahme...
19/12/2024

Yayin gabatar da kasafin kuɗi, Tinubu ya faɗawa ƴan majalisa cewa duk za su lashe zaɓen su a 2027

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba ya yi barkwanci inda ya ce ‘yan majalisar dattawa ta 10 sun “sake cin zaɓe.”

VANGUARD ta rawaito cewa hakan ya faru ne lokacin da shugaban ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 ga taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Tinubu ya yi wannan furuci ne bayan ya yi kuskure wajen kiran majalisar dattawa ta 10 da sunan ta 11.

Ya yi wannan barkwanci ne bayan wasu daga cikin ‘yan majalisar sun gyara shi, k**ar yadda aka gani a wani bidiyo da ya bazu wanda ke da tsawon minti ɗaya da dakika 14.

"Domin cika ɗaya daga cikin hakkokina na doka tare da jajircewa wajen sake gina Najeriya da tabbatar da mun tsaya tsayin daka a tafiya mai zuwa ta samar da makoma mai albarka, na gabatar da kasafin kudin 2025 ga taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta 11,” in ji Tinubu.

Bayan wannan, ‘yan majalisar sun tuna wa Shugaban cewa su ne Majalisar Dokoki ta 10.

“Ta 10? Na rubuta ta 11, wanda ke nufin kun sake cin zaɓe gaba ɗaya,” Shugaban ya amsa da dariya.

Gwamnatin Legas ta k**a almajirai 27 Jami’an kwamitin ko-ta-kwana na ma'aikatar muhalli ta jihar Legas sun k**a wasu mut...
19/12/2024

Gwamnatin Legas ta k**a almajirai 27

Jami’an kwamitin ko-ta-kwana na ma'aikatar muhalli ta jihar Legas sun k**a wasu mutane 27 da ake zargi da aikata barace-barace a tituna.

Kwamishinan Muhalli da Ruwa na Jihar, Mista Tokunbo Wahab ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X , a jiya Laraba, inda ya ce hukumar ta gudanar da aikin ne a ranar Talata.

"An k**a mutane 27, da s**a hada da yara kanana 15, wadanda ke yin barace-barace a kan tituna ba bisa ka'ida ba, a tsakiyar zirga-zirgar ababen hawa,".

A cewar kwamishinan, duk wadanda ake tuhuma za a mika su zuwa ma'aikatun da s**a dace na gwamnati k**ar yadda doka ta tanada.

Yi Following Din Dan Uwanka Shi Ma Ya Yi Follow Back Dinka Domin Ku Taimaki Juna Saboda A Shekarar 2025 Facebook Za Su F...
19/12/2024

Yi Following Din Dan Uwanka Shi Ma Ya Yi Follow Back Dinka Domin Ku Taimaki Juna Saboda A Shekarar 2025 Facebook Za Su Fara Biyan Masu Followers Sama Da Dubu Goma A Nijeriya

Samun 10K followers kafin January abu ne mai matukar wahala, amma idan kuka cire hassada kuka yi following din juna ina da yakinin da yawa daga cikinku za su haura fiye da 10k followers.

Please a duba comments domin following din mutanen arziki. Duk wanda ya yi following dinka Don Allah kai ma ka daure ka yi "Follow Back".

Duk wanda ba ma following din shi please yanyi comments In Sha Allahu za mu yi following dinshi, sannan don Allah duk wanda ka ga comments din shi ka yi following dinshi, shi ma yayi "following back" ku taru ku taimaki juna, an ce a shekarar 2025 Facebook za su fara biyan 'yan Nijeriya da suke da fiye da 10k Followers.

Mun bada wannan damar a shafinmu domin mabiyanmu su amfana.

Sannana ku yada (sharing) domin sauran jama'a su gani. Kada kuma ku manta idan ba ka following Rariya za ka iya yi yanzu.

Wannan shine shahararren mai Da'awah kuma babban malamin Addinin Musulunci a Africa Sheikh Muhammadu Sabihu Gwammaja.She...
19/12/2024

Wannan shine shahararren mai Da'awah kuma babban malamin Addinin Musulunci a Africa Sheikh Muhammadu Sabihu Gwammaja.

Shehin malamin ya karar da rayuwar sa wurin wa'azantar da al'ummar musulmai da tsoratar da al'umma azabar da Allah zaima wanda ya saba masa a lahira tare da zamantakewar sure.

Yayi rayuwa a tsakanin jihar Kano da Borno, da wasu jihohin arewacin Najeriya. Kafin rasuwar sa ya hadu da makiya wurin wa'azin sa.

Allah ubangiji madaukakin sarki ya jikan sa da rahma ya yafe masa kura-kuran sa. Amiin

Daga: Babangida A. Maina
Tijjaniyya Media News

Abdul Samad Rabiu (BUA) ya narka biliyoyin Naira a sake gina babban masallacin Juma'a na garin Zariya - Duba rahoton gin...
18/12/2024

Abdul Samad Rabiu (BUA) ya narka biliyoyin Naira a sake gina babban masallacin Juma'a na garin Zariya - Duba rahoton ginin a sashen sharhi.

Hoto: Uba Sani (Facebook)

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kora Engr. Babachir David Lawal, kenan, y...
03/12/2023

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kora Engr. Babachir David Lawal, kenan, yayin da yake gabzan Kosai da lemon roba (5alive) a gonarsa.

📸: Babachir Lawal| Facebook

BARKWANCI: idan Kaine headmastern ya zakaryi©DDR News
03/12/2023

BARKWANCI: idan Kaine headmastern ya zakaryi

©DDR News

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DDR News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share