31/01/2023
KAKAKIN MAJALISAR DOKOKIN JAHAR KATSINA YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA
....Saura kiris a tsige shi
Mu'azu Hassan
@ Katsina City News
Jaridun Katsina City News, sun tabbatar da labarin cewa saura kiris da an tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Alhaji Musa Tasi'u Maigari.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa, masu yunkurin sun fara shirinsu ne tun ranar Litinin 23/1/2023. Kuma har sun samu amincewa da sa hannun 'yan Majalisar Jihar 18.
Majiyarmu ta ce ya zuwa ranar Juma'a 28/1/2023, masu yunkurin suna da cikakken goyon bayan mafi yawan 'yan Majalisar da za su tsige Kakakin nasu.
Majiyarmu ta ce wani dan Majalisa daga shiyyar Funtua ne ya jagoranci karya lagon shirin, inda ya k**a daki a wani sabon katafaren otal da ke nan cikin birnin Katsina inda ya yi aikin wargaza shirin.
Daga wannan otal aka samu sa hannun 'yan Majalisa tara wadanda s**a fitar da hannunsu daga shirin.
Babban Editan jaridun Katsina City News ya ga takardu biyu na sa hannun farko na kudurin tsige Kakakin Majalisar da kuma wanda 'yan Majalisa tara s**a sanya wa hannu da ba su yarda da tsigewar ba.
Majiyarmu ta ce wani dan Majalisa daga shiyyar Funtua, kuma na kusa da Kakakin Majalisar shi ne ya jagoranci wannan yunkurin.
Matsalar da ya samu ita ce, ya nemi in yunkurin ya yi nasara shi ya zama Kakakin Majalisar na sauran watannin da s**a rage.
Wani dan Majalisa daga shiyyar Daura ya tabbatar wa da jaridunmu cewa, daya daga cikin dalilan da s**a sanya shirin ya kasa nasara shi ne, kudirin dauke kujerar Kakakin Majalisar daga shiyyar Daura ta koma shiyyar Funtua na sauran watannin da s**a rage.
Masu yunkurin sun zargi Kakakin Majalisar da son kansa da kin taimakon su lokacin zaben fitar da gwanin 'yan takarar da aka yi.
Da kuma cewa maganar kudi shi kadai yake amfana, yayin da su kuma ya bar su cikin wahala har gwamnatin ta zo karshe.
Wata majiya ta ce hatta Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari CFR sai da ya sa baki wajen ceto kujerar Kakakin Majalisar.
Zaman jiya 30/1/2023 aka so a tabbatar da juyin mulkin, amma bai yi nasara ba.
Duk da majiyarmu tamu ta ce ya zuwa yanzu komai ya daidaita a Majalisar, amma daya daga cikin masu shirin ya ce sun sa ido idan Kakakin ya canza, to magana ta wuce, amma idan ya ki canzawa za su canza salo.