11/08/2026
FCE Katsina Ta Rantsar Da Sababbin Shuwagabannin Daliban Kwalejin (SRC)
Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Katsina, ta rantsar da sabbin Shuwqgabannin Majalisar Wakilan Dalibai (SRC) da aka zaba a kwalejin.
An rantsar da sabbin shugabannin SRC tare da shugabannin kwamitocin dalibai daban-daban a wani biki da aka gudanar a babban dakin taro na kwalejin.
Taron rantsarwar ya samu halartar manyan jami’an gudanarwar kwalejin, Shugabannin Kwalejoji, Shugabannin Sassan karatu, ma’aikata, dalibai da kuma ’yan uwa da abokan arzikin sabbin shugabannin da aka rantsar.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwalejin, Dr. Ahmad Tijjani Ibrahim, ya taya sabbin shugabannin murna bisa samun damar jagorantar dalibai, tare da samun damar yi musu hidima.
Dr. Ahmad Tijjani Ibrahim ya tunatar da sabbin shugabannin irin nauyin da ke kansu da kuma kalubalen da ke gabansu, inda ya bukace su da su gudanar da ayyukansu cikin jajircewa, da’a da kuma kishin alhaki.
Ya kuma tabbatar wa daliban cewa, gwamnatin kwalejin za ta ci gaba da jajircewa wajen inganta jin dadin dalibai da kuma samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar samun ingantaccen ilimi.
A nata jawabin, Shugabar Sashen Kula da Jin Dadin Dalibai ta bayyana cewa, sabuwar Majalisar Wakilan Daliban ta kunshi daliban NCE da kuma daliban karatun digiri.
Ta ce an zabo jami’an ne bisa cancanta da kuma la’akari da kwarewarsu wajen wakiltar muradun dalibai yadda ya kamata.
A cikin jawabinsa na godiya bayan rantsar da shi, sabon Shugaban Majalisar Wakilan Dalibai, Comrade Kamaladeen, ya tabbatar wa dalibai cewa gwamnatinsa za ta gudanar da mulki bisa tsarin bude kofa ga kowa.
Ya kuma yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da sauran mambobin majalisar da kuma masu ruwa da tsaki, domin cimma manufofin da majalisar ta sanya a gaba.
Comrade Kamaladeen ya nuna godiyarsa ga mahukuntan Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Katsina, bisa damar da s**a ba su na yi wa dalibai hidima, inda ya yi alkawarin tabbatar da cewa ya cancanci amincewar da aka ba shi.