Kadarko TV

Kadarko TV Gaskiya da Amana Shine Jarin Mu

Kadarko TV kafar yada labarai da aka kafa domin samar da ingattatu

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da dala biliyan 1 domin tallafa wa marasa ƙarfiGwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin H...
27/08/2026

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da dala biliyan 1 domin tallafa wa marasa ƙarfi

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin HOPE-SP na dala biliyan 1 domin agaza wa marasa ƙarfi a ƙasar, inda ta ce shirin zai sauya yanayin tallafin da ake yi zuwa na ɓullo da hanyoyin dogaro da kai.

Shirin mai suna Household Prosperity and Economic Social Protection Project (HOPE-SP), an ƙiyasta zai ci dala biliyan 1, a wani mataki da ke nuna sauyin tsarin tallafin jinƙai daga bayar da tallafi na ɗan lokaci zuwa samar da hanyoyi da gwamnatin ta ce masu ɗorewa da za su taimaka wa jama’a su fita daga talauci.

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta ƙaddamar da shirin a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ta yaba wa ministan harkokin jinƙai da rage talauci, Dr. Bernard Doro, da tawagarsa bisa ƙoƙarin da suke yi.

An tsara sauye-sauyen ne domin inganta yadda ake gano da tantance gidajen da ke cikin buƙata, da kuma tabbatar da cewa tallafi ya isa ga waɗanda s**a fi cancanta. Haka kuma, za su ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shirye-shiryen jinƙai da na rage talauci, tare da samar da tallafin gaggawa yayin fuskantar matsaloli da kuma ƙara gaskiya da riƙon amana.

Ministan ya ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan shirin shi ne One Humanitarian, One Poverty Response System (OHOPRS), wanda zai haɗa shirye-shiryen agaji, zamantakewa da rage talauci cikin tsari guda na ƙasa.

"Tsarin zai yi amfani da rajista guda, hanyoyin isar da tallafi na zamani, ingantaccen tsarin kuɗaɗe da bayanan sirri na zamani domin yanke shawara cikin gaggawa."

Babban Sakatare na Ma’aikatar, Olubunmi Olusanya, ya ce sauye-sauyen za su ƙarfafa haɗin gwiwa da riƙon amana, yana mai jaddada cewa babban ma’aunin nasara shi ne ganin sauyi na zahiri a rayuwar ‘yan Najeriya masu buƙata. Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, da abokan hulɗar kamar Tarayyar Turai da Bankin Duniya, sun yaba da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa tsarin ayyukan jin jinƙai a Najeriya.

EFCC za ta ba wanda ya fallasa kuɗin sata da aka ɓoye a ƙasar waje kashi 5Hukumar EFCC ta ce mutanen da s**a bayar da sa...
27/08/2026

EFCC za ta ba wanda ya fallasa kuɗin sata da aka ɓoye a ƙasar waje kashi 5

Hukumar EFCC ta ce mutanen da s**a bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano dukiyar da aka wawure daga Najeriya tare da ɓoyewa a ƙasashen waje, na iya samun lada har zuwa kashi 5 cikin 100 na asalin dukiyar da aka ƙwato.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yi kira ga mutanen da ke da sahihan bayanai kan inda aka boye kuɗaɗe da kadarorin Najeriya a ƙasashen waje da su fito su bayar da bayanan.

Ya yi wannan kiran ne yayin wani taro kan laifukan tattalin arziki da aka gudanar a Cambridge, Ingila, ina ya ce a ƙarƙashin tsarin ladar, mai fallasa bayanai (whistleblower) wanda bayanansa s**a kai ga samun nasarar ƙwato dukiya, na iya samun lada tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 na ƙimar dukiyar da aka ƙwato.

Da yake magana a taron, Olukoyede ya ce ya kamata a ƙara matakan kariya ga mutanen da ke bayar da bayanan da ke taimakawa wajen tona asirin laifukan kuɗi, inda ya nanata cewa kariyar na da muhimmanci, musamman a ƙasar da wasu masu bayar da bayanai ke fargabar ramuwar gayya bayan fallasa mutanen da ke da alaƙa da siyasa ko kuma masu tasiri a ƙasar.

Najeriya ta ƙaddamar da manufar kare masu fallasa bayanai ta gwamnatin tarayya a shekarar 2016, wadda ta tanadi lada ga mutanen da s**a taimaka wajen fallasa almundahana, ɓoye ko karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kadarorinta. Sai dai, duk da alkawarin bayar da lada, an taɓa nuna damuwa cewa wasu masu fallasa bayanai sun shafe lokaci suna jiran biyan kuɗaɗen da aka yi musu alkawari. Haka kuma, babu wata takamaiman doka da ke ba su cikakkiyar kariya.

Sai dai sabuwar sanarwar EFCC kan ladar ta haifar da tambayoyi kan ko hukumomi za su iya tabbatar da sirri, kariya da kuma biyan ladan kamar yadda aka yi alƙawari.

Emir of Daura Turbans Tinubu-Ojo, Hannatu Musawa with Hausa Traditional TitlesThe Emir of Daura, His Royal Highness Alha...
26/08/2026

Emir of Daura Turbans Tinubu-Ojo, Hannatu Musawa with Hausa Traditional Titles

The Emir of Daura, His Royal Highness Alhaji Umar Faruk Umar, has conferred the traditional title of Jakadiyar Kasar Hausa on Mrs. Folashade Tinubu-Ojo, Iyaloja-General of Nigeria and Lagos and daughter of President Bola Ahmed Tinubu.

The Emir also bestowed the title of Mairamar Kasar Hausa on the Minister of Arts, Culture, Tourism and the Creative Economy, Hannatu Musa Musawa.

The colourful ceremony took place at the Emir’s Palace in Daura shortly after the Hawan Magajiya, popularly known as Sallar Gani.

Governor Malam Dikko Umaru Radda attended the historic occasion alongside the Chief of Staff, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir; Principal Private Secretary, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji; and several female traditional title holders who gathered at the palace to witness the occasion.

The titles were conferred in recognition of the recipients’ contributions to society, particularly their efforts in promoting cultural heritage, women’s empowerment and community development.

The conferment further highlighted the enduring cultural traditions of the Daura Emirate and the importance of recognising individuals who contribute to the promotion and preservation of Hausa culture and heritage.

The ceremony attracted top government officials, traditional rulers, dignitaries and other traditional title holders who gathered at the palace to witness the historic occasion.

Gwamna Radda Ya Halarci Hawan Gani a Masarautar DauraGwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya halarci Hawan Ga...
26/08/2026

Gwamna Radda Ya Halarci Hawan Gani a Masarautar Daura

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya halarci Hawan Gani da aka gudanar a Masarautar Daura, wani gagarumin biki na gargajiya da ake gudanarwa duk shekara a matsayin wani bangare na bukukuwan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Hawan Gani na daga cikin muhimman al’adun Masarautar Daura, inda sarakuna, hakimai, dagatai, masu unguwanni da sauran al’umma ke fitowa cikin kayatattun kayan gargajiya domin nuna al’adun masarautar tare da yin murnar wannan rana mai albarka.

Bayan kammala hawan, Gwamna Radda ya taya daukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW), tare da addu’ar Allah Ya ci gaba da ba al’ummar Musulmi zaman lafiya da albarka.

Gwamnan ya kuma jinjinawa Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, bisa irin ƙoƙarin da yake wajen karewa da raya al’adun gargajiya na Masarautar Daura, yana mai addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, ƙarfi da hikimar jagoranci.

Haka nan, Gwamna Radda ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa ba jihohi dama da goyon baya wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar al’umma.

A ƙarshe, Gwamna Radda ya roƙi al’ummar Katsina da ƙasa baki ɗaya da su ci gaba da sanya jihar da ƙasar nan cikin addu’o’insu, domin samun zaman lafiya, ci gaba da wadata.

Sauran wanda s**a halarci taron akwai Ministar Al'adu Barista Hannatu Musawa, Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt.Hon Nasir Yahaya Daura, Ƴar Shugaban ƙasa Mujidat Folashade Iyaloja TinubuShugaban ma'aikatan gidan gwamnati Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, Sakataren gwamnan Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin Masarautu Hon. Usman Abba Jaye, da Sauran su.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

August 26, 2026.

FEDERAL GOVERNMENT UNVEILS ONE BILLION DOLLAR RENEWED HOPE SOCIAL PROTECTION PROGRAMMEAbout 7.6 million Nigerians are se...
26/08/2026

FEDERAL GOVERNMENT UNVEILS ONE BILLION DOLLAR RENEWED HOPE SOCIAL PROTECTION PROGRAMME

About 7.6 million Nigerians are set to benefit from a one-billion-dollar Renewed Hope Social Protection Programme as the Federal Government unveils the Household Prosperity and Empowerment Social Protection Project, HOPE-SP, as a new pathway to poverty reduction in the country.

Nigeria’s First Lady, Oluremi Tinubu, while unveiling the initiative, says the Bola Tinubu administration is implementing far-reaching reforms to lay a solid foundation for sustainable growth and shared prosperity.
State House correspondent, Adeniyi Taiwo, reports that the initiative is designed to strengthen social protection, expand economic opportunities and empower vulnerable households across the country.

NDLEA, CIVIL DEFENCE PLEDGE SUPPORT FOR PEACEFUL  CAMPAIGNS AND 2027 GENERAL ELECTIONSAs political parties commence camp...
26/08/2026

NDLEA, CIVIL DEFENCE PLEDGE SUPPORT FOR PEACEFUL CAMPAIGNS AND 2027 GENERAL ELECTIONS

As political parties commence campaign activities ahead of the 2027 general elections, security agencies across the country are ramping up efforts to ensure peaceful and credible process.

The National Drug Law Enforcement Agency, NDLEA, says it will intensify the crackdown on drug abuse and trafficking during the elections period.

Meanwhile, the Nigeria Police Force, Nigeria Security and Civil Defence Corps, NSCDC, have assured Nigerians of adequate protection of lives and property throughout the campaigns and elections.

Diphtheria ta kashe yara 50 a KanoAƙalla yara 50 ne s**a mutu sakamakon ɓarkewar cutar mashaƙo wato diphtheria a jihar K...
26/08/2026

Diphtheria ta kashe yara 50 a Kano

Aƙalla yara 50 ne s**a mutu sakamakon ɓarkewar cutar mashaƙo wato diphtheria a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, a cewar jami'ai.

Mahukunta a jihar sun ce cutar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi shida, lamarin da ya ƙara haddasa damuwa kan lafiyar al'umma.

Sun buƙaci hukumomin yankunan da abin ya shafa su tura ƙarin ma'aikatan lafiya tare da ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile yaɗuwar cutar, musamman a wuraren da ke da haɗari.

Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ƙwayoyin cuta ke haifarwa, kuma tana iya jawo mummunar rashin lafiya har ma da mutuwa, musamman ga yaran da ba su samu rigakafi ba.

Gwamna Radda Ya Halarci Maulidin Zawiyyar Madinatul Ahbab, Ƙofar Baru DauraGwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda...
25/08/2026

Gwamna Radda Ya Halarci Maulidin Zawiyyar Madinatul Ahbab, Ƙofar Baru Daura

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya halarci Maulidin Annabi Muhammad (SAW) na Zawiyyar Madinatul Ahbab, ƙarƙashin jagorancin Khalifa Sheikh Naziru Kofar Baru, a Daura.

An gudanar da karatun Alƙur’ani mai girma tare da karanta ƙasidu daban-daban. Taron, wanda ke gudana duk shekara sama da shekaru 60 a daren 12 ga Rabi’ul Auwal domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), na samun halartar mutane daga sassa daban-daban na Afirka.

A jawabinsa, Sheikh Kofar Baru ya gode wa Gwamna Radda bisa irin gudummawar da yake bayarwa wajen tallafa wa addinin Musulunci, tare da tabbatar da cewa Zawiyyar za ta ci gaba da ba shi goyon baya.

Shi ma Gwamna Radda ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da bayar da gudummawa wajen ci gaban addinin Musulunci, inda ya sanar da cewa zai gina wa Zawiyyar Madinatul Ahbab gidan baƙi da take buƙata, da kuɗin aljihunsa.

Gwamnan ya kuma roƙi Malaman da su cigaba da saka jihar Katsina cikin addu'o'in su domin samun ingantaccen zaman lafiya a jihar dama ƙasa baki ɗaya.

Cikin wanda sa s**a halarci wurin akwai Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt.Hon Nasir Yahaya Daura, Shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, Kwamishinan Addinai Hon. Ishaq Shehu Dabai, Ɗan takarar Majalisar tarayya na S/D/M Alh. Muhammad Ɗaha Umar Faruk, Sarkin Kurayen Katsina Alhaji Usman Darda'u, Sarkin Arewan Daura, Alh. Mansur Daura, da sauran su.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

August 25, 2026.

MAS'UDU MUSTAPHA BANYE ASSUMES OFFICE AS ACTING HEAD OF KATSINA STATE CIVIL SERVICEThe newly appointed Acting Head of th...
24/08/2026

MAS'UDU MUSTAPHA BANYE ASSUMES OFFICE AS ACTING HEAD OF KATSINA STATE CIVIL SERVICE

The newly appointed Acting Head of the Katsina State Civil Service, Alhaji Mas’udu Mustapha Banye, has formally assumed office.

Alhaji Banye took over on Monday following his appointment by the Executive Governor of Katsina State, His Excellency Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D., CON.

He was received at the Head of Service Office by the Permanent Secretary, Administration, Alhaji Ado Yahaya, alongside other Permanent Secretaries, Directors and top government officials.

Alhaji Banye was accompanied to the office by the management and staff of the Ministry for Local Government and Emirate Affairs, where he previously served as Permanent Secretary.

The appointment, which took immediate effect, is part of the state government’s efforts to strengthen the civil service, enhance professionalism and improve service delivery in line with the administration’s _Building Your Future Agenda_.

In his remarks after assuming duty, Alhaji Banye expressed appreciation to Governor Radda for the confidence reposed in him.
He assured that he would work diligently to justify the trust and contribute meaningfully to the development and transformation of the state civil service.

He also pledged to provide purposeful leadership, uphold professionalism and support reforms aimed at improving efficiency and effective service delivery across Ministries, Departments and Agencies.

Until his appointment, Alhaji Mas’udu Mustapha Banye served as Permanent Secretary, Ministry for Local Government and Emirate Affairs.

Najeriya ta ƙaddamar da yaƙi ta sama kan ƴan fashin dajiRundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta ƙaddamar da wani shirin...
24/08/2026

Najeriya ta ƙaddamar da yaƙi ta sama kan ƴan fashin daji

Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta ƙaddamar da wani shirin yaƙi ta sama a jihohin arewa maso yammacin ƙasar kan “ƴan ta’adda da sauran masu aikata laifuka” da s**a addabi yankin.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta ce yaƙin wanda ta yi wa laƙabi da ‘Hannun ƙarfe’ zai tallafa wa sojojin da ke kai samame ta ƙasa domin dawo da tsaro a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kebbi da kuma Kaduna, inda sojoji ke aiki ƙarƙashin shirin ‘Operation Fansan Yamma’.

“Wannan shiri ya tabbatar da ƙoƙarin dakarun saman Najeriya wajen amfani da dabarun yaƙi ta sama da haɗa hannu da sauran hukumomin tsaro wajen daƙile ayyukan ƙungiyoyin miyagu’.

Haka nan a cikin wani saƙo na daban rundunar sojin Najeriya ta sanar da wani shiri na kawar da ƴan ƙungiyar Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi.

A watan Mayu ƙungiyar IS a yankin Sahel ta yi iƙitrarin ɗaukar nauyin wasu hare-hare a jihohin Sokoto da Kebbi.

Address

Katsina
KT

Telephone

+2348035562339

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kadarko TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kadarko TV:

Shortcuts

Share